TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A bangaren Ruqayyah ranar da ta sha mari a gurin Inna kusan kwana tayi ta kasa bacci, ba wai marin ne yayi mata zafi ba a’a yadda akayi mata marin a gaban kannenta sannan inna ta wanke ta tas da soso da sabulu shi yafi kona mata rai. Yanzu ai sai su raina ta su cigaba da kallon ta da sunan da Inna ta kira ta dashi “butulu”.

Ita kuma Inna hankalinta gaba daya a tashe yake da jin kalaman Ruqayyah, ita da kanta wai take ikirarin saita wa mijin da zata aura zama idan anyi auren su. Wannan kadai ya nuna cewa ita ba ta rike alkhairi a ranta ba akan auren nata, Inna taji tana jin tsoro, tana jin tsoron abinda Ruqayyah zata aikata a gidan mijinta. Sai taji a ranta cewa kamar ta bawa Baban biyu shawarar cewa ya dakatar da auren baki daya, amma kuma tana jin tsoron abinda Ruqayyah zata aikata in akace an fasa wannan auren, zata iya yin komai koda kuwa abinda zai lalata mata rayuwa ne, tsoron wannan yasa Inna Ade ta kasa yiwa Baba maganar.

Ita dai tuntuni ta san cewa Ruqayyah jarabawa ce a gare su ita da Baba, iyakacin iyawarta tayi tarbiyyar, ta bada ilimin, ta kuma yi addu’ar. Ba dan Allah ya saka sauran ya’yan sunyi turning out good ba da sai taga kamar laifin sune su iyayen amma yanzu su sun sani, Allah ya sani, sannan duk wanda ya san su ya sani cewa sunyi kuma suna yin iyakacin kokarin su. Allah shi ya barwa kansa sanin yadda zaiyi da Ruqayyah.

Da safe yaran suka zagaye uban. “Baba ba ka ga gidan ba, bandakin fa irin wanda ake korawa da ruwa ne” “kaga kujerun Baba? Wannan in inna ta zauna ba zata iya tashi ba” Sumayya ta fada tana tsokanar Inna, Inna ta harare ta tace “ai dai kinsan ba daga ruga aka dauko ni ba ko? Sai dai ki fada wa zazzagawa sune basu saba hawa manyan kujeru ba” Baba yayi shiru bai kula ta ba duk da ya fahimci tsokanar sa take yi, shi wannan lamari da yaran nan suka kawo masa yana da girma sosai, gida kuma? Har da dakuna kowa da nasa? Da bandakuna na zamani da palo mai kujeru da talabijin? Anya kuwa abinda yaron nan yake yi bai yi yawa ba? Anya kuwa ya dace ya karbi wannan kyautar? In ma zai karba ai kamata yayi ace sai bayan biki tukunna sai ya iya karba a matsayin surikin sa amma yanzu gani yake yi anytime yaron zai iya zuwa yace ya fasa auren. Inna tace “Baban biyu, nima gaskiya ina tsoron karɓar gidan nan, daga yadda suke kwatanta shi kasan ba karamin gida bane ba. Ya bar mu anan din mu tunda gashi nan har kana kokarin yin katangar nan” yace “har plaster nake so ayi wa dakunan nan ayi musu penti kafin bikin” yaran duk suka fara bata rai “dan Allah Baba, dan Allah Inna yace fa da sunan ka ya sayi gidan nan, kyauta ya baka shi, bana jin ko ba’a yi auren ba zai dawo da kalaman sa baya” Sumayya tace tana karya wuya. Sulaiman da Zunnur suka durkusa kusa da ita suna hade hannayensu “dan Allah Baba ka karba, dan Allah Baba ka karba”.

Baba yayi shiru yana kallon su yana tunani sannan yace “shikenan ki ce wa Hassana ta kira min shi tace in ya samu dama yau da magariba yazo ina son magana dashi..

Sakon yana zuwa kunnuwan Hassan ya gane cewa akan maganar gida ne, ya shirya ya taho yana addu’ar Allah yasa ba rejecting gidan Baba zai yi ba. A tsakar gida aka shimfida musu tabarma suka zauna daga can bakin kofar shigowa. Hassan ya gaishe shi cikin ladabi da jin kunya, Baba ya amsa sannan yace “jiya yara suka zo min da wani lamari mai girma, shine na kira ka inji daga bakin ka” Hassan yace “gaskiya ne abinda suka fada baba, ina kuma fatan ba za’a ki karba ba kamar yadda aka ki karbar kuduri na na bada jarin sana’a, yadda na hakura na bayar da aiki ina fatan wannan karan nima za’a dube ni a karbi wannan din. In ba’a karba ba gaskiya zanji babu dadi, zanga kamar……” Baba yace “kamar an raina?” Hassan yace “a’a kamar ba’a sona tunda ba’a son abin hannuna” Baba yace “ba haka bane ba, son naka da nake shi yasa nake maka haka. Bana son in cutar da kai” Hassan yace “ta yaya zaka cutar dani Baba? Karbar wannan kyautar ai faranta min zaiyi ba bakanta min ba” Baba yace “haka ne, amma ina matukar jin kunyarka” Hassan yace “Allah yasa hakan yana nufin za’a karba” Baba yayi ajjiyar zuciya yace “na karba Hassan. Allahu yayi maka albarka ya baka masu yi maka kaima a lokacin da kake bukata” Hassan ya sunkuyar da kansa, fuskarsa tana nuna irin jin dadin da yayi yace “Nagode sosai Baba, na gode da karamcin ka da soyayyar ka” Baba ya dago kai yana kallon sa, yaron kirki ne, sam bai dace da Ruqayyah ba, sai yaji kamar baiyi masa adalci ba.

Hassan da kansa ya turo da driver ya debe su zuwa sabon gidan su. Kafin su tafi duk suka shiga gidajen unguwa suka yi musu sallama tare da basu kwatancen sabon gidan su. Kayan sakawarsu kawai suka dauka da dan abinda suka san zasu bukata a sabon gidan sannan suka rufe dakunan su suka rufe gidan suka tafi, zuciyoyin su fal da mabanbantan feelings.

Yaran suna jin feeling na murna sosai, suna ganin sun taka wani babban matsayi a rayuwa kuma suna ganin wannan wani chanji ne mai kyau a rayuwarsu yayin da iyayen suke jin rashin dadi na barin gidan da suka yi shekara da shekaru suna zaune a ciki, suna kuma alhinin shiga wata sabuwar rayuwa wadda basu san menene a boye a cikin ta ba.

Ruqayyah kuwa a nata bangaren, ji take yi cewa wannan chanjin kamar misalin wanda zaije sama ne sai ya taka dutse, wannan ba komai bane a gurin ta, wani step ne da ta taka zuwa gaba.

Wannan kenan………..

A bangaren Gimbiya Fatima kuwa shirye shirye sun kankama sosai, a da lokacin da aka saka bikinta wata takwas ji tayi kamar ta dora hannu aka tayi kuka saboda ganin tsayin lokacin da kuma zakuwar da tayi na ganin ta kasance da hasken idanunta, Hussain. Sai gashi yanzu har watan bikin ya kama. Tana ta shirye shiryen ta iyayenta suma suna yin nasu. Duk tsarin gidan Hussain babu abinda bata sani ba dan tare suka tsara kayan su, sun kuma shirya duk events din da zasu yi. Ita a bangaren ta zata yi bridal shower a gidan babban yayan su a nan cikin garin kano, sai kuma kamu da yini da za’a yi rana daya anan cikin palace ranar Friday, ranar Saturday kuma za’a yi grand dinner da maimartaba ne da kansa ya shirya musu kuma har da ango da abokan sa da yanuwansa duk za’ayi. Ana saka ran zasu zo su wuni ranar Saturday din da daddare ayi dinner sannan su kwana sai da safe a daura aure su tafi da amaryar su zuwa Kaduna.

Duk wasu ashobis sun fitar uta da kawayenta wadanda yawancin su tare suka yi jami’a a Europe, sai wadanda suka yi secondary school tare a Abuja, sai kuma family friends dinta. Sun gama tsara komai kuma Hussain ya sakar musu kudi wanda wani lokacin har sai ta daga masa hannu dan bata son kawayen natakuma su mayar dashi saniyar tatsa dan shi duk abinda suka ce ya basu basu kawai yake yi. An aika an gano gida kuma kusan komai an gama siya jira kawai akeyi bikin ya kara matsowa sai aje ayi jere.

Sakamakon binciken da Hassan ya tura ayi masa a kano a kan Adam ya fito, kuma kusan komai yayi tallying da abinda ya fada banda abu daya. Hassan ya dago da kansa daga karatun report din yana shafa sajensa, fuskarsa da alamar damuwa. Ya dauko form din daya cike biography din Adam yana kuma dubawa dan yayi confirming maganar, sai kuma ya dauko wayarsa ya saka number din da Adam din ya bashi ya kira.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button