TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ikon Allah ne kawai ya dawo da Sumayya cikin mota, bata iya zama ba sai ta zauna ta fara kuka a hankali. Hassan ma da ya shigo bai yi wa kowa magana ba sai ya tayar da motar yayi reverse suka bar gurin. Sai a lokacin Ruqayyah tayi magana “ina kuka je wai? Kun fita kun barni a mita ni kadai, ne kuka yi? Ta juyo tana kallon Sumayya tace “ita kuma wannan mai aka yi mata?” Babu wanda ya amsa mata a cikin su, sai Hassan ne ya kalli Sumayya yace “ki daina kuka Sumayya, farin ciki ya kamata kiyi, ko babu komai munsan cewa yana da rai yana kuma da lafiya, kar ki manta maganar mai gadin da yace suna sonsa sosai? They will never harm him” Ruqayyah ta sake cewa “wai waye kuke maganar sa?” Hassan yace mata ” Adam” tayi sauri ta kalle shi idanuwa a bude, yace “yes, gidan iyayen sa ne nan, kuma muna suspecting wata ce daga gida ta aiko gidan su ta fadi inda yake, dan haka muna tsammanin iyayensa ne suka dauke shi” Ruqayyah ta dauke kai gefe tana kallon titi, trying so hard ta boye tashin hankalin ta, ta jima tana juya maganar sannan tace “at least yanzu zaku ragewa kanku damuwa saboda, he is in the safest of places for him. Yana tare da iyayensa”.

Har suka je Kaduna babu wata maganar kirkin da suke yi a tsakanin su, gidan sa ya zarce dasu direct kuma suka tarar already Aunty ta aiko an yi duk gyare gyare-gyaren da ya kamata a yi a cikin gidan, har abinci an kawo musu an ajiye a dining. Suka ci abinci suka yi wanka sannan sai ga su Aunty sun shigo sun duba Ruqayyah. Daga baya kuma sai ga Inna Ade da Baba dasu Sulaiman, Baba ya barsu a gidan bai dawo daukarsu ba sai dare, a lokacin ne kuma inna Ade ta saka Ruqayyah a gaba da nasiha saboda ta fahimci ta sauki maganar ciwon nan da zafi sosai. Sumayya kuwa jin su kawai take yi tana tunanin maganganun mai gadin nan, kalmar wata mata ta tsaya mata a zuciya, wacce matar? Kuma wai a gidan take. Wacece ita? Tunani da yawa yana crossing mind dinta amma sai ta kawar dashi, no, it can’t be, her sister can’t be that cruel da har zata raba ta da happiness dinta saboda selfish reason dinta. It can’t be. Idan haka ta kasance zuciyarta ba zata iya dauka ba, idan haka ta kasance babu ita babu Ruqayyah, har abada.

But she is going to find out, zata yi bincike da kanta saboda bata son tayi zargin yaruwarta……..

Sai dare Baba ya dawo ya dauke su gaba ki dayan su har Sumayya suka tafi gida. Bayan sun tafi ya rage Ruqayyah da Hassan da kuma yara su guda uku. Shi yayi wa yaran wanka yana jin missing dinsu a ransa ya fito dasu ita kuma ta fara shirya su da kayan baccin su suna tayi mata gwaranci da alama sunyi missing dinta sosai. Sai ya jawo kujera ya zauna yana kallon su yana jin dadi, ta daga kai tana kallon sa tace “mijina. Nace wai yanzu tunda ba zan iya shiga jirgi zuwa kasar waje ba, why not kayi min kokarin yadda za’a yi shi doctor din yazo nan ya duba ni?” Ya nade hannunsa a kirjinsa yana kallonta yana mamakin ta, yace “yazo nan ya duba ki? Da wadanne kayan aikin? Da wannan kudin kuma zan iya hayar likita kamar wannan yazo har Nigeria ya duba matata?” Ta tsaya da abinda take yi tana kallonsa Tace “ban gane ba? Kai fa kace min zaka yi duk iyakacin kokarin ka kaga na samu lafiya, I am just trying to hold you to your promise” yace “haka na fada kuma haka zanyi, amma abinda kike fada is not possible” tace “not possible? A gurin ka? Kar ka manta fa yanzu fiye da rabin abinda Hussain yake dashi sanda yana da rai ya zama naka” sai ya mike tsaye yana kallon ta yace “tunda kince haka let me tell you plans dina duk da ban gaya wa kowa ba yet. Nayi putting up H and H gabaki dayan ta for sell, already har ance dangote ya fara tayawa, zan siyar da komai, in nace komai ina nufin komai including gidan nan da muke ciki da motocin da Hussain ya bari duk zan siyar, za’a fitarwa da Fatima gadonta a kaiwa iyayen ta, za’a fitar dana sisters din mu a basu abinsu sannan sauran zanyi sadaka dashi, gaba dayansa, da fatan Allah ya kai ladan kabarin Hussain”.

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020

Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa
Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin AllahThe Fourth Wave*

Yana kallo rigar Yusuf da take hannunta ta zame ta fadi, yanayin fuskarta ya fara chanzawa from fair to bad then to worst. Har saida yanayin ta ya juya zuwa yadda bai taba gani ba, sai yaga gabadaya ta chanja daga Hassanar da ya sani ya kuma aura zuwa wata halitta ta daban wadda bai taba sani ba. Tabbas yasan tana son kudi, yasan ta boye masa cewa tana son kudi tun ranar da tayi subutar baki a gabansa ta gaya masa cewa shi bashi da komai dan uwansa yana da komai, amma bai taba zaton son da take yiwa kudi ya kai wanda yanayin ta zai iya wannan chanzawar a lokaci daya ba dan yace zaiyi wa dan’uwan sa sadaka da kudin da dan’uwan nasa ne ya tara da kansa ba wani ne ya tara masa ba.

Yana kallonta ta mike tsaye, har tana bude Yusuf da yake kusa da ita yana jiran ta saka masa riga, amma bata kalli yaron ba kamar ma bata san ta bige shi din ba tace “what? Me naji kace?” Ya rungume hannunsa yana kara studying dinta yace “abinda kika ji shi na fada, zanyi sadakar duk abinda Hussain ya bari da kuma share din daya bani kafin rasuwar sa ga mabukata, da fatan Allah ya kai rahama kabarin sa, thats how much nake son sa”

Idonta yaga ya kawo ruwa sannan hawaye ya fara zuba daga idon, ta bude baki ta mayar ta rufe, amma bai fita ba kuma bai daina kallon ta ba yana so ya karanta wani abu a idonta, yana so ya hango ko da burbushin yarinyar nan data taimaka masa ranar nan a idonta amma babu, she is totally gone.

Ta hadiye abinda ya hana ta magana sannan tace “love? Love kake cewa? That’s how much kake son Hussain, Hussain da baya duniya bayan mu kuma gamu a duniya, what about us? Mu baka son mu? Ni da yayanka. In kai baka bukatar dukiyar mu ai muna bukata, ni da yayanka, ta yaya zaka kula damu? Ko dan na zama nakasashshiya shine kake saka ran zan fita inyi bara in samo abin bukata? Wannan shine abinda kake nufi?” Fada take yi tana magana da duk kan karfinta, daga inda yake yana kallon yadda jikinta yake rawa, yana kallon yadda rage yake burning a cikin idonta. Bai taba dauka zata dauki zafi irin haka ba akan kudin da ba nata ba. Sai ya tako xuwa kusa da ita yace “yayana da ke da kannena da aunty duk responsibility dina ne, zan kula daku koda dako zanyi a kasuwa, kudin Hussain shi ya tara bani ba and am sending it back to him, nima zan tara nawa zan kuma kula da ku da iyakacin arzikin da aka rubuta min, na yanke wannan hukuncin tun ranar da Hussain ya raba dukiyar sa biyu ya bani saboda in kula da kaina in kuma kula da aunty da yan uwanmu saboda yana gudun kar Fatima ta haifi namiji in kasa gadarsa, yes, that’s how much he loved me. And…..” Ta kwace hannunta daga nasa tana masa wani irin kallo, tace “rabin dukiyarsa? Ya baka? Amma baka taba gaya min ba a matsayi na na matarka?” Yace “yes, saboda banyi niyyar amfani da ita ba tun a wancan lokacin, dan haka nayi tunanin gaya miki bashi da amfani” ta dafe kanta da hannu biyu tana fitar da numfashi sama sama, Wato tayi spending time a matsayin matar ceo without her knowing, kuma da tasan da wannan maybe da bata yi abinda tayi har yake hanata bacci ba. Ta bude idonta tana kallonsa tace “da kasan abinda kayi da bakayi ba, da zan gaya maka abinda kayi da kayi nadama babba” ya bude ido yace “me nayi? Dan ban gaya miki kanina yayi min kyauta ba shine zanyi nadama? I don’t think so” sai kawai yaga tayi wani irin murmushi ta kawar da kanta gefe sannan tace “lallai rashin sani kukumi ne” ya saka hannu ya juyo da fuskar tata yace “me kike nufi, what don’t I know?” sai ta rufe idonta saboda bata son ganin cikin idonsa, ko wuka zai saka mata a wuya ba zata fada masa abinda tayi dan ta samu dukiyar da yake kokarin rabarwa ga mutanen da ko sanda basu taba dagawa dan ganin samuwar dukiyar ba, bayan ita sai data….sai data…., Ko a cikin zuciyarta bata fadar abinda tayi ballantana a fili, ballantana a kunnen Hassan. Amma wannan hanyar daya dauko ba mai bullewa bace ba, she deserves that money, ba zata yi biyu babu ba, ba zata taba barinsa yayi mata wannan tozarcin ba, za kuma tayi komai dan ganin baiyi abinda ta gani a idonsa cewa ya gama daukan niyyar yi ba. In tace komai tana nufin komai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button