TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan tsahon lokacin da Hassan ba zai iya tunawa ba sai doctors din suka fito sannan suka bashi damar ya shiga ciki gurin dan uwansa. Yana shiga Hussain ya dago hannunsa yana masa alamar yazo, ya tako a hankali ya zo ya jawo kujera ya zauna tare da kamo hannun Hussain ya rike a cikin nasa. Hassan yace “Hussain ” Hussain yace “don’t talk. Just hold me. Let me talk” Hassan yace “a’a kayi shiru ka rufe idonka ka huta kaji? Ka samu kayi bacci in ka tashi zaka ji ka warke” Hussain yayi murmushi, sai Hassan ya jinjina masa cewa duk da halin da yake ciki amma still yana iya yin murmushi. Ya bude baki a hankali yace “take care of our kids bro. All of them” Hassan ya maimaita “all of them” Hussain ya sake cewa “take care of everyone at home” sai kawai Hassan yaji yana so ya karanta masa kalmar shahada, sai ya karanta masa sau uku sannan ya maimaita sau daya. And then he is gone. A hankali Hassan yaji hannunsa yana zamewa daga cikin nasa, sai ya kara rike hannun hopping yaji ya rike amma bai rike ba sai kara saki da yayi, sai Hassan yaji tamkar wani bangare na ruhinsa ya fita ya barshi, tamkar ya zama rabi ne shi ba cikakken mutum ba. Tamkar ruhin Hussain ya fita ne tare da wani sashe na daga nasa ruhin.

. ***. **

Tunda su Hussain suka fita Fatima bata koma cikin gida ba, sai ma ta samu kujera ta kafa a bakin kofar ta zauna tana jiran dawowar sa, kowa ya yi mata magana amma taki shiga ciki, gani take yi bata da wani sauran abinyi a cikin gidan, gani take yi kamar rayuwar ta ta kare a cikin gidan. Bayan awa biyu da tafiyar su ta dauki wayarta ta kira Hussain, tana so taji ko sun sauka lafiya amma wayar shiru ba’a dauka ba, ta kuma kira still shiru, sai ta kira ta Hassan shima bai dauka ba. Ta mike tana dosar part din aunty, a lokacin ne Ruqayyah ta shigo a mita tare da Minal sun dawo daga soyayyar zasu dauki wasu kayan sannan ta kai Minal gida. Suka tsaya a gefen Fatima, Ruqayyah tace “Fatima ya dai nag kamar hankalin ki a tashe? Wani abu ya faru ne” Fatima tace “yauwa Ruqayyah ki gwada kira Hassan da Allah muji ko sun sauka lafiya” Ruqayyah tace “sun je wani guri ne? Ni tun safe bana gida” Fatima tace “sun tafi Abuja, shi da Hussain, na kira Hussain bai dauka ba, ina so ne kawai in san ko sun sauka lafiya. Ruqayyah da Minal suka kalli juna suna tabe baki. Sannan Ruqayyah ta dauko wayarta ta kira Hassan amma bai dauka ba tace “bai dauka ba” Fatima ta fra yarfe hannu, “na shiga uku, ni gaba na faduwa yake yi. Ji nake yi kamar babu lafiya, kamar wani abu ya sami mijina” Ruqayyah ta tabe baki tace “kin san dai halin su in suna tare, na tabbatar da cewa hira ce ta saka basu ga kiran ki ba” Fatima ta sake girgiza kanta, sannan ta hango wani driver lawan ta kira shi “lawan dan Allah dauko mota ka kaini Abuja yanzu” Ruqayyah ta saki baki “for real? Wai bin sa zakiyi dan bai dauki wayarki ba? Fatima tace “ba rashin daukan waya bane ba, it is something else” sai ta juya ta nufi inda lawan yake fito da motar.

Minal ta kalli Ruqayyah tace “wai ke ma ba da mijin ki akayi tafiyar nan ba? Ke ba kya jin wani iri a jikin ki?” Ruqayyah ta tabe baki tace “ni lafiya nake jin jikina” Minal tace “dalla tashi ki bita, kema ki nuna kin damu da naki mijin” Ruqayyah tace “Abuja? Na bar fa dan jariri na tun safe a gurin Aunty” Minal tace “ba zai mutu ba ai, ki tashi ki bita ki ce kema naki jikin babu dadi mijinki kike so ki gani” Ruqayyah ta karasa packing sannan ta fito, Minal ma ta fito sai kuma lokaci daya tayi tunanin to in taje gida ma me zata yi? Ai gwara kawai ta bisu ta ga yadda dramar zata kare, sai kawai ta tafi itama ta bude gaban mota ta shiga ba tare da tayi tunanin bata tambayi mijinta ba ko kuma tunanin abinda zai je ya zo, Fatima kuma tare da Ruqayyah suka shiga baya sannan lawan driver ya ja suka dauki hanyar Abuja.

Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani wajen na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020.The Accident

Ko bi ta kan wayar ta sa da ya yar bai yi ba, bai kuma kula da mutanen da suke tambayar da ko lafiya suka gandhi a rikice ba, kokarin sa kawai shine ya ganshi a gida ya ganshi a gaban Hussain kuma ya yi convincing dinsa su tafi asibiti. Ko parking bai kammala ba ya fito ya rufe kofa ya doshi part din Hussain dan yaga Adam ma’ana Hussain yana gida kenan.

Yana shig ya samu daya daga cikin yaran Fatima “ina Fatima take? Me gidan yana ciki?” Ganin Yadda hankalinsa yake a tashe ya sa ta rude “gimbiya bata nan, sun fita dazu ita da Aunty Khadija, amma yallaban yana ciki banga saukowarsa ba…..” bai jira ta karasa bayanin ta ba ya wuce ta ya haura sama da sauri ya nufi wing din Hussain. A palo ya same shi a kwance akan doguwar kujera da diary dinsa a gabansa, idonsa a rufe, hannun daya akan cikinsa dayan kuma akan diary din. Motsin shigowar Hassan ne ya saka shi bude idonsa da sauri. Sai kuma yayi kokarin mikewa zaune yana dan cije lips dinsa amma kuma fuskarsa da murmushi “hey, gidan mijin aure ne fa kake shigo min kai tsaye, ko baka san ni mijin aure bane ba?” Hassan ya share shi ya nufi diary din kamar zai dauka sai Hussain ya riga shi, a tura shi bayan sa yace “sirri ne na gaya maka” Hassan yana kallon sa yana lura da yadda yake iyakacin kokarin sa na ganin yayi keeping straight face sannan yace “why? Me yasa zaka yi mana karya Hussain? Ko zaka yi wa kowa karya ni mai yasa zaka yi min Hussain? Why do you choose to suffer alone bayan ba kai kadai aka haife ka ba tare dani aka haife ka? Me yasa zaka ware ni when you need me the most?” Hussain ya dauke kansa gefe, ya fahimci cewa ya sani, sai ya girgiza kansa yace “what does it matter in na gaya maka din, babu abinda zaka iya yi min, babu abinda kowa zai iya yi min, wanda zai yi min komai na gaya masa na kuma roke shi ya bani lafiya, na saka kun taya ni rokonsa ya bani lafiya, tunda ka ga bai bani ba to lafiyar bat da alkhairi a gurina, shi kadai yasan me yake nufi da ni”.

Zuciyar Hassan ta karye ya durkusa a gaban Hussain tare da dafa gwuiwar sa yace “Hussain dan Allah kazo mu koma asibiti, dan girman…..” Hussain yayi sauri ya rufe masa baki “mun gama maganar nan Hassan, na roke ka kuma ka amince, kayi min min alkawarin ba zaka sake mayar dani asibiti ba. Hassan likitoci ba zasu hana mala’ikan daukan rai ya dauke ni ba, kudina dukka ko zan karar dasu ba zasu kara min adadin kwanakin da aka kayyade min ba. Dan Allah Hassan kar ka tilasta min komawa asibitin nan, bana so in mutu a zagaye da likitoci da injina,bana son in karasa sauran kwanaki na a asibiti looking at faces din mutanen da basu da muhimmanci a rayuwata. Na fi son in zauna a gida tare da ku, tare da Fatima, nafi son inyi making use of my last days doing abinda zai amfani lahira ta ba wai neman lafiyar da babu wanda zai bani ita ba. Wancan aikin da akayi min na gaya maka na amince ne dan in faranta maka ba wai dan raina yana so ba” Hassan ya sake girgiza kansa “ba dan ni ba, yanzu kayi dan Fatima, dan abinda yake cikin Fatima” Hussain ya dauko diary dinsa yana budewa yana murmushi yace “Allah baya taba barin wani dan wani yaji dadi, ko babu ni nasan abinda yake cikin Fatima yana da uba, nasan ba zai yi kuka maraici ba, zai samu gatan uba a gurinka kuma a bangaren mahaifiyarsa ma ba zaiyi rashin komai ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button