TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

ya ajiye wayar yana kallon Hussain daya koma da baya ya kwanta a kan gadon yace “zamu je ayi wannan test din daka gudo baka tsaya anyi maka ba. Anan zan tabbatar maka cewa likitan is wrong” Hussain yace “what if he is right?” Hassan yace “then zamu ne mi magani, babu wata cuta da bata da magani Hussain. You will have the best care in the world” Hussain yayi murmushi yace “you are beginning to sound like me. But you are forgetting something, even the best doctor in the world ba zai kara min second daya a cikin lokacin da Allah ya kayyade min ba a duniya. Ni ba mutuwa ce problem dina ba, dan haka ba zan yi going through wannan procedure din ta doctors ba, that chemotherapy treatment and those surgeries da ba zasu kare ni da komai ba. Ko so kake in koma kamar aljani kafin in mutu? So kake doctors su ringa gutsirar hanji na piece by piece har sai ya kare sannan su barni in tafi? In zan mutu Hassan na fi son in mutu in one piece. At least nafi son in mutu looking my best ba wai kwarangal da kai babu gashi ba” ya karasa maganar yana murmushi.

Hassan yace “wannan ba abin wasa bane Hussain. Look, dan Allah yace ka yarda da kaddara ba ya na nufin in ciwo ya kamaka kayi folding hannunka ka jira mutuwa ba. Promise me zaka bini mu tafi” Hussain yace “zan bika muje dan ayi maka confirming abinda ni na riga na sani. But I will not go through those cancer treatment processess”.

Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020The Surgery

Tun Ruqayyah tana zuba idon ganin saukowar Hussain har ta hakura ta hau saman, ta ga kofar dakin a rufe tasan kuma suna ciki, tayi tsaki ta shiga nata dakin, sai data yiwa twins dinta wanka ta shiryasu sannan ta fito dasu falo, still tana tunanin menene suke ta magana haka a cikin daki. Ta kira mai renon twins ta bata su tace su tafi gidan Aunty duk da tasan cewa basu gaisa da baban su ba ballantana uncle din su daya shigo, sai dai kuma ita bacci take so ta koma.

Suna tafiya Hassan ta bude kofa suka fito shida Hussain, fuskar Hassan kadai ta saka taji gaban ta ya fadi. Ya dan kalle ta yace “zamu fita, sai mun dawo” ta dan bata fuska “abinci fa? Ba ka karya ba fa” ya wuce ta yana cewa “ki ajiye min, inna dawo zan ci” shi a ransa ya ma manta da wani abu wai shi abinci. Hussain yace “sorry Madam. Na dauke miki miji ko? Aro na dauka zan dawo miki dashi in one piece”. Ta bi si da kallo har suka fita a ranta tana tunanin something is up, kuma koma menene it is not good.

A ranar suka gama binciken oncologist din daya kamata Hussain ya gani, a India yake, a ranar kuma suka fara kokarin booking yadda zasu ganshi.

Ruqayyah tana zaune a palo suka kuma shigowa tare shida Hussain, gaisuwar ta kawai Hassan ya amsa ya wuce daki, Hussain ne ya dan tsaya yayi wa twins wasa sannan yabi bayan Hassan din suka shige dakin sa. Ruqayyah ta saki baki tana kallon wani sabon salo wai kiran sallah da usur sai kuma taga Hussain ya fito shi kadai yayi mata sallama ya fita.

Bata bi ta kan Hassan ba sai data gama duk abinda zata yi ta kwantar da babies dinta tayi wanka tana shirin kwanciya sannan dai tace bara ta leka shi. A kwance ta tarar da shi ya lullube har kansa kuma ya kashe acn dakin. Ta zauna a bakin gado tana dan bude shi kadan sai dai tiririn da taji yana taso wa daga jikin sa kadai ya sa ta fahimci cewa bashi da lafiya

“subhanallah. Ai zazzabi ne a jikin ka mijina” ya bude ido sa yana kallon ta, tayi kokarin daga shi “ka tashi ka sha magani, ko in kira Hussain ya kaika asibiti?” Sai ya kama hannun ta ya rike “Hussain? Bana son komai ya samu Hussain” daga yadda yayi maganar ta san magagin zazzaɓi yake yi, tace “babu abinda zai samu Hussain kuma kai ma babu abinda zai same ka, zazzaɓi ne kawai kake yi” tayi kokarin tashi sai ya jawo ta jikinsa yana cewa “babu abinda zai same shi? Thank you, ohhh thank you” ya fada yana shigar da ita cikin bargon sa tare da lullube su tare.

Washegari Ruqayyah ta tashi da murnar Hassan ya fara saukowa, a ranar ne kuma doctor din da suka yi contacting jiya ya aiko musu da email na cewa zasu iya ganin sa next week, dan haka tun a ranar suka fara shirye-shiryen tafiya.

A dakin Fatima tana zaune tana kallon Hussain da yake shirya mata maganar zuwan da zasuyi India shida Hassan saboda Hassan din da yake son ganin likita a can. Tayi kamar zata yi kuka, “kuma yanzu tafiya zakayi ka barni? Ni baka taba yin tafiya ka barni ba fa dan Allah. Ni bana son ka tafi ka barni, zan biku kaji?” Yayi murmushi yana zama kusa da ita. “Haba Princess, in nace zan tafi dake Hassan ba zai ji dadi ba tunda shi yace ba zai tafi da Ruqayyah ba, kinga babu dadi ko? Itama Ruqayyah ba zata ji dadi ba. Ki bari akwai tafiyar da zan shirya mana muna dawowa daga indiyan nan, daga ni sai ke kuma duk kasar da kike so ita zaki zaba” ta fara biga kafarta kamar me shagwaba “ni dai bana so ka tafi ka barni. To ka lallaba Hassan din mana ya tafi da Ruqayyah kaga sai mu tafi gabaki daya”

Yace “Ruqayyah tana shayarwa kin manta? Tafiyar ba zata yi mata dadi ba da babies har biyu ko?” Fatima tace “zan ke tayata rainon ai, sai in karbi daya in bar mata daya” ya hade hannayensa “Please Princess kiyi hakuri, nima bana so in tafi in barki babu yadda zanyi ne” sai yaji maganar tasa tana bada wata ma’ana ta daban wadda tasa yaji jikinsa yayi sanyi. Ita kuma sanyin da taga jikin nasa yayi ne ya sa ta sauko. “Shikenan, Allah ya kiyaye hanya. Amma dan Allah kar ku dade. Kuma kullum sai munyi video call sau biyu” yayi murmushi yace “sau uku ma zamu ke yi, safe da rana da daddare”.

Ruqayyah kuma da Hassan ya gaya mata zancen tafiyar tasu cewa tayi “yanzu daga zazzaɓi sai tafiya India? Bana baka magani ba tun a ranar kuma har ka warke” ta fada cikin zolaya, sai dai baiyi dariya ba kuma bata ga alamar zaiyi dariyar ba. Yace “bamu san tsahon lokacin da tafiyar zata dauke mu ba amma muna saka ran insha Allah ba zamu dade ba”

Ta fara kokarin kawo masa korafin cewa ya kamata su tafi tare amma a take ya nuna mata hakan ba zai yiwu ba, daga shi sai Hussain zasuyi tafiyar. Dole ta ja bakin ta tayi shiru, a ranta tana mita “ni sanda ina da ciki har na haihu cewa yayi ba za’a fita dani ba, amma da yake shine daga yin zazzaɓi har anyi booking ganin likita a India”

Babu bata lokaci suka tafi, su ka bar yan’uwa da iyalin su da tunani amma kowa ya dauka Hassan ne marar lafiyar musamman yadda a cikin kwana biyu yayi rama sosai sannan annurin fuskarsa gabaki daya ya disashe. Suna isa Mumbai suka zarce asibitin da Dr din yake suka shigar da information dinsu da komai sannan suka tafi suka kama hotel. Ranar kwana suka yi suna hirar childhood memories, irin rashin jin Hussain da kuma kaffa kaffan Hassan, farkon kafa H and H da kuma yadda tafiyar ta kasance zuwa yanzu. Sai kuma suka yi hirar future dinsu yadda suke son ta kasance, yadda suke da burin yayansu su taso tare and maybe wata rana idan har an samu wadanda suka daidaita a tsakanin su a hada su aure.

Sai bayan da suka yi sallar asuba sannan suka kwanta suka yi bacci tunda appointment din Hussain sai 12. Bayan sun tashi suka yi wanka suka shirya suka fita waje suka ci abinci sannan suka tafi asibitin, duk cikin su babu wanda yake maganar ciwon Hussain amm kuma abin duk yana ransu suna kuma tsoron sakamakon da binciken zai bayar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button