TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacin da Hassan ya shiga gida baki har kunne yana nunawa Ruqayyah email din da Hussain yayi masa forwarding zuwa wayarsa, a daki ya same ta a kwance dan wannan cikin kasala yake saka ta ba kadan ba, ya jawo ta ya rungume ta “Hassana Hussain ya warke, ya warke ya warke, Hassana ki taya ni murna Hussaini na ya warke” farko bata ma gane me yake cewa ba, ta dan bata rai tana ture shi saboda bata son kamshin turarensa tace “me kake cewa? Me ya samu Hussain din?” Ya sake ta yana murmushi, idonsa yana kyalli “babu abinda ya same shi babu abinda zai same shi likitoci sunce ya warke” ta danyi shiru tana digesting maganar “wait, what? Ya warke fa kace, dama ana warkewa daga cancer ji nake yi bata da magani” ya danyi dariya “babu ciwon da bashi da magani Ruqayyah, ita cancer maganin ta shine ayi aiki a yanke bangaren da yake da ciwon sai kuma a kashe gurin yadda ciwon ba zai dawo ba balle ya yadu, in dai akayi nasara a wannan to shikenan mutum ya rabu da ita, akwai mutane da yawa da suka warke daga cutar cancer kuma Hussain yanzu is one of them. I am so happy, I was so scared cewa wani abun zai iya samunsa” tayi sauri ta mike ta shiga toilet pretending as if amai ne ya taso mata. Ta rufe kofa sannan ta jingina da jikinta. Daga inda take tana iya hango katangar gidan Hussain ta tagar toilet dinta. Ta runtse idonta tana tuno mugun labarin da jiya ya cika gidan na cewa Fatimah tana dauke da ciki, kuma a yadda Nafisa take gaya mata wai cikin har yayi wata biyu ma’ana banbancin wata biyu ne tsakanin nata da na Fatima. Wannan wacce irin bakar rana ce? Dukkanin mafarkanta sun tarwatse a cikin kwana daya. Fatima ta samu ciki sannan Hussain ya warke.

Ta tari ruwa a hannunta tana wanke fuskarta, a zuciyarta tana jin haushin kanta data daina shan pills dinta har ta kai ga samun ciki a hope dinta na rike gidan ta hanyar amfani da ƴaƴan ta, gashi yanzu gimbiya zata haifi nata, guda dayan da zai doke dukkan nata guda ukun tunda ubansa shine mai kudin gidan. Ta tuna da irin celebrating din da akayi tayi a gidan tun jiya bayan ita sanda ta samu nata cikin farin babu wanda ya ko da daga murya ne da sunan murna. Wannan ciki kuwa ko maganar sa ma ba’a yi, wani abin haushin shi kansa uban yayan sanda ya fahimci tana da cikin sai da yayi mata magana, a lokacin suna Saudiyya . “Ina pills din da doctor ya baki” tace “suna Nigeria, ban taho dasu ba” ya bata rai “ai dama ba nan nake nufi ba, ai ba anan aka samu cikin ba, a Nigeria din nake nufi ba kya sha dama” ta bata rai “ina sha mana, wasu kwayar magani sun isa su hana mutum haihuwar abinda Allah ya riga ya rubuta sai an haifa. In baka so ka gaya min kawai ba sai kana boye boye ba” ta fara hawaye, ya kamo hannunta, ya zanyi ince bana so Hassana? Ko ya’ya nawa zan haifa ai duk Allah ne ya bani kuma duk ina so kawai dai jariran can nake tausayawa wallahi, kin ga basu yi wani kwari ba yanzu suke kokarin fara rarrafe” tace “ai dama suna shan madara, sai su cigaba da shan madarar su kawai ni kuma su barni in ji da kaina” daga nan kusan babu wanda ya kuma yin maganar cikin nata a zaman nasu na Saudiyya, su duk sunfi mayar da hankalin su akan addu’ar samun sauki gun Hussain. Gashi yanzu addu’ar tasu ta karbu ita kuma sun barta a tasha.

Ta tuna da alkawarin da wannan malamin duban yayi mata “zaki yi kudi fiye da kudin da kike saka ran zaki yi” tayi tsaki “banza makaryaci” ta fada a fili. “Allah yaso ban bashi ko kwandala ta ba” ta dawo daki ta tarar Hassan ya fita ta koma tayi kwanciyar ta ta na jin duniya duk tayi mata kunci, me yasa ne duk plan din data shirya sai ya wargaje ne wai? Ita har yanzu fa ko quater din abinda take so bata samu ba. Wata zucuyar ta gaya mata ko dai tayi giving up ne ta koma school irin na Sumayya tayi karatu ko zata samu aiki ta dan kara wani abu? Tayi tsaki, kuma shikenan yadda ake ganin ta kuma sai aga ta koma makaranta? Wanda ma bai san cewa bata yi jami’a ba shikenan sai ya sani.

A haka har magrib tayi, dama yanzu tun dawowar su ta dawo da cook din su ta da ta cigaba dayi musu abinci saboda tana laulayin ciki, twins kuma shekaran jiya taje ta kaiwa su inna tsarabar su ta barsu a can zasu dan kwana biyu. Dan haka a daki take wuni sai dai ta fita taci abinci ta dawo, wani lokacin kuma abincin ma a daki ake kawo mata taci abinta takwanta. Balle yau da bata so taga fuskar kowa dan tana jin duk wanda ya kula ta zata iya rufe shi da masifa ko da kuwa babu laifin da yayi mata. Starting from Hassan dan da yasan haushin sa da take ji yau din nan da ko inda take ba zai dosa ba.

Tana zaune a kan sallaya ya shigo ya tsaya yana kallonta a ransa yana jin ba dadi akan irin yadda tayi reacting to labarin samun saukin Hussain. Baya son ya yadda da abinda kwakwalwar sa take gaya masa akanta. Yace “ki shirya in an jima zamu je gurin Aunty, ta shirya mana cin abinci na musamman dan murnar abinda ya samu Hussain” ta mike daga kan sallayar tana kallon sa “cin abinci na musamman? Saboda me? Saboda matar mai kudi ta samu ciki ko kuma saboda yar sarki ta samu ciki? Ni sanda na samu nawa cikin ko shan ruwa na musamman ba’a shirya min ba balle cin abinci, kai ni ko magana ta musamman ba’a gaya min ba” ya karaso tsakiyar dakin yana kallonta yace “da ni da Hussain duk daya muke a gurin Aunty, da ke da Fatima duk daya kuke a gurin Aunty, Aunty kuma uwa ce a gareni dan haka ina so ki san maganar da zaki fada a kanta. Ba kudin Hussain ko matsayin Fatima ne yasa zamu taya shi murna ba, ba kuma cikin jikin Fatima zamu yi celebrating ba, samun lafiyar Hussain zamuyi celebrating saboda ba wai abu ne common ace mutum yayi Cancer briefly ya warke ba, warkewar sa shine abinda zamuyi celebrating” ta cire hijab dinta tana ninkewa tana huci “eh dama ai kai kowa yana da muhimmanci a gurinka banda ni, ban isa in fadi magana akan kowa ba sai kace kar in kuma amma ni duk abinda za’a yi min mai baka gani, duk irin wariyar da ake nuna min kai baka gani” yaji bacin ransa yana karuwa, yace “dan Allah Ruqayyah kar ki bata min rai bayan ina cikin farin ciki, can’t you at least pretend to be happy ko dan in shiga cikin yan uwana cikin jin dadi? Menene problem dinki ne wai? Yanzu rashin son da kuke yiwa Hussain har ya kai baki damu da samun lafiyar sa ba” ta ajiye hijab din ta hau kan gado ta kwanta tace “tunda bata maka rai nake yi it will be better idan banje gurin ba, kar in cigaba da bata maka ran acan ma. And ina taya Hussain farin ciki da samun lafiyar sa, kawai dai am not in the mood for celebration ne” ta ja bargo ta rufe har fuskarta.

Haka ya juyo ya fito daga dakin ya shiga nasa ya shirya ya fito, ko kallon dakinta baiyi ba ya fita ransa duk babu dadi, shi duk ba haka yayi tsammanin auren sa zai kasance ba, shi ba haka yayi tunanin matar da ya zaba a cikin matan duniya zata ke treating dinsa ba, shi ya saka ran total submission daga gurin matarsa yadda zata faranta masa shima kuma ya faranta mata. Bai taba tsammanin yarinya karamar daya dauko daga cikin talauci ya kawo ta cikin daula zata raina abinda yake dashi take kuma mayar masa da magana aduk lokacin daya fadi wani abu ba, bai dauka young and innocent hassanar sa zata iya fadar bakar magana akan Hussain ba ballantana Aunty.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button