TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Nan take hankalin Sumayya ya kuma tashi, a dole Hassan ya dauke ta a mota suka bi baya ambulance din da doctor din yasa Ruqayyah a ciki suka tafi asibiti suna bayar da sakon cewa idan yara sun dawo su tafi gidan Aunty. A asibitin anyi duk abinda za’a yi dan ganin an tashi Ruqayyah daga bacci amma abin ya gagara, suna can suna ta abu daya har yamma har aka yi sallar magrib sannan ta farka tana jinsu suna ta maganganu can nesa, babu hearing aid dinta dan haka bata fahimtar abinda suke cewa, sai ta bude idonta a hankali ta sauke shi akan Sumayya da take tsaye suna magana da wata nurse akan tests din da doctor din ya rubuto wa Ruqayyah, yawancin su akan lafiyar kwakwalwar ta.

Ruqayyah ta mayar da idonta ta rufe sannan da dan karfi tace “me kike yi anan?” Sumayya ta juyo da sauri tana tahowa inda take sai Ruqayyah ta daga mata hannu tana yi mata alamar ta dakata daga inda take “babu ni babu ke. Maci amana. Kamar yadda kika ce babu ke babu ni saboda adam to nima babu ni babu ke saboda Hassan” Sumayya ta tsaya daga inda take ta kasa karaso wa ballantana tayi kokarin kare kanta. Duk da tasan ko tayi maganar ma Ruqayyah ba jinta zata yi ba tunda babu hearing aid a kunnenta.

Ruqayyah ta dafa gado ta mike zaune, tana jin jikinta wani iri sannan kuma kanta yana wani mugun sarawa kamar zai tsage biyu, ga cikinta kamar an yashe duk abinda yake ciki. Idonta da yake cike da tsana akan Sumayya, bata taba tunanin akwai ranar da zata zo wadda a cikin ta zata tsani Sumayya ba amma sai gashi yau ranar tazo. Ta dauke kanta ta daina kallon ta cikin tsawa ta kuma cewa “ki fita daga nan nace. Bana son ganin ki ba tsane ki na tsani kowa na tsani komai, bana bukatar ku babu ni babu ku kar ku sake nema na kar ku sake zuwa inda nake kar ku saje tunanin ma akwai wata alaka a tsakani na da ku”

Sumayya ta karasa da sauri ta kama hannunta sai ta ture ta da karfi, dai dai lokacin da Hassan ya shigo, kallo daya Ruqayyah tayi masa ta juyar da kanta gefe hawaye masu zafi suna zubowa daga idon ta.

Gani tayi yayi mata kyau, irin kyan da bata taba tunanin yana dashi ba, irin kyan dabata taba gani a gurin sa ba sanda yana nata sai yanzu da ya zama ba nata ba tukuna. Sanda yana nata bata kallon sa, wadansu take kalla shi yasa bata taba zama ta yabi surar sa ba, kamar yadda gidan Hussain kafin ya zama nata take ganin sa kamar shine aljannar duniya yanzu kuma daya zama nata sai ya koma mata kamar makabarta, sanda bata da kudi kuma sai ta ke kallon masu kudi a matsayin wadanda basu da wani problem a duniya, yanzu kuma da tayi kudin sai taga a yanzun ne ma problems suka fara mata.

Kaicho….

Hassan yazo da sauri ya rike Sumayya yana janye ta daga kusa da Ruqayyah, ya saka hanu ya goge mata hawayenta a kunnenta ya rada mata “let’s go home”.

Har sun kai bakin kofa Sumayya ta sake juyowa ta kalli Ruqayyah, sai suka hada ido and she can see the heart break da yaje idon Ruqayyah and her heart went out to her. Har suka je gida basu yi magana da, suna tsayawa sai Sumayya ta roki Hassan ta shiga gidan Ruqayyah ta saka aisha ta hada kayan da ta san Ruqayyah zata bukata a asibiti ta hada da hearing aid dinta sannan ta saka driver ya tafi da ita asibiti ita kuma Ruqayyah ta dawo gida.

Dakinta ta wuce direct tayi alwala tayi sallah sai ta samu kanta da kuka a sujjadar ta tana rokawa Ruqayyah dai-dai to a rayuwarta. Sai data idar sannan ta shiga toilet tayi wanka. Tana fitowa suka hada ido da Hassan a zaune a bakin gadonta, a guje ta juya ta koma bandakin tare da rufo kofa, dariya ta kama Hassan, dama yana sane ya zauna dan yaji motsinta a toilet din yasan kuma zata fito babu kaya. Sai yaja pillow ya kwanta kafafuwan sa a kasa hannayensa a rungume a kirjinsa idonsa akan toilet din. Ya san dole zata fito shi kuma yana nan yana jira.

Ta jima a tsaye tana mayar da numfashi, Inna lillahi, yau ya zata yi? Ta yi ta dube dube babu wani abu da zata rufe jikinta dashi, towel din nan na jikinta shikenan sa dan ko kaya dama bata shigo dasu ba da towel din ta shigo. Ta jingina a jikin kofar tana tunanin abinda zata yi, ta jima a haka sannan ta leka ta ramin key ta hango shi yana nan a kwance akan gado. Ta dafe kanta tana jin ana kiraye kirayen sallar ishai, ga sanyin toilet din ya fara ratsa ta tasan kuma in tayi wasa yanzu zata kama zazzaɓi.

Ta danyi knocking kofar toilet din sannan ta dan bude kadan. “Dan Allah yaya Hassan ka miko min zani da hijab” ya gyara kwanciyar sa yace “saboda me?” Tace “saboda Allah. Wallahi sanyi nake ji, zanyi mura da zazzaɓi” yace “to ki fito mana ki shirya, ni ina ruwa na dake” taji kamar zata yi kuka tace “ba zan iya shiryawa a gaban ka ba, dan Allah ka tafi dakin ka” yace “nan ma dakina ne, dan dakin matata ne” tace “ai Allah nace maka. Kaga ana kiran sallah zaka rasa jam’i” yace “shikenan sai muyi tare, in mukayi tare ma zamu samu ladan jam’i ni dake”

Ta dora goshinta akan kofar idonta a rufe tana jin sanyi yana ratsa ta tace “dan Allah dan Annabi daddyn Hussain ka fita, wallahi sanyi nake ji” ya mike zaune yana kallon toilet din yace “to ke me yasa ba zaki fito ba sai na fita, ni ba mijinki bane ba?” Tace “kunyarka nake ji Allah, ba zan iya fitowa babu kaya a gaban ka ba” yadda tayi maganar kamar zata yi kuka yasa ya ji tausayin ta, ya mike yai kamar zai shiga toilet din, yaga ta rufo kofar da sauri har da murda key sai yayi dariya yace “na fita to. A shirya lafiya, amma zan dawo”.

Sai data leko ta tabbatar ya fita sannan ta fito da sauri taje ta murda key din dakin. Ta jingina da jikin kofar tana ajjiyar zuciya, a ranta tana rokon courage daga gurin ubangiji. Ta shirya cikin plain doguwar riga budaddiya sosai mai adon stones a wuyanta kuma hannayenta. Mai kawai ta shafa sai turaruka a jikinta amma ko hoda bata shafa ba ta saka hijab tatayar da sallah, tana idarwa ta ji ya murda kofar amma ya jita a rufe sai ya wuce. Ta tashi ta nade sallayar sannan ta dan kara turare a jikin ta sannan ta bude kofar sau suka hadu dashi yana hawowa da basket din abinci a hannunsa, daga dukkan alamu daga gidan Aunty aiko musu.

Ta karba daga hannunsa da sauri, ya juya yana cewa ki kai mana dakina” sai ya juyo kuma yace mata “yau dinner in bed zamuyi” daga haka ya koma kasa da sauri. Tayi kamar zatayi kuka amma sai ta wuce ta tafi dakin nasa ta ajiye basket din tare da budewa tana ganin abincin da yake ciki amma sai taga gasashshiyar kaza ce da aka yayyankata aka kuma bade ta da yaji, tana budewa kamshinta ya cika dakin gaba kidaya. Ta bude dayan food flask din shi kuma ta tarar da farfesun kifi mai kyau, daga dukkan alamu yanzu aka sauke shi dan turiri yake yi sosai kamshinsa yana chakudewa tare da na kazar.

Taji an bude kofar dakin an shigo, sai tayi sauri ta rufe ta mike tsaye tana rarraba ido, ya bita da kallo sannan ya kalli basket din yace “kwadayi ko? Daga baki sako sai kizo kina budewa?” Taji kunya ta kamata sai ta wayance da cewa “ina yarana? Ka aika a dauko su please” ya zauna yana ajjiye drinks din hannunsa a kan table yace “kina da number din Aunty ai, ki kirata kice ta dawo miki da ƴaƴan ki” sai ta tura baki, wato magana ya gaya mata kenan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button