TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai kuma wani tunani yazo masa, tunanin da ya sa ya mike straight yana mantawa da ciwon da yake ji a zuciyarsa ya karasa gabanta tare da rike hannunta yace “what else did you do saboda kudin Hussain? Me kika yi? Did you cause the accident? Did you kill Fatima and her baby saboda kici gadon su?” Tayi kokarin kwace hannunta amma karfin rikon da yayi mata yasa ta kasa kwacewa, cikin wata irin budaddiyar murya yace “answer me!” Saboda karfin muryar da yayi mata magana da ita sai da taji dakin ya motsa, ta kalle shi taga yana yi mata wani irin kallo mai nuni da cewa zai iya yi mata komai, ta kalli cikin idonsa tace “wallahi, tallahi, billahillazi la ilaha illa huwa ban kashe Fatima ba ballantana abinda yake cikinta, kuma bani nayi sanadiyyar accident din mu ba” a idonta yaga cewa gaskiya take fada masa sai ya saketa, ta matsa baya tana murza hannunta inda ya rike din, ya juya hannunsa dafe da kirjinsa zai bar dakin sai tace “ina sake tuna maka, kar ka bayar dako kwandala a kudin nan” ya juyo yana kallonta da juyayyun idanuwa yace “are you threatening me?” Direct Tace “yes” ya juyo a kufule yace “me zaki yi? Idan na rabarda dukiyar mezaki iya yi akai? And after duk abinda kika gaya min kina tunanin zanyi abinda kike so?” Tace “ba zaka yi ba amma ni zan saka ka kayi. Ba dai Hussain ba? Ba dai dan kana son Hussain ne kace zaka rabar da dukiyar sa ba? To albishirinka, in dai kayi haka ni kuma sai na tabbatar nayi destroying duk wani kykykyawan fenti da Hussain ya shafa wa kansa sanda yana da rai, I will make sure mutanen da suke sonsa suke kuma yi masa addu’a sun dawo suna kinsa suna kuma tsine masa” yaji tamkar ta saka mashi ta chaki zuciyarsa, yace “and ta yaya zaki yi hakan?” Sai ta koma bakin gado ta dauki Hussain da yake kwance tace “zan je gidajen rediyo in fadi cewa wannan yaron dansa ne ba naka bane ba, in ce raping dina yayi har na haife shi. Nasan wasu ba zasu yarda ba amma da yawa zasu yarda saboda mutane sunfi yarda da labarin karya aka na gaskiya. Zan ce kudinsa na cult ne, ta yaya Mutun mai kananan shekaru kamar sa zai tara kudade irin wadannan? Zan fada cewa baban ku ya fara bayarwa, shine silar yin kudinsa, zan kuma ce sanadiyyar mutuwar sa shine matarsa aka ce ya bayar tare da abinda yake cikinta, shi kuma yaki bayarwa shine suka sanye jininsa a gabanka tare da drivern ku shi yasa drivern ya bata har yau ba’a ganshi ba, sannan kuma suka yi causing accident dinda matar da mutu da tsohon ciki dan su dauki fansar kin bin maganar su da yayi. Am sure wasu ba zasu yarda ba amma wasu zasu yarda. Kuma am sure su kansu wadanda basu yarda ba dinzan saka musu doubt a kan sa. Zan kuma ce wannan dalilin ne yasa ka rabar da dukiyarsa saboda kace ba zaka iya cin dukiyar haram ba………”

Wata shakada yayi mata tare da bugata da bango ce tasa sauran maganar ta tsaya a makogwaronta, idanuwan ta a waje, ta saka hannunta duk biyun tana kokarin raba hannunsa da wuyanta amma ta kasa, a take ta fara jin kamshin mutuwa, ta fara fitar da rai da rayuwa, lallai tayi playing too bad dan wannan rikon da yayi mata bata jin zai sake ta har sai numfashin ta ya bar jikinta. Ya fara magana da karfi kamar zai tsaga dakin “why??! Why?! A kan kudi? Akan kudin da baki san ta yadda yayi ya tara su ba? Akan sa zaki yi ikirarin yi masa wannan mugun sharrin? Saboda duniya? Saboda kina so ki samu duniya, Allah wadaran ki Ruqayyah. Allah wadaran haduwata dake Ruqayyah. Kaico na, ina ma dai na mutu a ranar dana hadu dake da ban kawo wa family na jaraba ba. Allah wadaran aure na dake Hassana”

Kafafunsa yaji an kama ana jan wandonsa, ya sunkuyar da idonsa da yake cike da hawaye zuwa kasa yana kallon yan biyun sa da suka rike kafafuwan sa suna kuka, bai ji shigowar su ba bai kuma ji kukan su ba kawai taba shin da suka yi ne ya dawo da hankalin sa kansu. “daddy don hut mommy” yusuf ya fada yana matso hawaye, Aminu yaje ya kama rigar Ruqayyah data kusan suma saboda azaba yace “mommy mommy”.

Hassan ya cikata da sauri yana ja da baya yana girgiza kai, ta durkushe a gurin tana jan numfashi da kyar hawayen azaba yana zubowa daga idonta. Yaran suka tafi da gudu suka fada jikinta suna kuka ita kuma ta rungume su tana kallon Hassan. A hankali yace “Baba da Inna sunyi asarar haihuwa”

Sai ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba yabar gidan, ya shiga mota ya dauki hanyar gidan su Ruqayyah a hanya yana iya kacin kokarin sa dan ganin bai concentrating akan maganganun ta ba har yaje kofa gidan yayi packing, yana fitowa Baba yana tsayawa a cikin Napep dinsa, amma ganin yanayin Hassan kadai ya saka hankalin sa ya tashi ya kira Sulaiman da sauri suka kama Hassan din da kyar yake iya taka kafarsa suka shigar dashi cikin gida suka ajiye shi a palo suna ta tambayar shi “lafiya Hassan? Wani abu ne ya faru? Wani ne ya kuma mutuwa? Ko Ruqayyah ce?” Hassan ya dago kai yana kallon Baba yace “Ruqayyah ce Baba, amma ba mutuwa tayi ba, mashi ta dauko ta soke zuciyata da shi” Baba ya dafe kansa, tabbas ranar da yake gudu kuma har ya fara tunanin ba zata zo ba tabbas tazo yau. Ruqayyah tayi aika aika, kuma daga yanayin Hassan yasan abinda tayi yafi abinda yake tunanin zata yi din. Ya wuce duk lissafin sa.

Ya dago kai yana kallon Hassan, yana kara ganin rashin dacewar Hassan da Ruqayyah sai yace “Hassan zan roke ka wata alfarma duk kuwa da bansan abinda Ruqayyah tayi maka ba” Hassan ya fara girgiza kai tun kafin yaji alfarmar dan ba zai iya yafewa Ruqayyah na, amma sai yaji baba yace “Sulaiman dauko min takarda da biro” Sulaiman yaje ya kawo sai Baba ya mika wa Hassan yace “dan Allah Hassan, dan Annabi, ina rokon ka ka saki Ruqayyah” Hassan ya kalli Baba sai yaga cewa har cikin zuciyarsa hakan yake nufi, ya dauki biron ya dora akan takardar, lallai yasan Baba ya gaya masa haka ne dan ya cire masa nauyin sa kar yaga mutumcin su ya kasa sakin Ruqayyah shi yasa ya zamanto shine ma ya roke shi, sai yayi rubutu kamar haka…

“Ni Hassan Aminu Abdullahi na saki matata Ruqayyah Yusuf saki uku”

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan ???? kwasar garabasa
Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin AllahThe Fifth Wave

“Ni Hassan Aminu Abdullahi na saki matata Ruqayyah Yusuf saki uku”

Ya ajiye biron, amma sai ya kasa mikawa Baba takardar duk da yasan baban ba iya karatu yayi ba balle ya karanta abinda ya rubuta, sai dai a ransa da ace ana iya yin saki goma da kuwa tabbas shi zaiyi wa Ruqayyah. Dan babu abinda yake nadama a yanzu irin aurenta, babu abinda yake dana sanin yi irin hada zuri’a da ita, babu kuma abinda yake tausayi irin yayan da suke a tsakanin su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button