TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai dai kuma ganin cewa da akwai sauran lokaci ya sa har yanzu bai mayar da hankali wajen kammala ginin ba saboda so yake yayi shi a nutse, using the very best of komai, dan Hussain baya karbar komai in ba best ba.

Hassan ya bude motar sa yana shiga, Hussain ya leko da kansa yace “zanje fa” Hassan ya haɗe rai yace “kar Allah yasa kaje ɗin”.

Washegari Hussain ya shirya yaje. A kofar gidan da aka kwatanta masa da Google map ya tsaya yana karewa gidan kallo sannan ya juya yana karewa unguwar kallo, yana lura da yadda mutane yara da manya suke ta kallon motarsa. Ya dan sauke glass ya kira wani yaro wanda ya taho da gudu yana leka cikin motar. Hussain yace “ka shiga gidan nan kace wai ana kiran Hassana tayi bako” yaron ya girgiza kansa yace “babu Hassana a gidan” Hussain ya hade rai yace “babu Hassana kuma? Sai wa?” Yaron yace “akwai Sumayya akwai Ruqayyah” Hussain ya tabe baki yana sake kallon gidan, tabbas nan ne gidan ta yadda aka fasalta masa shi.

Yace “to kace ana kiran su duk su biyun” da sauri yaron ya shiga. Yana bude kofa kofar gidan suka kusa yin karo da Ruqayyah wadda taji alamar tsayuwar mota ta taho yin tsegumi, a ranta tana fatan Hassan ne ya dawo kuma gurinta yazo ba gurin Sumayya ba. Ta ja yaron gefe, “waye a waje?” ya wangale mata baki cikin murna yace “wani farin kyakkyawan saurayi ne yake kiran ku ke da Sumayya” ta bata fuska cikin mamaki “fari kuma? Baki dai ko? Ko baka gani sosai ba?” Yaron ya girgiza kansa yace “fari ne wallahi, tas ma kuwa”

Ta juya tana kallon dakin da Inna Ade take ciki sannan ta leka ta tsakanin kofa, ba irin motar ranar nan bace wadda Hassan yazo da ita, wannan ta ci uban waccan, ita bata taba ganin irin wannan motar ba ma. Ta koma da baya tana dafe kirjinta. Waye wannan kuma? Ko Hassan ne yayo mata aike a daya daga cikin motocin sa? Ko motar ya aiko mata da ita kyauta?

Muryar Inna Ade taji daga bayanta, “me kike yi a gurin nan Ruqayyah?” Ta dan tsorata kadan sai kuma ta saki fuskarta. “Wai wani ne yake kiran mu ni da Sumayya” Inna Ade tace “kuma shine kike leka shi” ta juya gurin yaron tace “kaje kace waye” yaron ya fita ya tambayi Hussain, ya danyi tsaki yana kallon agogon hannun sa yace “kace hussainin Hassan ne” yaron ya koma ya fada.

Ruqayyah ta dan bata rai. Me yasa shi Hassan ɗin ba zai zo ba sai ya bawa Hussain motarsa ta taho? Ko dai ya karbi shawarar Baba, ko kuma har yanzu yana tunani ne akan shawarar. Inna tace “ku saka hijaban ku ku je, zuwa yayi ku gaisa” sai ta dauki kudi a cikin kuɗin da Hassan ya ajiye musu shekaran jiya ta bawa yaron tace yaje ya siyo lemo guda daya da ruwan roba guda daya.

A tare suka fita, ya bi su da kallo yana studying dinsu har suka zo gaban motar suka tsaya sannan ya sauke glass din. Sumayya tayi masa murmushi, sai ya mayar mata kuma yaji bai kamata suna tsaye a waje shi kuma ya zauna a mota ba. Ya bude motar ya fito. Wani irin lugude zuciyar Ruqayyah take yi. What? Wannan ai yafi Hassan dinta haduwa, ya akayi dan uwansa ya fishi haduwa?

Ta sauke idonta kasa tana tuno karin maganar hausawa da suke cewa ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau.

Sumayya ce ta fara gaishe shi sannan Ruqayyah ita ma ta gaishe shi. Ya amsa yana rarraba ido a tsakanin su. Yace “wacce ce yayar tawa a ciki?” Sumayya tace “ka chanka” ya kalle ta ya kalli Ruqayyah da idonta yake kasa yace “hmmm. Hassan yace min hassanar sa tafi yaruwarta komai, hankali, nutsuwa, kyau, bla bla bla. Jiya haka ya kwana yana min sambatu duk ya hana ni bacci shi yasa nace yau dai sai nazo naga wannan Hassana na huta, kuma from all indications…” Ya nuna Ruqayyah “ke ce Hassanar” Ruqayyah taji sanyi a ranta, wato Hassan bai chanja ra’ayin sa ba, Baba bai yi convincing dinsa ba.

Sumayya tayi dariya tace “son kai yake yi fa da yace ta fini komai” Hussain yace “na yarda dake, ta dai fiki sunkuyar da kai. Kin fita fara’a kuma daga alama zaki fita son mutane” ya fada cikin sigar tsokana, Ruqayyah ta danyi murmushi tana wasa da bakin jihab dinta sannan tace “na gane niyyar ku, so kuke ku hade min kai dan kunga baya nan ballantana ya tare min” Hussain yace “ohhh ashe kina magana. Ni na dauka ai mu biyu zamuyi hirar mu ban da ke”

Yace “to Malama Hassana, nazo ne…….” Ruqayyah ta katse shi “Ruqayyah” yace “what?” Tace “Ruqayyah shine sunan” yace “ohh, ni kuma Hassana ake ta gaya min a kunnuwa na” tace “wannan shi kadai yake fada ai. Special” yayi dariya sosai yana bayyana dimple dinsa, Sumayya ma ta taya shi dariyar tana cewa “Ruqayyah yaushe kika kile har haka?” Hussain yace “wallahi Hassan ya taro match. Kuma kamar kin fada a kunnuwan sa” ta dan rufe fuska alamun kunya “kar ka gaya masa dan Allah”.

Yace “kinsan me? Naga alamar kamar zaku daidaita da Gimbiya ta, Fatima sunanta, ita ce wadda zan aura. Tunda taji labarin ki take addu’ar ku daidaita da Hassan sai a hada bikin mu nan da wata biyar” ya zaro wayarsa yana bude lock din yace “ki saka min number dinki sai in bata ta kira ki ku gaisa” ta karbi wayar tana kallon hoton da yake kan screen din. Hoton sa ne tare da wata kyakkyawar yarinya wadda kallo daya tayi mata ta san ta fita komai, taji wani abu ya tsaya mata a wuyanta yana so ya kawo hawaye cikin idonta

Ta yi sauri ta mika masa wayarsa tace “bani da waya ai ni” Sumayya tace “kasan yanzu ne muka gama secondary school, Baba kuma dama yace sai mun gama zai siya mana waya” ya dan bata rai yana tunani yace “ku ka gama ko zaku gama? ai ba’a gama exams ba an dai yi neco saura waec. Ba zakuyi waec din ba?” Suka yi shiru duk su biyun, sai ya fahimci bashi da amsa dan haka yayi saurin chanja topic din da cewa “amma dai zaku cigaba da karatu ko?” A tare suka ce “eh” yace “good, Allah ya taimaka”.

A lokacin ne yaro yazo ya kawo masa lemo da ruwa a jere akan karamin faranti tare da kofi akai. Sumayya ta karba sai ta bude motar ta ajiye masa sannan ta rufe. Yace “Nagode sosai. Dama kishirwa nake ji. Bara inzo in tafi kar in gajiyar daku da magana, ni bana gajiya da magana. Sai dai kuma gashi ban kawo muku komai ba” da sauri Ruqayyah tace “lah, babu komai, ai zuwan shine mafi muhimmanci akan wani abu” Sumayya ta kalle ta da mamaki sai kuma tayi saurin gyara fuskarta tace “haka ne” yace “a’a ba haka bane ba, ita kyauta ai abu ne mai kyau saboda tana kara soyayya a zukatan mutane, ko mai kankantar abu in aka baka shi kyauta sai kaji wanda ya bakan ya kara samun daraja a gurinka. Nima kunga yanzu ruwan da kuka bani ai naji dadi har cikin raina. Koda mutum ya fika komai na duniya in kuka hadu samu wani abu ka bashi, zaka kara daraja a gurinsa”

Ya cigaba “wannan yasa duk wanda na hadu dashi ina kokari inga na bashi wani abu da zai ke tunawa dani kuma yaji yana son mu sake haduwa. Ku ma kuma ba zaku zama exceptional ba. Ban taho da leda ba amma na san a jikina ba za’a rasa wani abu ba, ko cash ne” sai ya fara laluben jikin sa, yayi tsaki “these days sai mutum ya duba jikinsa yaji wai bashi da kudi”.

Ruqayyah ta sake cewa “ba wani abu fa, ka barshi kawai”.

Sai ya bude motar ya bude aljihun mota, sai gashi ya dauko rafar farare bugun Abuja, ya fito ya miko wa Sumayya, ga wannan kwa sayi jambaki” Ruqayyah tayi saurin rike hannun Sumayya duk kuwa da cewa sumayyan ba wai miko hannun tayi ba tace “uhm uhm, ba zamu karba ba gaskiya.” Da mamaki yace “saboda me?” Ta sunkuyar da kai still hannunta rike dana Sumayya Tace “kawai dai. Babu abinda zamuyi dashi. Mungode”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button