TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Da wannan Hussain ya bar Salisu. Bayan cike ciken takardu da yayi da kuma sauran abubuwa sai ga kudinsa an dawo masa dasu cif ko kwandala bata yi ciwo ba. A ciki ya fitar ya bawa police kaso mai tsokar da yasa duk sai da suka ji sun kasa rufe bakunansu saboda murna, sannan kuma yayi alƙawarin biyan hospital bill din police guda daya daya samu rauni.

A hanyarsa ta komawa asibiti ya kira gimbiya ya gaya mata duk halin da ake ciki, tun daga muryarta ya fahimci cewa tana cikin farin ciki sosai. Shima sai yaji duk damuwar da take ransa tana wucewa tana tafiya tare da sautin dariyarta. Yayi dariyar shima. Tace “kasan wani abu? This is the first time da naji kayi dariya tun ranar da aka dauki Hassan. Lallai ba karamin so kake yiwa Hassan ba, Allah ya bani, ko ince ya bamu ni da matar da Hassan zai aura ikon cigaba da karfafa kaunar da take tsakanin ku” sai yace “kinsan kuwa daga farkawar sa har ya fara xancen aure? Wai ya hadu da wata yarinya ta taimaka masa kuma wai ita zai aura” Fatima tayi dariya tace “anya kuwa Hassan din mu ne ba’ayi mana chanji a can ba? This is something that you would do, not him” yayi dariya yace “nima abinda nace masa kenan. Mr Careful is now not being careful” tace “amma nasan ai ba wai direct kawai za’ayi auren ba. Nasan zasu samu time together su dan fahimci junan su kadan. Hey! Why not a haɗa da namu kawai ayi tare?” Ya danyi tsaki yace “ke ma kin fara biye masa kenan ko? Ni kuma na rasa dalili nine yau nake zama Careful din akan maganar” tace “what happened to the Hussain I know, the Hussain that just go with the beating of the drum, relax and chill”

A asibiti ya tarar Hassan ya kuma tashi, har Aunty ta na bashi abinci a baki yana ci. Ya leka bowl din hannunta yaga fruit salad ne yace “kai da zaka ci abincin da zai saka ka ciko ka mayar da jikinka ina kai ina fruits?” Aunty tace “a yanzu ai lafiya yake nema ba wai kiba ba, yana bukatar alot of vitamin c” Hussain ya shafa kafadar Hassan da fatar duk ta fara yamushe wa yace “and alot of meat. Me suke baka ne a wajen?” Hassan ya doke hannunsa yana hararar sa yace “what I need is a deep bath, in na gaya maka rabona da wanka sai kayi dariya dan haka ba zan gaya maka ba” Hussain ya toshe hanci yace “shi yasa atmosphere din dakin take chocking mutane”.

Hussain da kansa ya hada wa Hassan ruwan wanka sannan kuma ya taimaka masa yayi wankan yadda ruwa ba zai taba sannan suka fito ya kuma taimaka masa gurin shiryawa a tsanake ya saka kayan da Safiyya taje gida ta dauko masa. Sannan suka kuma saka shi ya sake cin abinci duk da cewa da kyar yake hadiya saboda yuwansa yana yi masa ciwo sosai.

Hassan yace “ina fita daga nan zan fara shirya mana tafiya waje, gwara muje can a duba ka sosai” Hassan yace “ni da zaka bi ta tawa da ka bar maganar tafiyar nan. Babu abinda doctors din mu nan nan ba zasu iya bafa, wadansu daga cikin su fa su suke aiki a can din” Hussain yayi murmushi cikin rada yace “ai ba dan asibiti nake so mu fita ba, dan ka samu ka huta ne sosai. Anan yan dubiya da yan jaje ba zasu barka ka huta ba” Aunty ta dago kai daga zubawa Khadijah abinci tace “me kake cewa?” Ya shafa kansa Yace “babu komai Aunty, cewa nayi abincin yayi dadi sosai”.

Daga baya ne Hassan ya basu labarin duk yadda lamarin ya kasance, briefly ya gaya musu irin zaman da yayi a hannun kidnappers din da kuma yadda suka yi jiya. Hankalin Aunty ya tashi jin Salisu ne a ciki, yammatan suka fara masifar sai sunci ubansa, Hussain yace “wanne uban nasa zaku ci bayan ubansa yana lahira? Shi kuma yana police station daga can za’a kai sji court sannan a wuce dashi prison, me zakuyi masa wanda Allah bai riga yayi masa ba? Daga nan Hassan ya basu labarin haduwarsu da Ruqayyah da yadda ta saka rayuwarta a cikin hatsari dan ta taimaka masa. Duk jikinsu yayi sanyi sosai, suka kuma jinjinawa kokarin ta. Aunty tace “tabbas alamu sun nuna cewa yarinyar ta kirki ce, tunda bata san ko kai waye ba, zata iya kasancewa kai mugu ne da zaka iya cutar da ita ko ahalin gidansu. Wannan shine taimako na gaskiya, ka taimaka wa wanda baka da tabbas din shi zai taimaka maka” Hassan ya gyada kai yace “tabbas, tunda ba sani na tayi ba ballantana muce tayi ne dan ta samu wani abu a gurin mu” duk sauran suka amince amma banda Hussain, har yanzu maganar bata kwanta masa na, yace “tunda naji kace talakawa ne sosai ina ganin abinda za’a yi in mun dawo sai a kira babanta a samu wani abu mai kyau a bashi, yadda zai samu jari, ko kuma ita a bata scholarship tayi karatu” Hassan ya girgiza kansa yace “ba haka za’a yi ba, aurenta zanyi, sometimes money is not always the solution, kudi in muka basu zasu iya karewa amma aure, hada jini, babu yadda za’a dawo dashi baya”

Hussain yace “exactly my point, babu yadda za’a yi undoing aure, ko an rabu tambarin yana nan, shi yasa ya kamata ayi dogon tunani da dogon nazari kafin ayi shi. What if suna da wani aibu, wani ciwo ko wani tambari marar goguwa? What if da akwai wani hidding halinta ko na iyayenta wanda ba’a sani ba? What if a cikin rescue mission din nata akwai wata hidding agenda da bamu sani ba?”

Hassan yace “shi yasa nace zan aureta, ni Hassan, bance Hussain ya aure ta na. Ko ma menene a tare da ita it will be my burden not yours”

Suka tsaya suna kallon kallo

Aunty tayi tagumi tace “zaku tsaya in yi magana ne ko kuma ba kwa bukatar jin ta bakina? Yanzu ku shirya ku tafi inda zaku je ku huta din kar a dame ku. Kafin ku dawo zan nemi gidan inje da kaina inyi musu godiya daga nan zan ga yarinyar zan kuma ga iyayenta, sannan zan san abinda za’a yi musu” ta juya tana kallon Hussain tace “su kuma wadanda baka son su zo su dami dan uwanka yanzu zanyi musu yawa su zo su ganshi, tunda ya bata suke garin nan kuma babu yadda za’a yi ace an ganshi kuma har ya bar kasar ba tare da sun ganshi ba. Daga nan ta dauki waya ta fara sanar wa da jama’a, kafin laasar Asibitin ya cika da yan dubiya da jaje.

Washegari gimbiya tazo da safe, bayan ta duba Hassan ta kuma zuba masa lafiyayyen girkin data shiryo masa tun daga kano wanda duk masu ruwa ruwa ne yadda zai ji dadin hadiya, duk kamewar Hassan sai daya yaba mata da girkinta sannan yayi mata godiya. Daga nan sai suka fita ita da Hussain tana tayashi shirye-shiryen tafiyar su shida Hassan. Sai da suka gama komai sannan ya kaita airport shi kuma ya koma gida.

Two Day’s Later

Ranar Monday, kwana daya da tafiyar Hassan da Hussain India inda Hassan zai ga likita kuma zai samu ya huta sosai. A ranar ne su kuma su Ruqayyah bayan sun taso daga makaranta as usual Ruqayyah ta fito daga taxin tana mita. “Allah kaɗai ne yasan irin gajiyar da nayi wallahi. Yunwar da nake ji kuwa ina jin zan iya cinye abincin da akayi a gidan mu gabaki daya” Sumayya ta fara kokarin fitowa tana kuma zaro Naira dari a aljihun rigarta. Ta juya tana mikawa drivern sai taji yace “ki bata, ta sayi awara ta kara akan abincin dan ya ishe ta” tayi dariya yayin da Ruqayyah ta juyo da niyyar juye wa mai maganar kwandon bala’i, suka yi ido huɗu da drivern ranar nan. Ta bude ido tare da cewa “kutumelesi! Dama motar ka muka shigo?” Ya daga kafada kawai yana murmushi, ta juya gurin Sumayya da take dariya tace “da haɗin bakin ki muka shigo motar sa ko? Ya akayi ban gani ba?” Sumayya tace “nima sai da muka shiga sannan naga shine, nayi kokarin nuna miki ke kuma kina can kina yiwa yarinyar data taka miki kafa bala’i dan haka na rabu dake kawai” Ruqayyah ta kalle shi taga har yanzu murmushi yake yi sai taji tamkar ta kama kyakkyawar fuskarsa ta goga ta akan kwalta. Ta juya ta bar gurin tana maganganu kanana kanana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button