SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Bayan kwana ɗaya…
Tun da yamma ta je bayan gidan su ta tone shi da ɗan zurfi. Ta sa kwali da buhu ta rufe wajen.
Ƙarfe ɗaya saura ta ɗau ƙwaryan da Boka ya bata ta fita. Karen da ta siyo na kwance a wani keji gefen ramin da ta tona. Dama tun da yamma ta ma sa alluran bacci saboda Boka ya ce ba matacce za ta sa ba.
Lokacin da ta sa ƙwaryan a cikin ramin dai-dai agogon hannun ta ya cika ƙarfe ɗaya na dare. Ta cicciɓi karen za ta sa a cikin ramin aka dallota da torchlight.
“Anty Naomi what are you doing there?” Muryan ƙaninta Abel ya doki kunnen ta….
Skt 55
Naomi ta ɗago ido ta kalli Abel da ke nufo wajenta. Lokaci guda ta ji wani abu ya shiga kunnen ta, ta fara girgiza kai da sauri-sauri.
“Anty Naomi…” kafin ya ƙarasa maganar sa Naomi ta cilla ma sa Karen da ke hannun ta, ya goce da sauri har torchlight ɗin hannun sa sai da ta faɗi.
“Yirrrrrrrrrr, Ah Ah Ah, Chinkokoko kokokokoko Chichichichi…” waƙar da Naomi ta fara kenan tanayi tana rawa.
Abel ya tsaya yana kallon ta tareda kiran sunanta amma sam ba ta san yana yi ba sai tiƙar rawa ta ke yi, tana yi tana dariya.
Ganin fa ba dena rawar za ta yi ba, ya je ya kamota da ƙarfi yana faɗin “stop this nonsense please”
Naomi ta yi wani kuka sannan ta wancakalar da Abel ta baya ya faɗi ƙasa yana haki, “i’m coming oo i’m coming oo” abinda ta ke faɗi kenan kafin ta ranta a guje. Shi kuwa Abel ya fara ƙwala wa Maman su kira…
Ƙarfe ɗaya saura na dare ta tashi fitsari. Ganin idan ta koma bacci za ta iya kasa tashi ƙarfe biyu kamar yadda ta saba ya sa ta yi alwala kawai ta fara sallah. Ba ta kwanta ba sai ƙarfe uku da rabi bayan da ta ji ƙafafuwanta sun ma ta nauyi…
………………………………
Karfe biyar alarm ɗin ɗakin ya fara bugawa. Ya sa hannu ya laluba agogon ya kashe alarm ɗin. Idon sa a rufe ya fara jawo pillow jikin sa saboda yadda ya ke jin daɗin baccin. Daga saman pillow har ƙasansa ya shafa kafin ya ankara pillow ya rungume ba matar sa. Ya sa hannu ya fara laluba gadon ba tareda ya buɗe ido ba. Sai da ya ga hannunsa ya kai ƙarshen gado bai ji laushin mutum ba, sannan yai saurin buɗe idon sa tareda kai hannun sa wajen switch ɗin wuta ya kunna shi. Ɗakin ya ƙaraɗe da haske, yadda hannun sa ya lalubo ma sa babu hakanan idon sa ya gano ma sa babu. Tunanin sa banɗaki ta shiga dan haka yai murmushi haɗe da miƙa yana addu’ar tashi daga bacci a zuciyar sa.
Ya ziraro dogin ƙafafuwan sa ƙasa hannun sa akan idanun sa yana murza su saboda nauyi da su ka ma sa. Sai da yai minti biyu zaune kafin ya miƙe tsaye ya fara ƙoƙarin cire kayan baccin sa…
Lokacin da ya shiga banɗakin ma dai wayam ne ba kowa a ciki. Ya girgiza kai yana sawa a ransa ƙila ta je cin abinci ne dan ‘yan kwanakin nan har dare ta kan tashi ta ce yunwa, ta je ta yi girki ta ci.
Akwai ranan da ƙarfe ukun dare ta tashi ta je ta fara wanke wake wai ƙosai za ta ci. Ƙosan ma na manja irin wanda maƙociyar su Iya Abosede ta ke yi a Jos.
Cikin bacci ya farka da niyyar su yi abubuwa saboda kafin su kwanta ba su yi komai ba saboda ciwon kai da ya takura shi, ya ga gadon wayam. Ƙarshe a kitchen ya samu matar sa tana ta faman wanke wake.
Sai da ya tsaya a bakin kitchen ɗin ya ƙare ma ta kallo kafin ya ƙaraso wajen ta.
“My love mi ki ke yi da daren nan please?” Ya faɗa yana rungumeta ta baya.
“Ƙosan manja na ke son ci shine na ce barin zo na haɗa shi da sauri”
“Queen ki bari da safe sai ki yi mana, kin san ƙarfe nawa yanzu?”
” kar ka damu yanzu zan haɗa, na ma gama wanke waken saura marƙaɗe”
Ya sani ba haƙura za ta yi ba dole haka ya tsaya kusa da ita har ta markaɗa waken a blender ta zo ta soya ƙosan cikin manja. Duka duka ƙosan ma guda shida ne wanda ta yi su manya.
A kitchen ɗin ta zauna ta fara ci, tana ci yana kallon ta. Lokacin da ba ta da ciki ma ya aka ƙare da ciye-ciye balle yanzu da abun nema ya samu.
“My Champ ka taɓa ka ji, yai daɗi sosai Wallahi”
Ya girgiza kai ya ce ” ƙosan mangyaɗa ma bana ci balle na manja. Ki ci da kyau Maman princess”
Tana ci tana lashe manjan da ke yatsunta.
“Ka san da yanzu na yi da niƙaƙƙen waƙe da ba zai taɓa yin daɗi kamar wannan ba. Amma this one is fresh and yummy”
Gyaɗa kai kawai ya ke dan ba wai yana gane maganganun ta ba ne. Haka ya tsaya har ta take ƙosan nan gaba ɗaya…
Yai wanka ya ɗauro alwala ya fito, ya sa jallabiyar sa ya sauko ƙasa ganin har lokacin ba ta ɗakin. Duhun da kitchen ɗin ya ma sa ne ya tabbatar da babu mutum a ciki, amma duk da haka sai da ya kunna wutan kitchen ɗin, still ba kowa. Ya kashe wutan ya fita yana sawa a ransa tana ɗakin ta ne. Ya wuce masallaci dan gabatar da sallar Asuba.
Bayan an idar da sallah ya tsaya ya ɗan yi azkar sannan ya fito. Musabaha su ka yi da Alhaji Abubakar maƙocin sa inda Alhajin ke tambayar ko ya yi tafiya ne kwana biyu baya ganin yana fitowa asuba.
Najeeb ya girgiza kai tareda ƙoƙarin nemo dalilin da zai sa ba zai fito sallan Asuba ba bayan yana gida. Dalili biyu ne za su iya sawa, ko dai ya makara bai tashi ba ko kuma ana ruwa. To duk babu ko ɗaya aciki domin zai iya cewa tun da su ka dawo anguwar indai yana gida to baya fashin fita sallar Asuba, hakanan ko ruwan farko ba a fara a garin ba balle ya ce ruwan sama ne.
Bai ma san lokacin da Alhaji Abubakar ya tafi ba saboda nisan tunani da yai.
Yana tafiya abubuwa da dama na ma sa yawo a kwanyar sa.
“Its not possible” ya faɗa da ƙarfi lokacin da kwakwalwarsa ta tuno ma sa da mafi yawancin abubuwan da su ka faru cikin abinda bai wuce sati biyu ba.
Yana shiga gidan ya fara kiran sunan ta da ƙarfi.
“Alhaji Barka da Asuba” Tasallah ta faɗa wanda fitowanta kenan daga ɗaki za ta je ta fara haɗa ma sa breakfast saboda fitar sassafiya da ya ke yi.
“Ina Aysherh?” Ya faɗa da muryan da ta ke tattare da damuwa. Ba abinda idon sa ke gani kamar Aysherh a tsugunne gaban sa tana kuka.
“Alhaji ba kai ka sa folisawa su ka zo su ka tafi da ita ba kwanaki”
Yadda ka san guduma aka kwaɗa ma sa a kai haka ya ji saukar maganar Tasallah.
Maganar da ta yi ya sa ya tuno abinda ya faru ranan. Numfashin sa ne ya fara ɗaukewa ga wani duhu-duhu da ya ke gani. Ya fara ƙoƙarin dafa bango saboda kar ya faɗi amma bangon ya ma sa nisa, ƙarshe dai da shi da hannun duk ƙasa su ka yi. Tasallah ta fara Salati tana kiran Alhaji.
Dafe ƙirjin sa yai saboda zafi, ga uwa uba kan sa da ke sarawa.
Idon sa a buɗe ya ke amma baya ganin komai sai duhu.
Salatin da Tasallah ke yi ya sa shi ya fara maimaita kalmar Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’oun. Ya jima yana maimaita kalmar kafin ya fara jin sauƙin ƙuncin da ya ke ciki. Tashi yai a hankali ya rasa ma ina zai je waje zai fita ko sama zai haura.
“Aysherh Aysherh Ay…” bai ƙarasa na ukun ba ya faɗi ƙasa yigif…
……………………….
Bayan ta yi sallar Asuba sai da ta jima tana addu’o’i kafin ta ɗauko Ƙur’ani ta fara karantawa. Kusan ƙarfe takwas sannan ta ajiye ƙur’anin ta yi addu’a ta naɗe sallayar. Sai da ta je ta yi fitsari kafin ta zo ta kwanta tunda ba abinda za ta yi kuma ba yunwa ta ke ji ba. Tana kwance ne dai amma baccin ya ƙi zuwa, kewar mijinta ta ke yi sosai. Ba ta san yaushe wannan abu zai zo ƙarshe ba amma ta sani duk min daren daɗewa za a sami nasara tunda Allah su ka riƙe shi kaɗai. Ba dan kisa babban laifi ba ne da ba abinda zai hana ta je ta shaƙe wuyan Naomi har sai ta mutu.
Ta ƙara lissafta kwanakin da ta yi ba tareda zaman lafiya da mijinta ba. Kwanaki goma shauku ne rus yau ne ma cikon na sha ukun. Tunda ta dawo gidan Daddy kuwa ko zuwa bai yi ba balle kuma kira. Mafiya yawan lokuta takan wuni da waya a hannu ko za ta ga kiran shi ko text amma shiru. Dama tun ranan da ya faɗawa Daddy zai auri Naomi da su ka yi baran-baran har yau baya zuwa gidan.
Tana cikin wannan tunanin Aka fara buga ƙofar ta.
Yes ta faɗi tana miƙewa dan ta buɗe ƙofar.
Lokacin da ta buɗe ƙofar kafin ma ta ce ƙala Mom ta rungumeta tana faɗin “Alhamdulillah Allah ya amsa roƙon mu”