TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

. ***. **

Tunda su Hussain suka fita Fatima bata koma cikin gida ba, sai ma ta samu kujera ta kafa a bakin kofar ta zauna tana jiran dawowar sa, kowa ya yi mata magana amma taki shiga ciki, gani take yi bata da wani sauran abinyi a cikin gidan, gani take yi kamar rayuwar ta ta kare a cikin gidan. Bayan awa biyu da tafiyar su ta dauki wayarta ta kira Hussain, tana so taji ko sun sauka lafiya amma wayar shiru ba’a dauka ba, ta kuma kira still shiru, sai ta kira ta Hassan shima bai dauka ba. Ta mike tana dosar part din aunty, a lokacin ne Ruqayyah ta shigo a mita tare da Minal sun dawo daga soyayyar zasu dauki wasu kayan sannan ta kai Minal gida. Suka tsaya a gefen Fatima, Ruqayyah tace “Fatima ya dai nag kamar hankalin ki a tashe? Wani abu ya faru ne” Fatima tace “yauwa Ruqayyah ki gwada kira Hassan da Allah muji ko sun sauka lafiya” Ruqayyah tace “sun je wani guri ne? Ni tun safe bana gida” Fatima tace “sun tafi Abuja, shi da Hussain, na kira Hussain bai dauka ba, ina so ne kawai in san ko sun sauka lafiya. Ruqayyah da Minal suka kalli juna suna tabe baki. Sannan Ruqayyah ta dauko wayarta ta kira Hassan amma bai dauka ba tace “bai dauka ba” Fatima ta fra yarfe hannu, “na shiga uku, ni gaba na faduwa yake yi. Ji nake yi kamar babu lafiya, kamar wani abu ya sami mijina” Ruqayyah ta tabe baki tace “kin san dai halin su in suna tare, na tabbatar da cewa hira ce ta saka basu ga kiran ki ba” Fatima ta sake girgiza kanta, sannan ta hango wani driver lawan ta kira shi “lawan dan Allah dauko mota ka kaini Abuja yanzu” Ruqayyah ta saki baki “for real? Wai bin sa zakiyi dan bai dauki wayarki ba? Fatima tace “ba rashin daukan waya bane ba, it is something else” sai ta juya ta nufi inda lawan yake fito da motar.

Minal ta kalli Ruqayyah tace “wai ke ma ba da mijin ki akayi tafiyar nan ba? Ke ba kya jin wani iri a jikin ki?” Ruqayyah ta tabe baki tace “ni lafiya nake jin jikina” Minal tace “dalla tashi ki bita, kema ki nuna kin damu da naki mijin” Ruqayyah tace “Abuja? Na bar fa dan jariri na tun safe a gurin Aunty” Minal tace “ba zai mutu ba ai, ki tashi ki bita ki ce kema naki jikin babu dadi mijinki kike so ki gani” Ruqayyah ta karasa packing sannan ta fito, Minal ma ta fito sai kuma lokaci daya tayi tunanin to in taje gida ma me zata yi? Ai gwara kawai ta bisu ta ga yadda dramar zata kare, sai kawai ta tafi itama ta bude gaban mota ta shiga ba tare da tayi tunanin bata tambayi mijinta ba ko kuma tunanin abinda zai je ya zo, Fatima kuma tare da Ruqayyah suka shiga baya sannan lawan driver ya ja suka dauki hanyar Abuja.

Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani wajen na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020The Accident 2

Kafin mu dora.
Sanda zamu fara banyi wa kowa alkawarin smiles and laughter a lokacin karatun tagwaye ba, besides, ni ban taba yin rubutu da niyyar in saka readers nishadi ba, a koda yaushe dalilin rubutu na shine dan in yi sharing abinda ni na fahimta akan bangarorin rayuwa tare da sauran mutane, fahimta ta ce, bance lallai ita ce dai dai ba, kawai dai ina fatan wani zai iya ya dauki wani abu da zai amfane shi a ciki.
And yes,
Duk wadda take son refund na kudinta tayi existing paid group sannan tayi min magana ta private.
But the story will continue as it is…………..

Hassan ya sake kamo hannun Hussain ya kankame a kirjinsa yana jin hucin da zuciyarsa take yi yana huda kirjinsa yana dukan hannayensu, kuka yake so yayi amma ya kasa, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban kuka. Ya jawo hannun zuwa bakinsa yayi kissing, baya bukatar likitoci suzo suyi masa bayani ya riga ya sani cewa Hussain baya tare da shi ya tafi gurin mahaliccin mu baki daya, ya tafi inda Maman su ta tafi, babansu ma ya tafi, yanzu shima ya tafi, sai Hassan yaji a ransa bai san me yake zaune yake yi a duniyar ba, zai iya bayar da komai da yake dashi dan ya bi bayan dan uwansa. Ya kalli fuskarsa fes da ita kamar yana bacci, dai yaga yayi masa wani irin kyawun da bai taba ganin yayi irin sa ba. Fuskarsa da hancinsa sun kara yin tsaho tamkar ba nasa ba. Sai yaji a lokacin babu abinda yake so kamar shima ya zama tamkar Hussain, shima ya zama gawa ko ruhinsa zai tafi gurin mutane mafiya soyuwa a gurinsa.

Yaji wani irin kadaici ya rufe shi tamkar shi kadai ne dan Adam din daya rage a duniya. Sai rufe idonsa ya kwantar da kansa a kirjin Hussain yana lura da yadda baya jin motsin bugun zuciya a kirjin. Ina ma dai shima tasa zata daina bugawar? Ina ma dai zata daina yi masa zafi da radadin da take yi masa yanzu.

Sun jima a haka sannan yaji an bude kofar dakin an shigo, bai motsa ba dan baya son motsawar, so yake ya cigaba da kwanciya a haka har tasa zuciyar ta daina bugawa shima ya tafi inda Hussain ya tafi. Inda mahaifan su suka tafi.

Hannu yaji an dora akan kafadar sa, ya dan bude ido kadan yana kallon likitan a cikin Scrubs dinsa, Doctor din yace “I am very sorry Hassan. Allah yayi wa Hussain cikawa. Allah yaji kansa da rahama” sai Hassan ya mayar da idonsa ya rufe, yana so yace Ameen amma bakinsa ya kasa motsawa, zuciyarsa ma ta kasa amsawa. He just can’t accept cewa gaisuwar Hussain ake yi masa. Sai doctor din ya cire wa Hussain duk machines din da suka jojjona masa, ya kuma cire masa abin oxygen din da suka saka masa dan baya bukatar oxygen a yanzu, sannan sai ya jiya ya fita dan ya lura Hassan yana bukatar karin lokaci tare da Hussain. Bayan fitarsa ce wata nurse ta shigo ta dauki takardu ta fita, sannan wani ya shigo shima ya dauki wani abu da Hassan bai san menene ba, ya kuma rufe idonsa yaji shigowar wani, shi bai dauki komai ba ma ya fita. Sai Hassan ya fahimci wani abu, ya dago kansa yana kallon bakin kofa yana tunanin abinda ya faru a lokacin da akayi wa Hussain aiki a India ballantana yanzu da suke Nigeria, yadda Hussain yake public icon kowa zai so ace shi ya fara sanar da labarin mutuwarsa. Ya mike yaje ya rufe kofar dakin ya dawo ya ja abin rufa ya lullube Hussain har fuskarsa. Har yanzu kwakwalwar sa bata aiki sosai dan haka ya kasa tunanin mai zai yi. Ya jingina bayan sa da jikin kofar ya rufe idonsa yana sauraron bugun da zuciyarsa take yi, sai kuma yayi sauri ya bude idonsa ya fara laluben aljihunsa yana neman wayarsa, sai yaji bata jikinsa, ya barta a mota.

Hankalin sa a tashe ya bude kofar ya fita tare da yin amfani da key din daya gani a jikin kofar ya rufe ta ta waje, babban abinda ba zai so ba shine yaga hotunan gawar Hussain tana yawo a social media. Yes, people are that cruel, wasu tamkar jira suke yi abu ya same ka su fara yadawa babu ruwansu d halin da kake ciki ko abinda yadawar tasu zai iya janyowa. Ya tabbatar da yawa daga staff din asibitin by now sun san cewa Hussain Aminu Abdullahi ya mutu a cikin asibitin su, wani ya gaya wa wani wanin shima ya gaya wa wani, ya tabbatar kafin nan kafin minti biyu wani zaiyi posting a social media sannan wasu suyi sharing suma kuma ayi sharing nasu post din. Yasan kannensa gabaki daya suna social media haka ma Fatima, tashin hankalin sa kadai shine Fatima taji wannan labarin a media kamar yadda taji na rashin lafiyar Hussain. Musamman duba da halin da take ciki. Shi kuma a yanzu ba ya jin akwai wani abu da yake so fiye da abinda yake cikin Fatima, hatta yayan da ya haifa a cikinsa kuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button