TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya saki fuskarta jin bata ce komai ba. Ya yi taku biyu baya yana kallonta yace “akwai abinda kike boye min. Me kika sani wanda ni ban sani ba? Me kika aikata?kina son kudi na sani, ba kya son in bayar da kudin nan na sani, amma ina so ki san cewa kamar nayi na gama ne, ke matata ce, responsibility dina ce kuma zanyi iya kacin kokari na na ganin cewa na kula da ke na sauke duk wasu nauye nauyen ki da yake kaina. Amma dukiyar Hussain, no”

Ruqayyah tace “ni kuma zanga ta yadda zaka rabar da ita din, tsakanin ni da kai dan halak ka fasa, wallahi in dai ina numfashi ba zaka bayar da ko da kobo a cikin kudin nan ba, saboda kudin nan is as much mine as it is yours saboda ni matarka ce uwar yayan ka ce” bai ce mata komai ba sai ya juya yana kokarin barin dakin, shi duk inda tashin hankali yake yanzu baya baya yake yi dashi ba wai dan yana gudun mutuwa ba sai dan yana gudun wahala, yana gudun ya zama responsibility a gurin wadanda suke responsibilities dinsa saboda shi kansa yasan ciwo yana daf da kama shi indai rayuwa ta cigaba da tafiyar masa a haka.

Ta bi bayansa da kallo tana daga kafarta da kokarin zuwa ta tari gabansa, ta manta ma da problem din kafarta, jin kafar taki responding ya tuna mata da cewa kafar ta daina aiki wannan kuma ya kara tunxura ta tace “wallahi baka isa ba Hassan, wallahi baka isa ba kayi kadan wallahi. Wallahi sai dai ka zaba ko Hussain din da baya duniya ko kuma ni da yayana da muke da rai kuma muke da hakki akan ka. Wallahi ba zan taba barin ka ka aikata abinda kake da niyyar aikatawa ba, wallahi…..” Karar rufe kofarsa ya ankarar da ita cewa ya fita ya bata guri.

Ta zauna tana rusa kuka kamar wadda aka aiko mata da labarin mutuwar Baba da Inna a lokaci daya. Dan yadda take ji a ranta bata jin ko daya daga cikinsu ne ya tafi zata ji wannan bakin cikin. Yaran ta da suka gaji da jiran ta saka musu riga suka fara wasan su a kasa ta kalla, duk mafarkan ta tana hango yaran a ciki, tana hango cewa sun girma cikin dukiya da wadata ba irin yadda ita ta girma cikin talauci da kunci ba. Duk dan su take yi, shi kansa Hassan din da yake ta wannan firirita dan shi take yi dan shine zai zauna akan kujerar da take fighting for ba wai ita ce zata zauna ba. Shi wanne irin mutum ne mai zuciya kamar dutse? Da wani irin rikakken ra’ayi kamar dangin firauna.

Sai taji a ranta tana missing Minal, da tana nan da yanzu ta dauki waya ta kirata ta gaya mata problem dinta amma Minal bata da rai a yanzu kuma babu wanda ya sani sai ita kadai. Ta goge hawayenta tana tuno da yadda gawar Minal tayi a cikin mota da yadda kaurin konewar gawawwakin ya cika dajin, sai taji a hancin ta kamar tana shakar kaurin a yanzu. Tayi sauri ta girgiza kanta dan it has been very hard for her to keep that secret to herself sannan kuma Hassan yace duk wannan a banza? Gaskiya ba zata yiwu ba. So yake tayi biyu babu? Bayan ta tafka kuskuren da ita kamta tasan zai taba lahirar ta dan ta sami duniya shine zai ce duniyar ma ba zata samu ba? Wato babu duniya babu lahira kenan!

Hassan yana fita daga dakin ya dafe kujera saboda yadda yake jin bugawar zuciyarsa yana kara gudu sosai kamar zata fito daga kirjinsa, yana jin kalaman da Ruqayyah ta bi bayansa dasu amma kuma baya son ya koma su cigaba da rigima akan dukiyar Hussain. Dukiyar da babu abinda zata kara musu gabaki dayan su. Shin wannan ita ce matar da ya zabawa kansa? Ita ce kuma uwar daya zabawa yayan sa?

Duk su biyun babu wanda ya rintsa da niyyar bacci, haka ma Sumayya, a ranar itama bata samu tayi bacci ba tana ta bitar abubuwan da suka faru a ranar musamman maganganun mai gadin gidan su Adam, abubuwan daya fada sun nuna cewa akwai chance mai karfi na cewa Adam yana hannun iyayensa, wata kila sun jima suna bibiyarsa suna gudun kar ya fahimta ya sake gudu kamar yadda ya gudo daga Kano, suna binsa a baya da niyyar kidnapping dinsa idan sun ganshi shi kadai a haka har Allah yasa suka samu nasara ranar da Hussain ya mutu suka kama shi a hanyar Abuja, mai gadin yace matar da ta aiko musu da sakon inda Adam yake a gidan da Adam din yake aiki take, kuma duk gidan ita tana ganin babu wanda ya damu da wanzuwar Adam a gidan kamar Ruqayyah tunda har furta hakan tayi da kanta. Sai dai kuma ita kanta Sumayya tana fatan kar hakan ta kasance domin kuwa abinda zai biyo baya ba zasu taba jin dadin sa ba daga ita har Ruqayyah. Tana so tayi bincike dan ta san gaskiyar abinda ya faru amma tana ganin abune mai wahala ta samu amsar ta ta hanyar bincike dan bata san ta inda zata fara ba sai kawai ta samu kanta da addu’ar idan Ruqayyah ke da hannu Allah yasa tayi Confessing da bakinta dan wannan shine kadai solution, kuma kamar kullum tayi wa adam addu’ar samun guidance daga Allah.

Washegari Hassan bai bari ma sun hadu da Ruqayyah ba ya fita daga gidan da wuri saboda yau ne zasu yi pricing duk komai da komai na Hussain including motocin sa, da kuma gidan sa, sai dai kuma a ransa yaji yana son ya cire gidan nasa ya fasa siyar dashi. So yake sai ya gama pricing komai sannan zai gaya wa Aunty kafin ya siyar duk da yasan abin bazaiyi mata dadi ba amma yana saka ran in taji dalilinsa zata yi masa kyakykyawar fahimta kuma zata kara masa kwarin guiwa. Shi dai kam yayi damara baya jin akwai abinda zai saka ya fasa kudurin sa. Ruqayyah tana hango fitarsa itama ta jawo kafarta ta fito palo tana amsa gaisuwar da masu aikinta suke jera mata, sai kuma ta kira daya daga ciki ta aika ta gurin aunty tace taje tace in ji ta ta bata key din gidan Hussain, tun jiya ta yanke hukuncin abinda zata yi. Ta gurgunce ta kuma kurumce sabida babu yadda zata yi tunda wadannan Allah ne ya aiko mata dasu, kaddara ce, amma ba zata talauce ba kawai dan wani son zuciya irin na Hassan.

Aunty tayi mamakin aiken dan tasan Hassan yana da spare key din gidan Hussain a hannunsa kuma Ruqayyah tana son budewa a gurimsa zata karba ba a gurinta ba. Taso ta aika a tambayi Ruqayyah abinda zata yi da key din amma sai ta fasa saboda ita macece mai jan girmanta sosai bata son shiga abinda zai zubar mata da kima a idon na kasa da ita, ta kuma san yaran zamani da rashin kunya. Sai kawai ta dauko key din ta bawa yar aikin.

Ana kaiwa Ruqayyah, tea kawai ta sha ta tattara yaran ta bawa nanny dinsu sannan ta debi sauran sai gidan Hussain, ita da kanta ta bude gidan ta shiga, ta tsaya tana kallon palon tare da sauke ajjiyar zuciya a ranta tana jin ta shiga kenan wallahi, ba Hassan ba ko Hussain ya dawo daga lahira bata jin zata fita ta bar masa gidan. Nan take ta saka yaranta suka fara aikin gwaran gida, ta gaya musu cewa sun dawo nan da zama kachokan, suka yi ta murna abinsu, sai kuma ta aika gidan Aunty tana kiran yan aikin Fatima da da suke gidan bayan mutuwar Hussain kuma suka koma gurin Aunty suke zaune a can tace su zo suma ayi aikin dasu tunda sune suka san duk wani lungu da sako na gidan. A haka ta ja kafarta da kyar ta hau har saman, sai dai ta tarar wing din Hussain a rufe yake na Fatima ne a bude tunda jiya anzo an debi kayanta, amma kuma sai taga kamar ba’a diba ba dan furnitures din duk suna nan sai few abubuwa aka dauka. Ta kira wata a yaran gidan ta tambayeta “ba’a kwashe kayan Fatima ba dama?” Tace “sunzo sun diba, amma sunce sunbar furnitures din duk wanda zai zauna a gidan yayi amfani dashi” Ruqayyah ta gyada kai, lallai ma mutanen nan wato su kudi ba komai bane ba a gurinsu, ita dai gaba ta kai ta gobarar titi a Jos, dan haka kawai ta bude dakin Fatima aka fara gyara, sai da suka gyara komai tsaf can wajan azahar sannan ta koma part dinta ta fara hado kayata tana bawa yaranta suna shigar mata dashi gidan Hussain, sai a lokacin ta dauki wayata kira Sumayya. “Hello Sumayya? Nace ko zaki taho ki taya ni aiki? Yau muna tare wa a sabon gidan mu” Sumayya tace “sabon gida? Wanne irin sabon gida kuma? Yaushe kuka yi sabon gida” Ruqayyah tace “bayi mukayi ba, gidan Hussain ne can zamu koma” sai Sumayya taji wani iri, anya kuwa bai yi wuri ba su koma gidan Hussain su zauna? Tasan ya zama gidan su amma dai ai ta dauka zasu bari mutuwar ta lafa sosai tukunna kafin su tare. Sai tace “Allah ya sanya alkhairi, amma ba zan samu damar zuwa ba saboda nima ina gyara dakina yau tunda na kwana biyu bananan”. Sai Ruqayyah ta tabe baki kawai tace “shikenan, kwazo daga baya kuga sabon dakina” amma a ranta taji babu dadi, tana son duk sanda ta bukaci Sumayya tazo gurinta dan a lokacin ne take jinta fully satisfied.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button