SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

SAKATARIYA TA COMPLETE NOVEL

Ya jima yana rarrashin ta kafin ta yi shiru ta miƙa ma sa PT strip ba tareda ta ce ma sa ƙala ba. Bai gane ba ya tambayeta ” what is it?”

Ta ɗago jajayen idanun ta ta kalleshi ta ce ” i’m pregnant”

Allahu Akbar Najeeb ya faɗa tareda yin sujjada a gefenta. Har ya ɗago ba ta dena kallon sa ba.

“Kai i’m happy Aysherh, kin min komai a rayuwa ban san mi zan miki na saka miki ba”

Hararansa ta yi ta ce “it seems ka manta shayarwa na ke. Yaman is only 7months”

“So?”

“Da ke ba kai za ka yi wahalan ba ai”

Jawota jikinsa yai ya ce ” Aysherh aren’t you happy, mutane nawa su ke neman haihuwa ido a rufe amma Allah bai ba su ba. Amma ke kin samu kina kuka, let me ask you something. Kuɗin kula da su ne ba mu da shi ko kuma me ne?”

Skt 59

Maimakon ta bashi amsar maganar sa sai ta fashe da kuka. Har cikin ransa ya ke jin haushin kukan ta, dan shi bai ga abin kuka a nan ba.

“Ban yi aure da wuri ba Aysherh, i had my first child at 37yrs. Ina da abokai da ‘ya’yan su na fari suke shekara goma, takwas, bakwai. Kai Cousin ɗina Bilyamin da ke Gombe, shekara ɗaya aka haife mu, but his first daughter will be thirteen this year. Ba kya son haihuwa da ni ne?”

Shiru ta yi dan ba ta da abin cewa. Ita dai ta san tana son hutu, haihuwa ba wasa ba ne.

“Shekarun baya cikin wauta na tsara wa kai na iya ‘ya’ya biyu na ke so. Amma yanzu i’ve changed, ina son ‘ya’ya dayawa. Allah ya kawo mana ko nawa ne, da taimakon Ar-Rahman za mu kula da su, mu tarbiyantar da su bisa tafarkin addini, za mu yi komai dan mu inganta rayuwar su in har muna raye”

“Dole ka ce in haihu dayawa ai, salon nan da ‘yan shekaru kaɗan idan na gama yin laushi ka je ka ce za ka auro wata sabuwa tunda na tsufa. Wallahi lokacin ne za ka san Aisha Farida ka auro”

Lallai Farida har yanzu da sauran shirmenta, abin da ya ke hanga daban abin da ta ke hangowa daban. Cigaba da magana da ita a wannan lokacin ma shirme ne.
Miƙewa yai ya je ya ɗau Yaman da ke bacci ya ce “ka da abinda ya samu baby na Aysherh. Or else…” ya sa kai ya fita ba tareda ya jira mi za ta ce ba.

Ranan gaba ɗaya ɗauke ma ta wuta yai dan har raba wajen kwana su ka yi, ya kwana a ɗakin sa ita ma ta kwana a na ta.

Washe gari ma ko kulata bai yi ba. Tana gaishe shi ma sama-sama ya amsa ma ta. Haka su ka ci breakfast ba tareda wani ya yi wa ɗan uwan sa magana ba. Yana gamawa ya tashi ya fita…

………………………..

Yau kwana biyu kenan ma’auratan ba sa wani magana da junan su. Najeeb na dawowa daga office zai maƙalewa Yaman yana wasa da shi. Idan ya lura yana jin yunwa kuwa Tasallah zai kira ko matar Abdullahi su miƙawa Farida.

Najeeb na dawowa daga sallar Maghrib ya ga su Tasallah na fito da kayan Yaman ana sawa a boot ɗin mota. Farida na tsaye ɗauke da Yaman wanda ya sha kayan sanyi ma su kyau saboda yanayin garin akwai sanyi, itama Faridan da ganin shigarta fita za ta yi. Bai ce komai ba ya tsaya yana kallon ikon Allah. Farida ma kau da kai ta yi kaman ba ta gan shi ba tana jira su Tasallah su ƙarasa fito da kayan.
Sai da su ka gama Farida ta ce ” ba’a manta komai ba ko?”

Tasallah ta ce duk kayan da ta ce a ɗauko an ɗauko.
Farida ta sa kai ta shiga mota dreba ya ja mota su ka fita a compound ɗin. Najeeb na tsaye a wajen yana ganin ikon Allah. Ran sa kuwa yai matuƙar ɓaci, mi Farida ke nufi da shi.

Ya isa cikin gidan da ƙyar saboda ciwon kai da ya fara ji saboda ɓacin rai. A hankali ya ke maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’oun saboda ya samu nitsuwa…

……………………

Farida kam gidan su Najeeb ta wuce da Yaman. Da ta je a falo ta samu Mom da Najdah suna hira, itama ta zo gida.

“Oyoyo angona” Mom ta faɗa tana ƙarɓan Yaman a hannun Farida.

Shigowa da kaya da Danliti ya farayi ne ya sa Mom tambayar ko lafiya.

“Na kawo miki ɗan yaye ne”

“Ɗan yaye?” Mom ta faɗa tana sake kallon Yaman da ke hannunta. Yaron da watan shi bakwai da sati biyu ne a duniya.

“Mom yaron bai damu da nono ba, shima rashin son cin abinci kaman uban sa. Shi ne na ce gara na yaye shi”

“Amma Anty Farida da kin bari ya cika shekara ɗaya, Yaman fa bai da wani ƙwari” Najdah ta faɗa tana kallon Yaman ɗin da ke murmushi saboda Mom da ke ma sa wasa.

“Kema kina hanya ai za ki ji yadda ake ji. Allah ya kaimu nan da wata biyu lafiya”

Najdah ta yi shiru dan itama fama ta ke yi da kanta. Ta wahala sosai da wannan cikin tun yana ƙaramin sa har yanzu kuwa.

“‘yata ki bari Yaman ya kai 10 months mana, Najeeb ma a wata goma na yayeshi”

“Mom ki yi haƙuri dan gaskiya na yaye shi daga yau”

Mom ta kalli Faridan da kyau ta yi murmushi dan ta lura kaman Faridan na ɗauke da ciki ne…

Sai bayan sallar Isha Farida ta dawo gida. A falon sama ta samu Najeeb yana zaune sanye da baƙar jallabiya yana jan carbi.

“Barka da hutawa” ta faɗa tana ƙoƙarin tafiya ɗaki tunda har yanzu ba wai sun shirya ba ne.

“Aysherh” ya kira sunan ta a hankali.

Tsayawa ta yi tana jiran mi zai ce.

“Zo ki zauna?”

Ba musu ta dawo ta zauna a gefen sa.

“Ina ki ka kai min ɗa na?”

“Gidan kakannin sa”

“Why?” Ya faɗa yana ma ta kallon tuhuma.

“Na yaye shi ne, shi ne na kai mu su shi”

“Da izinin wa?” Ya faɗa da ɗan ƙarfi.

“Kai ne fa ka ce kar abinda ya samu cikin ka, lafiyata da lafiyar Yaman ya sa na yaye shi dan na kula da wanda ke cikina yanzu”

“And you made the decision without me”

“Ya ka ke so na yi, fushi ka ke da ni, ba ka min magana balle na gaya ma ka zan yayi Yaman”

Yana son yin magana amma idan yai hankalin sa ne zai tashi saboda ɓacin rai da ke cin sa.

Miƙewa yai ya ce ” tunda banida matsayin da za a yanke shawara tare da ni, shikenan ki yi duk abinda ki ke so. Wanda ya ke cikin ki ma idan ba kya son sa ki yi waje da shi kar ya takura ki ya sa ki tsufa da wuri”…

“Ba haka ba ne My Champ, Wallahi…” ta tsayar da maganar saboda wucewa da yai ɗakin sa ba tareda ya kalleta ba…

Yadda ya ke magana ta san ran sa a ɓace ya ke. To ba ya ma ta magana ya yake son ta sanar da shi shawaran da ta yanke…
…………

Waɗannan kwanaki huɗun sun fi kowani rana zafi a gareta. Idan ka cire lokacin da Naomi ta ma sa asiri, Najeeb bai taɓa shareta kaman na wannan kwanakin ba. Ba ya dawowa daga office sai ƙarfe goma ranan da ta je office kuma yadda ka san kwandon shara haka ya maidata ko kalma ɗaya bai ma ta ba. Lokacin da ta ke bashi haƙuri ma miƙewa yai ya bar ma ta office ɗin.

Shi kam Najeeb daga office gidan su ya ke wucewa ya je ya zauna da ɗan sa. A kwana na biyu Mom ta ma sa maganar ko zai tafi da Yaman ne, ya ce ta bar shi Farida na da ciki shiyasa ta kawo shi…

Ba abin da ya kai zaman lafiya tsakanin miji da mata daɗi. Farida har rama ta yi saboda fushin da Najeeb yai da ita. Yana dawowa da dare zai shiga ɗaki ya kulle sai kuma da safe.

Yau kam ta watsar da duk makaman yaƙin ta, ta ɗaga farar tuta. Tana son mijin ta, ga shi ko cikin ne ko minene dai ‘yan kwanakin nan da su ka yi ba sa tare ba ƙaramin kewar shimfiɗar mijin ta ta ke yi ba.

Zuwa ta yi aka ma ta ƙananun ƙitson bare-bari saboda Najeeb ya fi son ya ga ta yi ƙitso compared to barin gashin haka nan ba kitso, aka ma ta jan lalle mai kyau ya fito da kyaun ƙafarta da hannun ta.

Ta haɗa madara zuma da lalle ta shafe jikin ta da shi, da yai awa ɗaya ta shiga banɗaki ta kakkaɓe sannan ta yi wanka da shower cream mai ƙanshi.
Dama tunda rana ta blending kankana da apple da lemon ta sa a fridge yai sanyi. Da ta gama shiryawa ta sa dogon hijab ta sauƙa ƙasa ta je ta ɗauko juice ɗin ta, tana zaune bayan sallan Isha tana shan juice ɗin tana kallon wayarta ko za ta ga saƙon sa amma shiru. Tun ƙarfe biyar ta tura ma sa text akan dan Allah ya dawo da wuri, sai dai bai ma ta reply ba.
Ƙarfe tara da rabi ta ji horn ɗin mota ta yi hamdala a zuciyarta…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Leave a Reply

Back to top button