TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A take ya saka hannu a takardar siyan gidan sannan kuma ya tura kudin, duk da cewa yayi tunanin cewa gidan yayi tsada da yawa but for Hassana it is worth it. Yayi tunanin irin farin cikin da gidan zai saka ta, ya tuno irin farin cikin da ya gani a idobta ranar daya ke kunna mata wayar da Hussain ya siya mata.

Briefly ya sa akayi furnishing gidan, light furnitures irin wanda yasan ko shi zai iya amfani dasu sannan wadanda yasan su din zasu yi murna dasu sosai.

Daga nan kuwa sai ya sake ware wasu kudin masu kauri ya kaiwa Aunty “Aunty maganar lefe, nace kina ganin wannan kudin zai isa?” Ta duba kudin tace “zai isa mana, in dai ba irin na Hussain kake son kayi ba” ta karasa tana dariya, shima yayi dariya yace “Allah ya kiyaye, wadannan barsu kawai, Hussain shi kudi kamar mintsinin sa suke yi” sai kuma ya kara da cewa “kuma shi saboda irin gidan da ya debo wa kansa aure ya saka banyi masa maganar ya rage kayan ba, abu ne na manya da manya” ya fada sarcastically.

Aunty ta girgiza kanta tace “kasan halin Hussain ko ba gimbiya Fatima bace bama irin abinda zai yi kenan. Ballantana kamar yadda ka fada ai shi tuwon girma miyarsa nama ce” Hassan ya mike yana cewa “ai shikenan. Sai yaje yayi ta cin naman” Aunty ta sake daukan kudin ta juya tace “amma fa in bai isa ba zamu ce maka ka karo” yana dariya yace “manage it aunty, bafa gimbiya Fatima ba ce ba”.

An sanar da Baba maganar zuwa neman aure amma sai ya umarce su dasu hadu a Zaria gidan yayansa Malam Isyaku. Haka akayi kuwa suka hadu acan suka tambayar wa Hassan auren Hassana , a take aka ce an bashi, sai suka nemi a saka musu ranar da zata hadu da ta yan uwansa nan da wata uku da yan kwanaki. Malam Isyaku yace “anya kuwa? Wata uku ai yayi mana kadan ace mun shirya aurar da ya a cikin su. Kuyi dai wancan din wannan kuma sai a shirya a tsanake sannan ayi shi daga baya.

Baba Mustapha, ganin baban su Hassan yace “haba malam, wacce shiryawa zakuyi kuma? Mu ai ƴa kawai muka zo nema gurin ku bama bukatar komai daga gare ku. A yadda Hassan ya a bani labarin yarinyar nan ai nasan idan ma bashi zata aura ba shi zai yi mata kayan daki ballantana shi zata aura. Babu wani abu. Ita kawai zaku bamu. Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya da zuriya mai albarka”. Anan jayayya ta kare, date fixed.

Bayan dawowar Baba daga Zariya ne yan uwa suka yi ta tururuwar zuwa gar gida suna yi musu murna shi da Inna Ade. Fatsar su tayi babban kamu. Ruqayyah kuwa kullum bata iya rufe bakinta dan murna, lissafi take tayi na irin shagalin bikin da za’a sha, irin wanda aka jima ba ayi irinsa a Kaduna ba. “I can’t wait to see the reaction on my friends faces. Ruqayyah a ina kika hadu da mai H & H? Ko yanuwanku ne dama?” Ita kuma will be like “gani na kawai yayi a hanya ya like min. Yaga irin zubin matar manya” ta lissafa adadin parties din da za’a yi, dinner, luncheon, Arabian night, mother’s day, sisters eve. Irin kayan da zata ke sakawa zuwa kowanne event da kuma irin kawayen da zata je dasu “ba kowa za’a gayyata ba, kar suje su ba ni kunya a cikin dangin miji”.

Bayan Hussain ya dawo ne ya aiko wa da Ruqayyah tsaraba. Wani set din mayukan gyaran gashi ne, ya kira ta yace “gimbiya ta ce ta bani sako in siyo mata, shine kema na siyo miki ban sani ba ko zaki so shi. Kayan ku ne na mata, ni ban san kyansu ba” Ruqayyah ta bude dan akawatin kayan tana dubawa, ita duk bata san ma ya akeyin amfani dasu ba. Tayi tsaki ta mayar ta rufe. “Wannan Fatimah daga dukkan alamu ta fiya iyayi”.

Hussain yana dawowa ya tarar an gama saka rana, dan haka shi kuma sai ya mayar da hankalinsa kan ginin gidajensu. Shi Hussain a nasa tsarin so yayi yayi mudu ginin iri daya, komai daya, amma Hassan yana ganin plan din ya girgiza kai yace “wadanna dakunan duk me za’a yi dasu? Ni gaskiya bana son wannan plan din sai kace ba za’a bar duniya ba” Hussain yayi kamar zaiyi kuka yace “dan girman Allah kar ka bata mana tsarin nan, mun riga mun gama shirya komai na gama magana da engineers din nan sun gama fitar da plan dinsu…..” Hassan yace ” sai ayi maka naka plan din daban ayi min nawa daban. Ni I won’t be feeling comfortable a irin wadannan gidajen” haka Hussain a dolensa ya hakura saboda babu yadda zaiyi amma shi a son ransa yaso ace iri daya suka yi, komai iri daya.

A karshe sai da Hussain ya hada baki da engineers din sannan suka shawo kan Hassan ya bari aka dora masa bene, amma shi da cewa yayi shi baya son bene “ni bana jin zan iya rayuwa a sama kamar wani tsuntsu” sai engineer yace “amma oga Hassan tunda an riga an dora wa Hussain in ba’ayi a naka ba gidajen ba zasuyi kyau, zasu zama dogo da gajere kenan. Sannan kuma ginin oga Hussain zai toshe maka iska a naka gidan”. Da wannan aka samu Hassan ya yarda, amma shi ya tsara kayansa. “Two bedrooms a sama three bedrooms a ƙasa. Shikenan sun ishe mu. Ni plan dina na rayuwa da mace daya ne ni Hassana ta ishe ni har abada. Tunda muna kusa da gida nasan ba wasu baƙin kwana zamu ke samu ba sai dai daga nata bangaren, suma in sunzo dakunan kasa guda uku sun ishe su” Hussain yayi ajjiyar zuciya yace “wannan Hassana, ina tausaya muku kai da ita”.

Haka aka yi ginin part din Hassan aka gama, kullum yana gurin yan tabbatar wa cewa anyi masa yadda ya tsara abinsa. Ssi da aka gam ak koma kan na Hussain anan aka kure adakar gayu. Part dinsa daban na gimbiya daban na bakinta daban na bakinsa daban. Faluka iri-iri, ga gym ga swimming pool, irin kofofi da fitulun da aka saka a gidan ma kadai abin kallo ne. Amma Hassan ko a jikinsa bai ji cewa gidan Hussain ya burge shi ba. Shi tsarin nasa yafi yi masa kyau sosai dan har yana tunanin in ya fara gini irin wannan tsarin zaiyi sai dai maybe ya dan fi wannan girma saboda lokacin an fara tara iyali. He just can’t wait yayi rayuwa da hassanar sa a wannan gidan.

Ana tsakiyar shirye shiryen ne ya dauki Hussain ya kai shi gidan daya siyawa Baba ya gani, yayi masa bayanin aikin daya dauke shi da irin albashin daya bashi. Hussain ya gyada kai yace “ka kyauta sosai, yayi kyau sosai. Ni kuma a tawa gudun mawar zan siya masa napep yake zuwa dashi gurin aiki, ranar kuma da bashi ne da duty ba sai ya zagaya ya samu karin kudin cefane”

Hassan yayi masa godiya suka bar gidan. A hanya Hussain yake cewa Hassan “amma sai yaushe zaka bashi?” Hassan ya yi murmushi yana shafa kansa yace “sai satin bikin mu, sai su tare a sabon gida suyi bikinsu acan” Hussain yace “why? Hassan the planner. Da nine a ranar da na siya, maybe ma kafin inga gidan shi zan dauka muje mu gani tare. To me zan jira kuma? Yanxu in kai ka mutu kafin biki ko kuma shi ya mutu kaga ai siyan gidan bai yi serving amfaninsa ba”.

Wannan littafin na siyarwa ne, wadda take so tayi min magana ta wannan number din 08067081020

Seventeen: Ungrateful

Hassan ya dauke kai tana bata fuska “kai dai baka da zance sai na mutuwa, kullum sai ka ambaci mutuwa kake jin dadi, at the same time kuma kana gina rayuwa kamar ba zaka mutu din ba. Sometimes I find you confusing wallahi” Hussain yayi dariya “to mutuwa ai dole ce, kullum saka rai nake cewa ba zan kai gobe ba shi yasa bana taba barin abinda zan iya yi yau ince sai gobe, at the same time kuma ina living rayuwata the fullest tunda nasan in na mutun bani da second chance, ina kashewa kaina da mutanen da suke tare dani kuɗi saboda ina ganin basu da wani amfani banda a kashe su din, to inna ajiye me zasu yi min? In na mutu sai dai dangi suyi fada akan su to ba gwara in basu ba sanda nake raye? Ni fa kullum ina addu’ar ka da Allah ya bani kudin da ba zan iya kashewa ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button