TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sumayya ita ma data cika da mamakin jin adam din a gidan su tace “Inna ban san yadda akayi yasan gidan mu ba, mai taxi ne kawai da wani lokaci yakan kawo mu gida daga makaranta” Inna tace “dan taxi? Dan taxi fa kika ce min Sumayya, menene hadin ki da dan taxi?” Sumayya tayi kamar zata sa kuka tace “wallahi inna babu komai a tsakanin mu, kawai……” “Babu komai a tsakanin ku yasan sunan ki?”

Yaron da yake tsaye a gefe yace “me zance masa?” Sumayya ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta, Inna tace “ki fita, ki tambaye shi me ya kawo shi, in bai gaya miki dalili mai kyau ba ki ce kar ya kara zuwa gurinki, bana son jaye jayen mutane kina ji ko?”

Sumayya ta mike da sauri ta shiga daki, Ruqayyah ta mike ta bita “ki bar ni inje in korar miki shi, irin wadannan mutanen in ba korar kare aka yi musu ba ba hakura suke yi ba” Sumayya ta saka hijab dinta tace “thank you, but I don’t need your help. Zan iya yi masa Magana da kaina”.

A jikin taxi dinsa ta same shi kansa a kasa yana daddanna wayar sa, fuskarsa da murmushi. Sai da tayi sallama sannan ya dago yana kallon ta yana kara fadin murmushin sa yace “ameen wa alaikumus salam Sumayya. Nice to see you a cikin kayan da ba uniform ba” sai ta samu kanta da yin murmushi “it is nice to see you too” sai kuma ta tuna da abinda tazo gaya masa “ya akayi kazo gidan mu Adam? Me kuma ya kawo ka gidan mu?” Ya mayar da wayarsa aljihu yace “laifi ne kenan dan na nemo gidan ku? In laifi nayi kiyi hakuri. Nazo ne kawai dan in ganki, ko shima laifi ne?” Ta girgiza kanta “wannan ba dalili bane ba, babata da kyar ta barni na fito kuma cewa tayi inzo in sallame ka, idan kuma Baba yazo ya ganni anan tare da kai inajin sai ya targada ni, dan haka dan Allah Adam ka tafi kafin yazo ya ganmu”

Yayi ajjiyar zuciya, fuskarsa tana nuna rashin jin dadi yace “lucky you. Yar gidan inna da Baba. Inna zata ce miki bari Baba kuma zai yi fada, kinji dadinki. Shikenan bara in tafi. Dama kwana biyu bana ganin ku a school ne shine nace bara inzo in duba ku ko lafiya?”

Sai taji kuma babu dadi, taji something a tone din da yayi magana dashi ya taba ta tace “lafiya lau Adam. Mun gode sosai. Mun gama exams ne dama neco kadai zamuyi. Mun gode sosai da kulawa” ya gyada kai yana cewa “I understand. Allah ya bada Sa’a. Allah kuma yasa kuyi amfani da result din ku. Ni ga nawa nan a ajjiye suna ta kura” ya dan huri iska ta bakinsa, trying to hide his emotions ya sake cewa “bara in tafi nasan zaku je islamiyya ko?”

Ta girgiza kanta “mu bama zuwa islamiyya ai. Inna Ade ce islamiyya mu, a gurinta muka koyi komai na ilimin addini da kuma duk wata tarbiyya ta musulunci” yayi murmushi “yan gata, kunji dadi. Lemme go kafin Baba yazo yayi fadan ganin ki tare da ni” sai taji tana son jin dalili chanjawar fuskarsa, amma kuma tana tsoron jan maganar kar tayi kaifi a gurin Inna Ade ko Kuma kar Baba yazo ya same su.

Ta tsaya tana kallon sa har ya bude motar ya shiga sannan tazo kusa da motar ta sunkuyo tace “thank you Adam for the visit. I relly appreciate it” yayi murmushi yace “thank you for seeing me” ya ja motarss yana daga mata hannu ya tafi. Ta bi motar da kallo har ta kule, sai taji a ranta tana son ta ji abinda yake zuciyarsa, tana son taji menene labarin sa, kuma taji tana son su sake haduwa watarana.

Da safe kafin Hassan ya tafi office ya biyo ya kawo wa Ruqayyah sim card dinta. Tana fitowa ta gashi a mota ta gaishe shi tace “na dauka aikowa zaka yi ashe da kanka zaka zo? Ko Hussain ai da sai ka aiko?” Yayi dariya sosai yace “Hussain? Hussain baya min ladabi ai, yace da minti biyar kawai na girme shi, baya ma kasar nan ya tafi China jiya. Akwai yara dai da zan iya aikowa amma I didn’t want to miss the chance to see you, ina so inga wannan early morning look din naki” tayi murmushi tana dan juya masa baya tace “bayan ko wanka banyi ba” yace “and yet, you look like a model”.

Ta dauko kwalin wayar da har yanzu bata ko farke ta ba, amma bai kar ba ba sai ya sa hannu ya bude mata daya side din motar yayi mata alama da hannu cewa ta zagaya ta shiga. Ta zagaya ta danyi jim tana kallon motar kafin ta shiga, ita bata taba shiga cikin private car ba sai yau, kuma tasan wannan motar ko a cikin motoci sunanta mota. Ta zauna tana zagaye idonta a cikin motar sai suka hada ido da Hassan yana mata murmushi, sai ta nuna alamar jin kunya, cikin kwantar da murya yace “you like it?” Ta gyada kanta tace “tayi kyau, sosai” yace “thank you. Sai anyi bikin mu zan koya miki mota, kinga in zaki je unguwa sai ki dauki mota a gida kawai ki fita abinki ba sai kin nemi driver ba” tayi murmushi, fuskarta cike da annashuwa sai kuma ta girgiza kanta tace “ni me zanyi da mota. Ni babu inda ma zan ke zuwa” yace “dan dai baki saba yawo babe ba, ba dan kar Baba yayi fada ba da sai in kaiki yawo yanzu kiga gari” ta mika masa wayar hannunta tace “ni dai hada min wannan wayar, ni babu yawon da zanje, ni ba inda nake zuwa”.

Ya karba ya bude ya fito da ita yana nuna mata, yana jin dadin excitement din fuskarta kuma ya fahimci a matsayin ta na wadda bata taba yin waya ko raka ni kashi ba dole ta zana excited idan tayi irin wannan wayar. Ya kunna ya saka mata komai yayi mata duk setting din daya kamata. Yana yi yana mata bayani dalla dalla na yadda zata yi operating komai.

Sai da ya tabbatar ta gane sannan yayi kamar zai mika mata sai kuma ya juya wayar ya dauke ta a hoto. Ya jima yana kallon hoton sannan ya miko mata, itama ta kurawa hoton ido, camera din ta fito da fuskarsa sosai tayi kyau, ga background na mota mai kyau, ga kuma kyakkyawan murmushi a fuskarta, sai taga kamar ba ita ce ba, sai taga kamar irin yayan masu kudi din nan wadanda basu da matsalar komai a rayuwa. Yes, that’s who she wants to be, yes, that’s who she is now.

Da yamman ranar ta shiga makotansu gidan su Minal, a tsakar gida ta same ta taba kwance tana daddanna wayarta. Ruqayyah ta zauna tana cewa “albishirinki Minal” sai ta mika mata sabuwar wayarta. Minal ta karba sannan ta mike zaune baki da ido a bude. “Na shiga uku! Ruqayyah a ina kina samu wannan wayar” Ruqayyah tayi dariya tana jinta tana yawo a saman gajimare. Sai dai tayi plan din ba zata gayawa friends dinta ba tukunna, so take tayi surprising dinsu, so take kawai sai dai su ga iv.

Tace “a inda nasamu bashi da muhimmanci, abu mai muhimmanci shine na samu din” Minal ta kuma juya wayar a hannun ta sannan tace “Ruqayyah wannan fa babbar wayar mijin Aunty Hafsa ne. Irin wannan din yaso siya ya kasa shine ya sayi karamarta ” (yayarta, wadda da kudin mijinta suke ji a gidan su’ Ruqayyah ya kara kumbura tace “kuma gashi ni nayi ta ba. Kinga, ni zuwa nayi ki bude min irin su facebook din nan da sauran su. Ni na kasa gane yadda zan bude”

Nan take Minal ta bude mata facebook account, tayi mata komai sannan tace “saura hoton da za’a saka miki” Ruqayyah tayi sauri tace “akwai wani hoto, zaki ganni a cikin wata mota shi zaki saka min” Minal ta budo hoton sannan tace “wannan motar kuma fa, motar waye?” Ruqayyah ta juya idonta tace “ina ruwanki, in ba zaki saka min ba ki barshi” sai Minal tace “daga tambaya? Ke fadan ki bw matsalar ki. Kinga, a shawarce kar ki saka hotonki, saboda shi facebook guri ne na maza da mata gabaki daya, kinga babu dadi ki saka hotonki maza suna ta kallonki, gwara ki saka wani abu haka” Ruqayyah ta gyada kai tana daukan shawarar ta, yasan Hassan ba zai kasa yin facebook ba, kar yaje ya ga hoton ta kuma a samu matsala, amma kuma taso yin fafa da wannan hoton, sai dai dole ta hakura.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button