TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya girgiza kan sa da sauri, it can’t be a memory, ranar da aka haife shi ne, ta yaya zai samu memorin abinda ya faru ranar da aka haife shi? Ya shafa gashin fuskarsa da hannayensa biyu “this is crazy, it can’t be” sannan ya lura cewa magana yake yi shi kadai.

Ya goge ruwan fuskarsa dana hannunsa a jikin towel sannan ya dawo cikin Bedroom din ya kalli agogo, karfe daya dai dai, ya rage ac ya koma kan gado ya kwanta. Maybe gobe yaje asibiti gurin Moon ta duba kwakwalwar sa, maybe ya fara tabuwa.

Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo screenshot na transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.???????? TAGWAYE ????????

By

Maman Maama

Episode Two: The Beginning

Labarin ya samo tushen sa na farko ne daga wasu ma’aurata biyu, Alhaji Aminu da Hassana. Alhaji Aminu dan kasuwa ne kuma maaikacin gwamnati, yana kuma da dukiyarsa dai dai gwargwado. Asalinsa dan Gombe ne, zama da aiki ne ya kawo shi Kaduna inda anan ne tushen labarin yake. Matarsa Hassana ita ma ƴar Gombe ce, daga can ya auro ta ya taho da ita Kaduna, ganin cewa bata da kowa a Kaduna ya saka iyayenta suka hado ta tare da kanwarta Amina dan ta ke debe mata kewar gida kuma take tayata yan aiyuka.

Amina a lokacin tana da shekaru goma sha biyar. Dan haka suna zuwa Kaduna aka saka ta a makaranta dan ta cigaba da karatunta, kuma yayarta da Alhaji Aminu suka rike ta sosai. Shekara biyu da auren Alhaji Aminu da Hassana sai Allah ya bata ciki, ciki mai cike da tarin laulayi tare da tarin girma. Inda tun a awon farko aka tabbatar wa Hassana da cewa tana dauke da tagwaye. Hakan ya saka su cikin matsanancin farin ciki duk kuwa da cewa dama suna saka ran hakan saboda kasancewar Hassana tana da abokiyar tagwaitaka ya saka chances dinta na haihuwar tagwaye ya zama yana da yawa.

Ganin wahalar da cikin yake bata ya saka mahaifanta suka nemi su tafi da ita gida ta haihu a can amma son da Aminu yake yi mata ita da cikin yasa ya kasa barinsu su tafi ya nemi a bar masa matarsa shi zai ke kula da ita da kansa. Aka bar masa ita, ya kula da ita tamkar sabon kwai, har lokacin haihuwar ta yayi.

Da farko sanda ta fara nakuda likitoci sun dauka zata iya haihuwa da kanta, sai data yi awanni babu wani progress sannan aka fara shawarar yi mata aiki dan gudun samun matsala. Sai da aka gama shirya ta tsaf sannan kuma sai jini ya balle mata, a haka akayi mata cs aka fitar da tagwayen maza, masu kama daya, sai dai daya ya dauko fatar babansa “baƙi” dayan kuma yayo fatar Hassana “fari”.

Bayan an dawo da ita dakin hutawa ne ta farfado aka saka mata jariran a hannayenta biyu, Hassan a hannun dama, Hussain a hannun hagu. Ta rungume su a jikinta, a haka Allah ya dauki ranta. Fadar bakin cikin Aminu tamkar bata lokaci ne, dan mutane har sun fara tunanin ko zai bita ne, amma sai soyayyar yayansa ta danne bakin cikin rashin matarsa.

Da farko anyi niyyar karbar yaran daga hannunsa a tafi dasu Gombe gurin kakannin su amma Aminu yace sam babu mai raba shi da yaransa. Wannan yasa bayan dan gajeren zama tsakanin iyayensa dana Hassana aka yanke shawarar aura masa Amina. A gurin aka biya sadakin aka kuma daura auren. Bayan dan karamin biki a Gombe aka dawo da amarya kaduna gidan mijinta tare da tagwayen ƴaƴan ta.

Da farko Amina ta dauki auren ta tamkar wasan yara dan ita babu komai tsakanin ta da Alhaji Aminu bayan mutunta juna, ganinsa take tamkar yayanta da suka fito ciki daya. Abinda yake gabanta kawai shine karatunta da kuma marayun da aka bar mata wadanda ta dauki son duniya ta dora akan su, dan har ba’a iya banbance wanda yafi son yayan a tsakanin ta da Alhaji Aminu wanda kullum a jikinsa suke bacci.

An samo mata matar da zata ke tayata kula da yaran saboda lura da karancin shekarun ta da kuma makarantar da take zuwa, amma fa tana dawowa zata karbo yayanta. Ranar nan bayan ta dawo daga school ta samu mai renon tace “Baba Yaha Dan Allah ko kinsan maganin da za’a sha ruwan nono ya zo?” Baba Yaha ta kalle ta da mamaki tace “me zaki yi da ruwan nono Amina?” Tace “a makaranta an gaya mana irin amfanin nonon uwa agurin jarirai, yaran nan nake tausayi, su basu samu wannan alfanun ba tunda kinga madara suke sha. Shine nake so in samu magani insha sai inke basu nawa” baba Yaha ta jinjina irin soyayyar da Amina take yiwa yaran sannan tace “to wannan dai ba magana ta bace ba, kije ki samu mijinki kuyi shawara a tsakanin ku, in ya amince shikenan sai in samo miki, amma in bai yarda ba dole ki hakura. Dan haka sai ki lallaba shi”.

Da wannan Yaha ta kashe maganar, dan a lokacin babu yadda za’a yi Amina ta samu Alhaji Aminu da magana makamanciyar wannan saboda sam basa irin wannan da shi, ko wasa ma basa yi saboda shi ba mutum ne mai son wasa ba.

Amma tsakanin mata da miji hausawa suka ce sai Allah. Tagwayen suna da shekara biyar a duniya sai ga Amina da ciki. Ai kuwa ranar da tagwayen suka fara lura da cikin a jikinta suka sakataa gaba da jerin tambayoyi har sai da ta gaya musu cewa baby ne a cikin, baby zata haifa musu watarana. Nan suka fara tsalle a saman gadonta suna adungure zuwa kasa. Alhassan yace “Please, Please aunty ki haifa mana namiji dan muke wasa tare” Alhussain yature shi yace “me za’ayi da namiji, anyi ta haihuwar mazan kenan? Mace zata haifa mana shikenan na samu budurwa” nan sai fada, harda kokawa, sai da kyar ta raba bayan sun gama doddoke ta. Sannan ta zauna tana dariyar sokonci irin na Hussain, ko ta yaya yar da zata haifa zata zama budurwar shi?

Haka yake shi Hussain, akwai surutu, akwai fitina, akwai karambani kuma akwai kokari a makaranta. Shi kuma Hassan shine mai wayo, manyance, da zarar magana. In yayi wani abin zata ce yafi karfin shekarunsa, komai sai ya nuna kamar ma ya fika iyawa kuma ba wai iyawar yayi ba. Komai na shi careful yake yinsa, in dai taga anyi barna to tasan Hussain ne, shi ko abinci kika bashi daga kitchen ya kawo daki to sai ya zubar a hanya.

Hussain ne yayi nasarar wannan musun nasu. Dan mace ta haifa wadda aka mayar mata da sunan Hassana kuma ake ce mata Hassana ɗin. Daga ita kuma sai ta haifi Safiyya, Khadijah, Nafisa, sannan Zulaihat. Duk kusan a jejjere tayi su. Daga nan kuma sai ta dakata tukuna tace sai sun girma zata sake wani set din.

Amma Allah baya barin wani dan wani yaji dadi.

A shekarar da tagwayen suka gama secondary school dinsu a shekarar ne Allah yayi wa Alhaji Aminu rasuwa bayan yar gajeriyar jinya. Ya mutu ya bar mata daya da yaya bakwai. Maza biyu mata biyar.

Wannan mutuwa ta taba ba wai family dinsa ba har wadanda suka sanshi da sauran abokan aikinsa kowa sai da ya koka kuma ya tausayawa iyalinsa, kasancewar su kanana babu wanda za’a ce ya rike kansa ballantana ya rike yan uwansa, ita kanta uwar ba wasu shekarun kirki ne da ita ba.

Bayan anyi arba’in sai yan’uwa suka nemi su koma Gombe su zauna a cikin dangi. Hussain ya shafawa fuskarsa toka ya ce babu inda zasu je “yanzu yaran nan sai a cire su daga makarantun su kenan? So kuke yi mu koma can a fara yi mana dauki dai dai? Wannan uncle din ya dauki uku wancan ya dauki biyu wannan auntyn ta dauki daya?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button