TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Amma kuma sai wata zuciyar tata ta tuna mata da Fatima, Fatima mata ce a gurin Hussain wadda a koda yaushe zata iya samun ciki dashi, in kuwa ta haihu dashi to H and H yayi mata nisan da komai gudunta ba zata iya kamo shi ba. Tun da ta hadu da Hassan take mafarkin zama matar CEO na H and H, har yanzu kuma wannan mafarkin nata yana nan sai ma abinda ya karu, but a da bata san ta inda zata fara ba, a yanzu kuwa ta sani, already har plan ya fara forming kansa a cikin kanta.

Tayi murmushi tana kallon kanta a madubi tana hango kanta a matsayin matar CEO sannan kuma a matsayin CEO watarana.

Tana kwanciya Hassan ya shigo, daga alama daga wanka yake dan jikinsa da ruwa ya zauna a kusa da ita yana kallon fuskarta. Tayi masa murmushi “barka da shigowa mijina” ya shafa fuskarta “wai har kin kwanta? Ina can muna ta hira da Aunty da yara” tace “nima ban dade da kwanciya ba, muna ta hira da Sumayya” yace “I hope everything is okay a gida ko? Zuwa gobe sai muje mu gaishe da su Baba” ta gyada kai, yace “akwai abinta kike bukata ne?” Ta girgiza kanta, “babu komai mijina, na gode da kulawa” yayi mata murmushi “anything for my wife” ya dora hannunsa a marar ta “kuma uwar yaya na” ta dan bata fuska kadan, yace “”lafiya? Tace “kawai dai bana jin dadin na samu ciki Fatima bata samu ba” yayi dariya “shi ciki Ruqayyah Allah ne yake bada shi ga wanda yaso a kuma lokacin da yaso. Nata lokacin yana nan zuwa” tace “haka ne. Kawai dai bana jin dadin yadda har ta fara damuwa da hakan, dama ta sha gayamin yadda take son ta samu ciki da wuri, kullum zancen ta kenan. To kuma sai gashi ni da ban saka rai bama na samu. Yanzu kullum maganar ta akan cikin nan ne, ni har bana son mu zauna mu biyu daga ni sai ita sabod labaran data ke ta bani na wahalhalun ciki da haihuwa, da yadda ake mutuwa a gurin haihuwa. Ni shi yasa har yanzu banji ina son cikin ba saboda tsoro nake ji wallahi” tana lura da yadda yana yin fuskarsa ya chanja, ya kamata ya tashe ta zaune yace “look, duk karya take yi miki babu wani wahala a ciki kin ji ko? Ina nan tare da ke in ma akwai wahalar to tare zamu sha ta ni dake kina ji na?” Ta gyada kai, yace “kuma daga yau, kar ki kara zama ki saurari irin wadannan maganganun daga gurin ta” ta tabe baki tace “ai ko baka fada bama na dain kulata ni, tunda har ta iya bani shawarar in zubar da cikin nan ai na gane cewa ba abokiyar shawara ba ce ba” ya bude ido “what?” Tace “eh mana, ranar da muka je Egypt ai abinda tace min kenan, wai nayi kankanta da haihuwa tana tsoron kar in samu matsala a gurin labour gwara in zubar in na kara girma sai in kuma samun wani” Hassan ya girgiza kansa yana tunanin girman maganar, wannan ba maganar da ya kamata yayi shiru bace ba, maganar day kamata ya kira family meeting ce akanta, amma kuma Hussain, baya son abinda zai tab tsakanin sa da Hussain ko da kuwa a cikin mafarki ne.

Ya dafe kansa yanajin kamar kan zaiyi masa ciwo. Ya dago ido ya kalle ta yace “kin tabbatar haka tace miki?” Tace “eh fa. Wai magani zata karbo min insha shikenan, wai sai muce muku bari ne nayi” yace “okay. Daga yau kar ki yarda ta kara gaya miki magana kiyi amfani da ita, kar kuma ki yarda ta baki wani abinci ko abin sha ki karba. I will think about it zan san matakin da zan dauka akai”

Kwana biyu bayan nan da sassafe wayar Fatima ce ta tashi Ruqayyah tace “Kina nan kina baccin naki ko? Ki taso ki taho gym akwai wani abu da zan nuna miki” ta kalli agogo, karfe takwas saura. Tayi tsaki, ita bata san me yake damun Fatima ba, ga kudi har kudi amma ace mutum ba zai huta ba? Sai kuma ta mike, bata san menene kiran ba maybe wata opportunity ce zata yi presenting itself. Sai dai kuma yau ce rana ta farko da zata taka kafar ta zuwa gidan Hussain. Bata san me zata gani ba amma ta shirya wa kanta gamin koma menene din. Tana shiga a bakin kofa ta ga wata a cikin yaran Fatima tana jiranta sannan tayi mata jabora zuwa inda fatiman take, da ido Ruqayyah tabi tafkekem benen da yayi sama, sannan kuma ta zagaye idonta a palon da suke wucewa ta tsakiyar sa. “Allah dai ya kai damo ga harawa, ko bai ci b yayi birgima”.

A katon gurin da aka cika da kayan motsa jiki ta samu fatima da kananan kaya a jikinta, ta karaso gurin t tana murmushi “sleepy head ta tashi. Ina tashi da safe na tun ki da kuma halin da kike ciki shine nayi browsing irin exercises din da ya kamata masu ciki suke yi dan samun karfin jiki da kuma karin lafiya” ta jata suka zauna, “kin ga, wadanda aka fi so sune swimming, walking da running sai dancing, wannan kuwa ni ba zan koya miki ba sai dai Hassan ya koya miki” tayi dariya ita kuma Ruqayyah tayi murmushi, ta cigaba “kin tab jin kegel exercise kuwa?” Ruqayyah ta girgiza kanta, Fatima tace “to ki bude kunnuwan ki yau zan koya miki shi. Exercise ne da ake yi na pelvic floor muscles, maana duk tsokar da take mara. Yana da kyau sosai agurin mace ko da kuwa ba masu ciki ba. Yana karawa tsokar gurin kwari da elasticity yana kuma matse matan da suka fara budewa. Ga masu ciki kuma yana karawa tsokar gurin karfi yadda zai taimaka sosai a gurin haihuwa. Yana kuma preventing tear. Yadda ake yi shine zaki yi kamar kina rike fitsari haka, amma ki tabbatar cewa marar kika tike ba wai cikin ki ba, kiyi counting to ten sai ki saki sai ki sake yi a haka har sai kin gaji, zaki iya yi a kowanne lokaci a kuma ko wane yanayi, za kuma ki iya yi idan kuna tare da Hassan” ta sake dariya. Sannan tace “ga kayan motsa jiki nan a nan, akwai swimming pool nan in kika bude waccan kofar, duk sanda kika so kizo kiyi abinki. Yanzu bara in nuna miki yadda ake amfani da kayan gurin nan” suka tashi ta zagaya da ita tana nuna mata komai, tana kuma nuna mata wadanda ya kamata take amfani dasu da wadanda zasu iya cutar da ita. Ta kunna mata treadmill tayi setting dinta a slow pace sannan ta shiga shower room din da yake jikin gym din ta kunna shower tana wanke gumin da tayi.

Tana shiga Ruqayyah ta sauko. Sai data gyara muryar ta sannan ta kira Hassan, da muryar kuka tace “kana ina? Kazo ka taimaka min, ina jin bari zanyi” cikin tashin hankali yace “what? Kina ina? Me yake faruwa?” Tace “ina wani gurin su Fatima, tun dazu ta saka ni nake ta exercise kuma na gaya mata mara ta ta fara ciwo amma taki ta barni, sai yanzu data shiga toilet na samu na kiraka, gashi yanzu ciwo take min sosai kamar zan mutu, dan Allah kazo ka taimaka min wallahi ina son baby na” ta sake saka kuka” ya kashe wayar da sauri ya tafi gidan Hussain a miliyan.

Ta cigaba da kukanta tana rike da marar ta, yana shigowa Fatima tana fitowa daga toilet, daga ita sai towel, ta dan tsorata ganin yadda ya shigo a fusa ce, sai kuma ta fara kokarin neman abinda zata rufe jikinta dashi amma babu wani abin kirki a kusa da ita. Direct gurin Fatima ya dosa, cikin tsoro tayi saurin cewa “lafiya?” Ya daga hannu kamar zai mare ta, ta rintse idonta tana jikinta yana daukan bari a lokaci daya, bai mare tan ba amma sai ya daka mata tsawa “munafuka, stay away from my wife” sai kuma Ya tafi gurin da Ruqayyah take ya dauke ta chak yayi hanyar waje da ita. A bakin kofa yaga Hussain, yaba tsaye da sakakken baki idonsa yana kallon matarsa half naked, scared to the bones, a tsaye a gaban Hassan daya ke mata masifa. Ba tare da Hassan yace masa komai ba ya wuce shi ya fita, Ruqayyah rungume a kirjinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button