SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ba ta fahimci mi Mom ke nufi ba ko kuma dai ta fahimta ba ta gaskata hakan ba ne kawai.

“Ɗazu Tasallah ta kirani wai Son ya faɗi, dreba ya wuce da shi asibiti. Ni da Daddy mu ka fita ɗazu mu ka je asibitin. He’s back Ayshah. Mijin ki na neman ki, he wants to see you”

Tabbas ɗazu da tana azkar ta ji fitan su Mom amma ba ta kawo aranta wannan ne dalilin ba.

Hawayen daɗi ne su ka fara sauko ma ta, Mom ta sa hannu tana goge ma ta su tana faɗin ” ba kuka za ki yi ba, farinciki za ki yi Ayshah. Allah ya dube mu da rahama. Wassu su kan shiga wannan yanayi su jima a ciki, a ɗau watanni ko shekaru ana ta roƙon Allah kafin daga baya a samu sauƙi amma mu Allah ya mana gata cikin ƙanƙanin lokaci ya bawa Najeeb lafiya”

“Alhamdulillah, Alhamdulillah” Farida ta faɗi tana murmushi.

Skt 56

Lokacin da su ka shiga ɗakin yana kwance yana bacci an ɗaura ma sa ledar ruwa. Daddy ke gefen sa yana kallon ɗan na sa yadda abubuwa da dama su ka dinga faruwa da shi a rayuwar sa. Kowa da tashi ƙaddarar, shi kam Daddy bai fuskan ci irin waɗannan ƙalu bale ba kamar na ɗan na sa. Tunda ya mallaki hankalin sa, idan ka cire mutuwar Aisha baya tunanin akwai lokacin da ya shiga yanayi na ƙunci sai a kan Najeeb. Shi ne yai rayuwar kaɗaici shekara takwas saboda ya rasa Sabreen, shi ne aka kidnapping, shi ne yai accident yai kusan wata tara kwance a asibiti shi ne ya ɗau watanni kafin ya dawo dai-dai, shine kuma mace ta ma sa asiri har ya ke ƙyashin matar da ya ke mutuwar so. Kai Alhamdulillah, dama dole ne mutum ya fuskanci jarrabawa a rayuwar sa.
Yai wa ɗan na sa addu’ar Allah ya sa ya ci dukkan jarrabawar sa ta duniya.

Mom ta ce ” ya yi bacci ne?”
Daddy ya ce ” Likita ne ya ma sa allurar bacci saboda ya samu ya huta”

Farida ta gai da Daddy tareda ma sa ya mai jiki. Daddy ya amsa da cewa “Aishah kin ga al’amari na Ubangiji ko. Allah ya share ma na kukan mu, sai mu dage da addu’a kuma, kar mu taɓa sakaci da addu’a”

Farida ta amsa da Insha Allahu. Kallon Najeeb ta ke tundaga gashin kan sa har tafin ƙafar sa. Ya mata kyau sosai amma kuma ya rame…

Najeeb bai farfaɗo ba sai kusan ƙarfe ɗaya na rana. Yana buɗe ido ya ga matar sa zaune. Kamar wadda aka tsikara haka ya tashi zaune da sauri. Ganin ta haɗa rai lokacin da su ka haɗa ido ya sa ya tashi tsaye ya iso wajenta. Tana zaune akan kujera ko gizau ba ta yi ba balle ta tashi sai ma juyar da kai da ta yi.
Tsugunnawa yai a gabanta yana kallon gefen fiskarta.

“Na sani abinda na yi is unforgivable. Na sani kina da hujjar da za ki yi fushi da ni. Amma Dan Allah my Queen ki yafe min, I love you, only you”

Juyowa ta yi ta kalli ƙwayar idon sa wanda ke nuna tsananin so da begen ta. Ba abinda ta tuna irin yadda ta tsugunna gaban sa tana hawaye tana roƙon sa amma yai watsi da ita.

“I forgive you” ta faɗa a hankali. Ya taso da sauri zai kissing ɗin ta ta sa hannu ta tare bakin sa ta ce ” i forgive you amma kuma…”

……………………..

Kafin a samu a kamo Naomi sai washe gari a chan wani bola tana kwance duk kayan jikinta a yayyage. Kai tsaye gidan Pastor Chukudi aka wuce da ita, wanda ya ke shine pastor ɗin church ɗin da su ke zuwa. Maureen ce ta faɗi silar haukan Naomi shiyasa aka wuce da ita gidan Pastor ɗin. Ita kan ta Maureen ta tsorata da yadda ta ga haukar ƙawar na ta, acewarta su koma wajen Ifagbemi ya basu magani amma Mrs Comfort ta ce ba za su aikata saɓo biyu ba. Ga saɓon zuwa wajen Boka dan asiri ga saɓon neman magani a wajen boka. Ita ta yarda Jesus zai warkar da ‘yarta.

Annointed water da oil kam Naomi ta sha su kamar ba gobe amma shiru ka ke ji kaman an suka dusa. Ba sauƙi balle ayi tunanin za ta warke. Da dare Pastor Chukudi da tawagar su su wuni akan Naomi suna ma ta holighost fire amma su na yi tana ƙara rikice mu su…

…………………..

Cikin kwana biyu Najeeb ya fita hayyacin sa. Farida ta ƙi dawowa. Ta ce ta yafe ma sa amma ya bata lokaci ta yi tunani. Mom ma ta goya ma ta baya akan ya barta ta huta.

Yau ma dai gidan ya zo roƙo amma ba ta nan, Adama ta ce sun fita da Sabreen.

Ya zauna a falo yana jiran dawowar su duk da kuwa Adaman ta ce ba su jima da fita ba.
A falon Daddy ya dawo ya sameshi lokacin har ya fara bacci. Jin takun mutum ya sa ya farka.
Gaishe da Daddyn yai yana faɗin yana son magana da shi. Daddy ya ce ya biyo shi. A falon Daddy su ka ya da zango inda Daddy ke tambayar ko lafiya.

“Dad ka sa baki dan Allah. Ta ce wai sai ta haihu kafin ta dawo. 3 months yai yawa, ba zan iya jure rashin ta ba”

Daddy yai murmushi ya ce ” so ka ke na sa ta tayi abinda ba ta so?”

“No Dad amma idan ka ma ta magana wallahi ba za ta ƙi maganar ka ba”

” Son kenan, wannan tsakanin ka da iyalin ka ne ba ni da wani hurumi a ciki. Ka bata lokaci kaɗan za ta sauko, she went through alot saboda kai dan haka ka bi ta a hankali”

Najeeb ya haɗa rai dan bai ji daɗin maganar Dad ba, maimakon ya supporting ɗin sa sai ya ke maganar wai ya amince da hukuncin da ta yanke…

Lokacin da su ka dawo ma haka ta wuce shi, yana magana ko uhum ba ta ce ma sa ba ta haura sama.

“Sabreen please help me talk to her” ya faɗa yana haɗa hannu.

Kaman Daddy itama cewa ta yi ya ba wa Farida lokaci.

Ɗakin su ya wuce ko zai samu daman magana da ita amma ya samu ta kulle ɗakin.

“My Queen please ki bari na ganki ko na minti ɗaya ne”

Tana zaune akan gado tana jin magiyar sa amma ko ajikinta duk da chan ƙasan ranta tana son kasancewa da shi amma ba za ta janye ƙudirinta na son horashi kaɗan ba. Haka ya gama magiyar sa ya bar wajen….

Bayan kwana biyar da haukar Naomi Pastor ya bada shawaran a je a bawa wanda ta yiwa magani haƙuri saboda idan su ka yafe hakan zai sa Naomi ta samu sauƙi.
Mrs Comfort, Pastor Chukwudi da Saint Janet suka je gidan su Najeeb. Maigadi ne ya sanar da su Farida tana gidan au Najeeb, su ka karɓi address a wajen shi su ka wuce chan…

Mrs Comfort kuka ta dinga yi wiwiwi a gaban su Farida tana roƙon su gafartawa Naomi. Daddy ya ari bakin Najeeb da Farida ya ce sun yafe, Najeeb ya haɗe rai dan shi plan ɗin shi ma sai Naomi ta je jail.

Pastor ya mu su godiya sannan su ka tafi. Duk da wannan yafiya da aka yi bai sa Naomi ta warke ba. Kwana biyu da dawowar su daga gidan su Najeeb ta tsere daga gidan Pastor ta shiga gari. Wasa-wasa aka baza neman ta amma har sati guda ba labarin inda ta ke…

…………………….

Shirye-shiryen bikin Sabreen ake yi duk da kuwa Sabreen da Lukman ɗin sun amince akan ba za ayi hidima ba amma Mom da Farida sun ƙi. Wata guda aka saka har yanzu kuma saura sati uku.

Fitowarta kenan daga wanka ta kalleshi zaune akan gado. Mantawa ma ta yi ba tarufe ƙofan ba.
“Ni fa ba na so ana shigo mini ɗaki ba izini”

A hankali ya taso ya zo ya tsugunna gaban ta ya kamo hannunta biyu ya riƙe gam. Kallon sa ta ke yi yadda idon sa yai ja.

“Aysherh I cant, ba zan iya ba. Kafin 3 months ɗin nan zan iya mutuwa idan ba kya tareda ni. Please ki manta da komai ki dawo gida mu cigaba da rayuwar mu. I promised to make it up to you, ba zan sake ɗaukan sakatariya ma ce ba, yalla yarinyace ko tsohuwa. Zan dage da addu’an dare saboda kar wata ta kuma samun galaba a kaina. Zan yi duk abinda ki ka ce amma please come back to me. I love you”
Ya kai hannun ta kan kirjin sa ya ce ” My heart beats for you Aysherh, only for you. Ki taimakeni ki taimaki zuciyata kar rashin ki kusa da ni ya min illa. Na ɗauka zan iya jurewa amma Wallahi ba zan iya ba, its being 2 weeks amma gani na ke kamar 2 years ne. I miss you Aysherh, I miss us. Please my Queen…”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button