TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, bakar zuciyar Ruqayyah tana nan a kirjinta amma har yanzu dafinta bai bayyana ga Hassan ba. A haka akayi bikin Minal da alhajin ta lokacin su Yusuf suna da watanni uku a duniya. Ruqayyah tana tsananin son yayanta a zuciyarta amma being the Ruqayyah that she is, bata iya nuna soyayya ba dan haka sai ya zamanto yaran sunfi sabawa da Abban su, sai uncle dinsu wanda in dai yana gari to kullum suna tare har ya iya hada musu madara yayi feeding dinsu. Daga nan sai Aunty wadda dama daga sun dami Ruqayyah zata hada su da mai renon su su tafi gidan aunty, ita kuma ta dauki wayarta ta cigaba da daukan darasin mallakar miji.

A lokacin bikin Minal ne kuma Minal din da kawayenta suka zo gidan Ruqayyah da niyyar zasuyi bridal shower dinsu anan. Sai dai suk ayi rashin Sa’a suka tarar Hassan yana gida kuma Ruqayyah bata gaya masa za’a yi event din ba. Ya shigo yana kallon su, yana lura da yanayin shigarsu da kuma yadda babu wadda ta gaishe shi a cikin su. Sai ya sunkuya ya dauki yaransa y ahau sama da su, Ruqayyah ta bishi a baya.

Tana shiga dakin sa taga ya ajiye yaran akan gado yana musu wasa suna bangala masa dariya, ta tsaya a bakin kofa tana murmushi, bai kulata ba tace “dama bikin Minal dana gaya maka an fara, shine kawayen mu suka zo zasu dan yanka cake su kuma yi hotunan” ya juyo yana kallonta yace “kawayen ku? I thought you said kawayen Sumayya ne da na Minal? Ina ita Sumayyan take? Ko bata zo ba sai kawayenta?” Ruqayyah ta dauke kai gefe tana juya ido yadda ba zai ganta ba sannan ta karasa shiga dakin, ta dora kanta a bayansa tace “to yanzu menene dan nace musu kawayena? Ina laifin wanda ya kula ka? Ka manta su suka tsaya min da bikin mu?” Ya juyo yana kallonta yace “ina fa zan manta? Har duk rashin kunyar da suka yi min ina sane da kowacce kalma. I thought daga ranar ba zaki kara kula su ba saboda marar tarbiyya ne kadai zai riki wadannan a matsayin kawaye, baki san masu magana sunce ‘nuna min abokin ka Ni kuma in gaya maka halayen ka ba?” Ta daga shi tana jin ranta yana fara baci tace “ni banga abin daga hankali a wannan maganar ba, ko ma menene sukayi ko suka ce ai ya wuce ko? Idan da kai wani ne yanzu da ba sai dai inji kace ka dauki nauyin duk abinda za’a yi a gidan ba, ko kuma inga ka fita ka siyo mana duk abubuwan da muke bukata ba? At least haka akeyi a gidajen arziki, at least da Hussain ne da hakan zai yi ba wai ya zauna yana mitar abinda akayi shekara guda data wuce ba”

Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kuna son ki sayi halaliyar ki ki neme ni ta wannan number din through WhatsApp 08067081020Unveiled 2

Farko daskarewa yayi a zaunen da yake, sai kuma yayi blinking idonsa dan ya tabbatar cewa ba wai mafarki yake yi ba, sai kuma ya saka hannu yana bubbuga kunnuwansa ko sune suke yi masa karya sannan ya juyo yana kallonta, bakinsa da idonsa a bude amma kalma daya ta kasa fita daga bakin nasa, so yake ya tabbatar ita ta fadi wadannan maganganun, har da waigawa yayi dan ya tabbatar su kadai ne a dakin ba wata ce ta shigo ta fada ba, sai dai yana yin daya gani a fuskarta kadai ya isa ya tabbatar masa da cewa ita ta fada din. Rashin gaskiya kiri kiri a rubuce a fuskarta. Ta tosa kanta da sauri tana nin gabaki daya jikinta ya dauki kaikayi, sai kuma ta juya da sauri zata bar dakin. Tana son ta kasance ita kadai tayi bitar abinda tace din ta kuma shirya abinda zata ce ta rufe maganar tata.

Charaf ya rike hannunta,bata juyo ba sai idonta data rufe, ya mike daga kan gadon ya zagayo gabanta sannan ya saka cika hannun nata ya rike fuskar ta da hannayensa biyu. “Hassana?” Ta kwace fuskarta ta na kokarin juya masa baya ya sake rike ta, jikinsa har rawa yake yi “Hassana me kika ce min? Me kike cewa? Wacce magana kike gayamin Hassana? Are You okay?” A ransa ya fara tunanin anya ba aljanu suka taba Precious wife dinsa ba?

Bata ce komai ba still, yace “gidan arziki Ruqayyah gaya min me kike nufi da gidan arziki? Hussain? Da ace ni Hussain ne? Me kike nufi da haka?” Tsabar zafin da maganar tayi masa ya hana ya nuna bacin ransa sai ma karyewa da zuciyarsa tayi. So yake tayi magana, so yake ta gaya masa bata fada masa wadannan maganganun ba kawai imagination dinsa ne.

Ta bude idonta ta sauke su a kansa “kayi hakuri mijina ban fada da niyyar in bata maka rai ba, kawai dai ji nayi nawa ran ya baci kuma ban san na fada maka haka ba” ya sake ta, ta fada din kenan, bawai kunnensa ne bai ji masa dai dai ba wai imagination dinsa bane ba Hassana ce tace gidansa ba gidan arziki bane ba, da Hussain ne zaiyi abinda shi ba zaiyi ba.

Tana jin ya sake ta ta juya da sauri ta fita tare da rufe kofar, da ace da key a hannunta ma da rufe shi zata yi ta waje dan ita kan ta tsorata da fuskarsa da kuma rikon da yayi mata. Amma wannan bai hana ta shiga dakin ta ta dauko kudi ta fito gurin kawayenta suka cigaba da hidimar su ba. Sai da suka gama sannan ta fito da kudin ta basu tace inji Hassan yace suyi kudin mota. Minal tace “shi wannan mijin naki wallahi da kayan haushi yake, maimakon ma yace ga driver nan a waje a kai kowa gidansu sai ya wani bamu kudi?” Daya a cikin kawayen ta karbe kudin tana lissafawa tace “mu dai muna so, ke dan kin samu zaki shiga daga ciki shine har zaki yi yanga in an baki kudi?” Suka raba kayansu kowa ta saka a jakarta. Ruqayyah tabi jakankunan su da kallo tana hadiye daci a ranta, ta jima tana tara kudin nan tana son siyan wata sarka.

Da zasu tafi Minal ta jata kefe “to sai kin shigo dinner gobe” Ruqayyah tayi ajjiyar zuciya “dinner nan Minal ba lallai bane in shigo ta” Minal ta bude ido “amma kuwa da kin cika babbar marar m…dinner din bikin nawa zaki ki zuwa” Ruqayyah tace “ba cewa nayi ba zan zo ba, cewa nayi ba lallai bane inzo din, kin san ai komai sai Allah yayi ko? Ku tafi kawai, zamu yi waya zan baki labarin abinda yasa nace haka” Minal ta bata rai “ko ma menene ni ba uzuri bane ba a gurina, kuma in baki zo dinner ba wallahi nasan matsayina a gurin ki kuma na san kema a gurin da zan a jiye ki a zuciyata” Ruqayyah dai ta lallabata ta raka ta waje suka shiga motar da alhajin ta ya aiko ta dauke su.

Ta gefen idonta ta hango Adam yana fitowa daga part din Hussain yana tafiya hanyar shiga part din Aunty, a can yaje tare da sauran yaran Hussain a tsofaffin dakunan su Hassan. Ya saka hannunsa a aljihu yana taku dai dai jikinsa sanye da kaya masu kyau, in ka ganshi zaka iya tunanin kanin mai gidan ne dan yarintar sa ce kawai zata sa ba zaka ce shine mai gidan ba. Tayi tsaki, ta tsane shi har cikin zuciyarta, ya tsani guts dinsa, yadda yake tafiya da yadda yake magana da komai nasa. More importantly ta tsani alakar sa da only sister dinta. God knows tana son Sumayya har cikin ranta kuma zata yi iyakacin kokarin ta ta ga cewa alakar Sumayya da wannan tubabben bata cigaba ba, bata je inda su suke son taje dinba. She can’t imagine having nephews and nieces masu Christian blood a jikin su, masu kama da kedarai. Ta kara tsaki tana juyawa cikin gidan ta, dole zata nemi hanyar raba wannan alakar duk da tasan ba zata samu goyon baya daga Sumayyan ba ko Baba ko Inna but duk da haka she will find a way, zata yi shawara da zuciyarta kuma tadan zata samu mafita kamar yadda kullum zuciyar tata take bata mafita a duk problems dinta. Yanzu ma already ta bata mafita akan problem dinta da Hassan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button