TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Inna tace “Sumayya sai ta dawo dakina ke kuma ki zauna a nata, in yaso in yaran sun tashi kukan dare ke sai kiyi ta rarrashin su ke kadai. Ke da ba a miki abin arziki har zaki nuna ke ba kya son zuwa gida wanka. To kuma da a wancan daya gidan muke kuma fa? Da ya zaki yi? Dolen ki dai can din shine tushen ki shine tutiyarki, nan gidan mijin ki ne ba gidan ki bane ba* Ruqayyah tayi shiru a ranta tana jero istigfari dan bama zata iya imagining komawa wancan gidan ba. A ina zata kwanta?

Ita kuwa inna a ranta taji zafin abinda Ruqayyah tayi, godiyar ta ga Allah da babu kowa a gurin sai su kadai dan da ta basu kunya a cikin dangin mijin ta. Wannan kuma shi yasa Baba ya dage sai ta taho da ita “in dai har mijinta ya bari ki taho da ita gida tayi wankan ta anan, ayi taron suna anan, dan a tuna mata cewa nan ne gidan su ba can ba”.

Sosai Ruqayyah take samun kulawa, ko juyi tayi Sumayya ko Inna zasu tambayeta abind take so. Ita kuma sai iko take zubawa da iyayi son ranta. Duk baya kwana biyu kuwa sai Aunty tazo ta ganta sannan kullum sai tayi abinci ta turo wata a cikin yayanta takawo mata. Hassan sau biyu yake zuwa, safe da yamma, kuma bashi da shamaki da har dakin yake shiga gurin matarsa da yayansa. Kullum kuma yazo sai tayi masa mita, “jiya sauro ya ciji Hassan” “yau Hussain ya kasa bacci da safe sabida hayaniyar mutane” ita dai kawai so take yace tazo su koma gida shi kuma ya toshe kunnuwan sa yayi mata kamar bai san me take yi ba saboda duk da cewa shima yana son su zauna tare amma ba zai iya taka maganar Baba ba..

Ranar suna ta zagayo aka sakawa yaran sunan mahaifin su Hassan “Aminullah” da kuma sunan Baba “Yusuf” ko wanne kuma aka bar masa sunan sa ba’a boye musu ba.

Ruqayyah an sha hidima, a shiga wadannan kayan a fita wadannan, kawayenta suna kara zuga ta na kara kumbura kai duk dama dai ba haka taso ba, taso ayi a gidan ta ne ko gidan aunty tunda sunfi girma da kaya masu tsada. A ranar sunan ne kuma Hussain da Fatima suka zo, ba a ranar ya shirya zasu dawo ba sai dai yadda Fatima ta matsa tana son ganin babies din ya saka a dole yayi squeezing ya gama abinda yake da wuri suka taho, duk kuwa da cewa taga babies din a waya. Suna sauka direct gidan sunan suka taho, suna zuwa gaba ki daya idanuwa suka koma kansu, yan tsegumi suka fara, Hussain har cikin palo ya shiga duk da mutanen da suke ciki ya dauki babies din aka yi musu hotuna sannan yayi wa mutanen gurin ruwan kudi ya tafi, tafima kuma ya barta a gidan.

A take maganganu suka fara wayo “wannan waye haka?”
“Ai shine mai kamfanin nan na H and H”
“au ba mijin Ruqayyah bane ba dama mai H and H din ba?”
“Aa, wannan ne, mijin Ruqayyah dan uwansa ne”
“kun ga matarsa kuwa?”
“Ai Yar yar sarkin kano ce”
maganganu dai iri iri, a take marokan da Ruqayyah ta saka aka dauko mata hayar su dan suzo su koda ta a gaya wa mutane wanne irin suna akeyi sai suka juya kan Fatima suna yi mata kirari, ita kuma ta bude bakin jaka tayi ta musu barin kudi. Wannan ya saka Ruqayyah ta zare jikinta ta koma daki ta cire gwagwgwaron ta yi kwanciyar ta, sai ga Fatima ta shigo dakin ta tsaya tana kallonta tace “lafiya Ruqayyah kika kwanta ana tsakiyar taron sunan ki?” Ruqayyah ta juyo tana kallon ta tana yamutsa fuska tace “wallahi stitches din nan ne suke min ciwo, sun takura min. Kin san azabar zafi ne dasu. Ko da yake ashe fa ke baki sani ba ko?” Ta juya ta cigaba da kwanciyar ta.

Bayan Fatima ta koma gida tun da ta shiga babu labarin da take yi irin na taron sunan Ruqayyah. “Ruqayyah tayi kyau, twins din nan sunyi kyau sosai, sooo cute. Kamar in sako su a jaka ta in taho dasu in kawo mana su gida” Hussain yayi dariya “kar ki damu, in duka dawo gida zamu ke dauko su suna yi mana wuni anan” ya sunkuyar da kansa yace “kafin mu samu namu muma” sai tayi shiru tana breaking knuckles dinta, ya tsaya yana kallonta dan yasan wata magana take son fada, sai tace “Mi Amour, nace ko zamu fara zuwa asibiti ne?” Ya girgiza kansa da sauri yana rike hannunta yace “ko wata goma fa ba’a yi ba da bikin mu, let’s not be inpatient please, mu jira ikon ubangiji kinji Princess. Our time will surely come kinji?” Ta gyada kai a hankali, ya jawo ta jikinta yace “nima ina so Fatima, ina son naga jinina a duniya ko ba biyu ba ko daya, ko mace ko namiji, ina so nima. But nasan cewa what ever will be will be”.

Ta kwantar da kanta a kirjinsa tana sauraron bugun zuciyarsa, sun jima a haka sai wayar sa ta fara ruri ya dauko ta ya daga kiran ya saka a kunne. “Manya manya maganin kanana kanana. Ya akayi? Ya garin? Nayi fushi ai in dai har ka kuma barin kasar nan ba ka zo kaga gidana ba to nasan matsayi na” ya danyi shiru sannan yace “ai na gaya maka tun ranar nan da muka yi Magana, in har baka gwada ba babu ta yadda zaka yi ka tabbatar cewa zasu baka auren yarinyar nan ko kuma ba zasu baka ba? Fargaba fa asarar namiji ce” yayi dariya “ka sami takawan kawai ka gaya masa halin da ake ciki, shi zai tura a nemar maka auren ta” “oh haka yace? To shawara ta rage naka kuma, amma ni dai personally bana giving up without trying, ka shirya kaje Riyad din da kanka ka nemi auren yarinyar nan in an baka you come and thank me in ba’a baka ba kuma to kar kace ni na baka shawara” yayi dariya, “gata nan a kirjina. Kai dai tsaya wasa sai da kaga munayi” ya cire wayar daga kunnensa yana dariya, ya juya yana kallon Fatima “mutumin ki dai ya kusa zuwa karshen katanga. Babansa ya ki zuwa nema masa auren balarabiyar nan” ta gyara kwanciyar ta a kirjinsa tace “shine kai kuma kake zuga shi ya tafi shi kadai ko? Ba zasu bashi ita ba ko me zaiyi. Am sure” yayi ajjiyar zuciya yace “I know. But there is no harm in trying, right?”

A daddafe Ruqayyah tayi sati uku a gidan su, sai kawai ta shirya plan ta gaya wa Inna Ade cewa Hassan yace ta shirya zai zo ya dauke ta su koma gida, sai kuma ta gaya wa Hassan tace Baba yace yazo ya dauke ta su tafi. Shi bai san me ta shirya ba yayi ta murna ya gaya wa Aunty, ita kuma ta saka aka gyarawa Ruqayyah part dinta duk dan ta faranta mata. Ita kuma Ruqayyah ta dawo da niyyar in Fatima ta taba mata ya’ya ta gurza mata amma sai ta tarar Fatiman ma bata kasar gaba ki daya. Wannan ya kona mata rai, ita gani take yi wannan tafiye tafiyen kamar dan a kona mata rai ake yin su. Farkon dawowarta tare da Sumayya suka dawo, Sumayyan ce kuma tayi mata register da online catering classes da yawa inda take koyon girke girke da sauran kitchen tips kuma suna gwadawa tare a kitchen dinta, sannan suka koyi yadda ake amfani da kitchen appliances din da suke kitchen din nata. Anan ne Sumayya ta gwada tambayar ta ko tana da niyyar komawa karatu? Tayi dariya Tace “karatu kuma? Ni dama tun farko ai kin san ina karatu ne saboda in yi kudi, yanzu already ina da kudin da ko aikin nake yi ba lallai in samu albashin da zai bani wannan rayuwar ba so why should I bother myself?” Sumayya tace “shi karatu fa ai ba dan ayi aiki ko dan ayi kudi ake yinsa ba ko? Nima da nake karatun ba lallai ne inyi aiki ba musamman in na samu mijin da baya son matarsa tayi aiki ai kinga dole in hakura ko ? Tunda dai ai auren yafi aikin” Ruqayyah tace “say what you may, ni dai ba wata school da zan koma”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button