TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Zuciyar Hassan ta karye ya durkusa a gaban Hussain tare da dafa gwuiwar sa yace “Hussain dan Allah kazo mu koma asibiti, dan girman…..” Hussain yayi sauri ya rufe masa baki “mun gama maganar nan Hassan, na roke ka kuma ka amince, kayi min min alkawarin ba zaka sake mayar dani asibiti ba. Hassan likitoci ba zasu hana mala’ikan daukan rai ya dauke ni ba, kudina dukka ko zan karar dasu ba zasu kara min adadin kwanakin da aka kayyade min ba. Dan Allah Hassan kar ka tilasta min komawa asibitin nan, bana so in mutu a zagaye da likitoci da injina,bana son in karasa sauran kwanaki na a asibiti looking at faces din mutanen da basu da muhimmanci a rayuwata. Na fi son in zauna a gida tare da ku, tare da Fatima, nafi son inyi making use of my last days doing abinda zai amfani lahira ta ba wai neman lafiyar da babu wanda zai bani ita ba. Wancan aikin da akayi min na gaya maka na amince ne dan in faranta maka ba wai dan raina yana so ba” Hassan ya sake girgiza kansa “ba dan ni ba, yanzu kayi dan Fatima, dan abinda yake cikin Fatima” Hussain ya dauko diary dinsa yana budewa yana murmushi yace “Allah baya taba barin wani dan wani yaji dadi, ko babu ni nasan abinda yake cikin Fatima yana da uba, nasan ba zai yi kuka maraici ba, zai samu gatan uba a gurinka kuma a bangaren mahaifiyarsa ma ba zaiyi rashin komai ba”.

Hassan ya zauna sosai yana kallon Hussain guiwoyin sa sunyi sanyi da suka kasa cigaba da daukan sa, ya runtse idonsa yana fatan hawaye yazo masa ko zaiji sanyi a zuciyarsa. A ransa yana addu’a “Allah in zaka dauki wani a cikin mu Allah ka dauke ni ka bar Hussain, Allah ka dawo da ciwon Hussain kaina shi ka bashi lafiya ya Allah. Allah kar kasa Hussain ya tafi ya barni Allah” ya bude idonsa sai suka hada ido da Hussain yana yi masa murmushi yace “don’t cry bro, kar kabada maza mana, everything is going to be okay”.

Babu yadda Hassan bai yi ba amma Hussain ya tubure yace shi babu asibitin da zai koma, babu aikin da za’a sake yi masa, kuma ya roke shi Allah da Annabi kar yabari kowa yaji cewa ciwonsa ya dawo. “Bana so inga hawayen su, ga halin da Fatima take ciki bana so in tayar mata da hankali” sai dai Hassan bai hakura ba sai da ya kuma kiran wancan doctor din yayi masa bayanin irin taurin kan Hussain da dagewar da yayi akan ba zai koma ba, sai doctor din yayi referring dinsu to wani oncologist din a nan Nigeria ya kuma bawa Hassan shawarar ya lallaba Hussain ya kaishi can “ko ba za’a yi masa aiki ba sai a bashi drugs din da zasu rage masa radadin ciwo, cos he is in pain right now, ina mamakin ma yadda har kace yan iya harkokin sa har yana boye ciwonsa, he really is strong”. Hassan ya gyada kai yace “the strongest man I have ever known”.

Likitan da aka hada shi da shi a Abuja yake da private hospital dinsa kuma ya kware sosai a aikinsa. Hassan ne ya shirya yaje asibitin, ya tarar already an aiko da record din Hussain da komai daga can asibitin dan hak kawai takardu ya ciccike sannan ya koma Kaduna ya fara yakin lallaba Hussain akan ya taho yaga wannan likitan. Da kyar ya yarda suka zo, da alkawarin cewa ba kwantar dashi za’a yi ba. Da daddare suka zo secretly saboda gudun sa idon yan media, Doctor din ya duba shi sosai, yayi masa hotuna sannan yayi masa prescribing drugs din da zasu taimaka masa wajen dulling pain din da yake ji. Amma Hassan bai ji yayi promising komai ba. Haka suka karasa kwana a hotel tunda Hussain yaki kwana a asibitin.

Da safe ne da zasu taho yake cewa “da akwai wani abokina Sadiq, dan sarkin Abuja ne ina jin baka san shi ba dan a wani zuwa da nayi London muka hadu dashi kuma bai taba kawo min ziyara ba nima ones na taba zuwa gidan su tunda shi ba mazauni bane ba. Amma we are very close a waya munsan affairs din juna” Hassan yace “to ko zamu shiga ku gaisa?” A ransa yana fatan hakan zai farantawa Hussain rai, Hussain yayi murmushi yace “baya nan, ya bata” Hassan ya danyi dariya, “ya bata fa kace? Ya bata kamar yaya?” Hussain yace “wata yarinya yake so balarabiya, babansa sarkin Abuja yaki zuwa ya nema masa aurenta shine na bashi shawarar yaje ya nema da kansa, he went there kuma suka hana shi. Tun daga nan ba’a kuma jin labarin sa ba yayi cutting off ties da gida gaba ki daya har mu abokan sa babu wanda yasan inda yake. Rumors have it that ya sace yarinyar ne yaje ya aure ta, but babu wanda yasan a wacce kasar suke yanzu” Hassan ya bude baki yana mamakin wannan irin karfin hali na wannan bawan Allah, amma ya sani dole duk inda suka tafi ma watarana da kafafuwan su zasu dawo gida kuma yana guje musu abinda zasu tarar a gidan musamman saboda kasancewar su yan sarauta.

Hussain yaji dadin magungunan sa sosai, dan da suka kare shi da kansa ya kira Doctor din ya sake bashi wasu. Sun rage masa ciwon da yake ji a cikinsa sosai kuma yanzu yakan ita zama yaci abinci ya koshi, yaji dadin hakan dan hakan ya kara taimaka masa wajen kara boyewa Fatima halin da yake ciki. Cikin Fatima yana ta girma abinsa, cikin lafiya ita kuma cikin kwanciyar hankali dan babu abinda yake damunta, ga Hussain yanzu da yake kara makale mata kamar cingam dan office din ma yanzu ba fita yake yi ba in ma ya fita da wuri yake dawowa, yawon kasashen duniyar ma duk ya daina kullum yana tare da ita yana yi wa babyn cikinta hira, haka zai ta bawa cikin labarai yana dariya shi kadai ita kuma tana yi masa dariyar wautar sa “ba fa ta jinka” yace “injiwa? Haka ya gaya miki?” Tace “wai kai wa yace maka namiji ne? Na gaya maka mace ce” yace “ke wa yagaya miki macece? Ni na gaya miki namiji ne” tace “ai a cikina take ko? Muna communicating through placenta” yayi dariya “gori zaki yi min ko? Nima ai muna communicating through you, kuma ya gaya min shi namiji ne” tace “to aje a duba mana, sai a kure musu” yace “anki wayon. Ni bana so a kure ni”.

Sai dai ba wai rashin son a kure shine ya hana shi zuwa a duba gender din abinda yake cikin Fatima ba, damuwarsa shine yadda rabon gadonsa zai kasance idan ya mutu, dan haka ya yanke wani hukunci kuma ya gama tsara duk plans dinsa gabadaya sannan yaje ya samu Hassan a office dinsa ya ajiye masa takardu a gabansa yace “I need to sign these” Hassan ya dauki takardar yana jujjuya ta yana karantawa briefly, ya dago kai yana kankance idonsa yace “what is this? Me kake yi haka?” Hussain ya daga kafada yace “I am giving you half of h and h and all it’s assets. Dama sunan sa H and H ma’ana Hassan da Hussain, it is yours as much as it mine, ka sani kuma” Hassan ya girgiza kansa yana dawo masa da takardun gabansa yace “bazan karba ba kuma kaima ka sani, ba tun yau ba ka nuna kana son bani nace bana so saboda ni nafi son inyi working in kuma yi earning kudi na da kaina. Wannan naka ne, H and H naka ne ba namu bane ba kuma kai ma kasan wannan” Hussain yace “shikenan, in baka karba ba ya zama na lawyers dina dan already na riga na fitar dashi kuma sun saka hannu, yanzu saka hannun ka kawai ya rage” suka yi shiru suna kallon juna. Hussain yace “look Hassan, ba wai na baka bane dan baka dashi ko dan in taimaka maka ba a’a na baka ne as security for our family, ban san abinda Fatima zata haifa ba, in ta haifi namiji yayi muku katanga da duk wani abu dana mallaka ni kuma ba zan so haka ba, zanso ace kun gaje ni kai da kannen mu saboda dama dan in kula damu na fara business din nan. Gidan mu da wannan kamfanonin aka dogara gabaki daya, idan Fatima da danta suka karbe komai kai da Aunty da sauran yan’uwa zaku koma a karkashin ta kenan, you will be working under my son and wife abinda ni kuma ba zai min dadi ba duk da nasan Fatima kuma ina saka ran abinda zata haifa zai samu tarbiyya mai kyau daga gurinta da kuma gurinka. But zan so ace kun zama partners ne. Yadda ko ma me ta haifa you still have your share, wadda nasan zaka yi amfani da ita ne gurin kula da kanka da Aunty da yan uwan mu da yayan mu, all of them”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button