TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Da daddare suna zaune a tsakar gida suna cin tuwon shinkafa miyar taushe har da nama, duk a cikin kudin da Hassan ya ajiye ranar nan ne. Gaba dayansu su hudu a tray daya Inna kuma da Baba suma suna ci tare, ga maganin sauro an kunna a gefe ga iska tana kada su. Baba yana basu labari “wato gobe akwai drama, an sake aiko mana fa mu koma wannan inta uku din nan. Gashi yaron nan Hassan naga alamar bai san dani a ciki ba sai dai kawai ya ganni” a lokacin suka ji tsayuwar mota sannan aka yi sallama. Sulaiman ne ya fita, an jima kadan sai gashi da bagco guda biyu da kuma karamar leda yana ta washe baki.

“Wato yammatan nan sai kun bani tukuici, wai wannan kayan sako ne inji Hussain yace ace muku “asha yammatanci lafiya”.

Wannan littafin na siyarwa ne, in baki sani ba kika karanta a rashin sani to yanzu kin sani. In kina son cigaba ki nemi wannan number 08067081020.Episode Fourteen : The Gate man

Da sauri Ruqayyah ta mike, zuciyarta fara kal kamar takarda, it is about time daya kamata suma su fara shigowa gari. Wannan talauci haka har ina!

Ta tari Sulaiman a hanya tana karbar karamar ledar cikin zumudi tace “inji Hussain ko inji Hassan?” Ya dan dakata yana tunani sai kuma yace “kamar dai Hussain yace min, oga Hussain, haka yace. Amma bara in koma in sake tambayar sa” ya ajiye kayan zai juya Inna Ade tace “kai! Dawo nan. In Hassan in ma Hussain menene abin tambaya? Duk daya ne in daya ya bayar tamkar dayan ya bayar ne “

Ruqayyah ta bude ledar hannunta, jikinta har rawa yake yi, tayi arba sa kwalayen waya guda biyu “wayyo Allah na” ta fada tana rungume kwalin wayar a kirjinta “Sumayya wayoyi ne, handsets ne ta so ki gani!” Sumayya ta ajiye cokalin hannunta ta mike da sauri tana karbar guda daya a hannun Ruqayyah sannan suka saka ihun murna suna rungume juna. Samarin kuma suka bude jakankunan suka fara fito da kayan ciki. Kayan sawa ne da sauran kayan bukatu na mata. Zunnur yace “wannan duk sanda ya sake dawowa sai naje na gaishe shi nima na samu rabona”.

Baba ya daga murya yace “lafiyar ku kuwa? Menene haka kuke yi? Menene wannan din?” Inna Ade ta karbe wayoyin hannunsu Ruqayyah sannan ta ja jakar zuwa gaban Baba, Ruqayyah ta biyo ta tamkar magnet, Inna tace “kaya ne baban biyu, Hussain ne dazu da bakanan ya zo yaga yaran nan shine yanzu ya aiko musu da kaya. Ta fada tana kokarin firfito masa da kayan, ya hade rai yace “kayan lefe ne?”

Ta yi dariya “kayan lefe kuma Baban biyu? Kayan lefen ne za’a aiko driver ya kawo?” Yace “to kayan menene?” Tace “kyauta ce kawai yayi musu” ya kuma hade rai “gaya masa sukayi suka ce basu da suttura? Ko kuma sutturar jikinsu ya raina” Inna ade tayi shiru, ya juya kan yammatan, “rokonsa kuka yi kuka ce ya siya muku?” Da sauri Ruqayyah, cikin rawar murya tace “wallahi Baba ba rokonsa muka yi ba, daya bamu kudi ma cewa muka yi bama so, shine kawai ya aiko mana” ya juya kan Inna Ade “to ba da ni za’a yi wannan abin ba. Yanzu me kike tunanin zai faru idan Hassan din yace ya fasa aurenta? Ya zamuyi mu biya su kayan su? Gidan nan zan saka a kasuwa?” A hankali Ruqayyah tace “ba zai ce ya fasa ba” ya juyo yana kallonta yace “to fitsararriya, ina magana kina mayar min ko? Ta yaya kika san ba zai ce ya fasa ba? Kin san abinda gobe zata zo dashi ne?”

Inna Ade tace “amma Baban biyu bana jin irin mutanen da zasu yi mana haka ne, in sun fasa ma bana jin zasu ce a biya su kayan su, kuma ma ai ba rokonsa suka yi ba” yace “to kaddara ma ba zasu ce a biya su ba. Yanzun in kika bawa wannan yarinyar” ya fada yana nuna Ruqayyah data rungume kwalin waya a kirjinta idonta ya kada yayi jawur “wannan wayar, kika kuma bata sannan leshin ta saka, idan ba’a yi auren ba ta yaya zata cigaba da girmama wannan” ya nuna wayar hannunsa “da kuma wannan” ya nuna kodaddiyar atamfar jikin Inna.

Ruqayyah ta maimaita “ba zai ce ya fasa ba” yayo kanta “in kika kara Magana sai na kakkarya ki a gurin nan na zubar da kasusuwanki” Inna Ade ta shiga tsakani tana bashi hakuri “dan Allah kar ka taba ta Baban biyu, dan girman Allah kar ka dake ta” ya juyo kanta “ki tattara kayan nan ki nemi gidan wata kawarki ki kai a ajiye, duk ranar da akayi auren sai a dauko su a basu”

Ruqayyah ta durkusa “Baba dan girman Allah kar ka karbe kayan nan, dan Allah ka bar mana abin mu, na tuba Baba wallahi na daina duk abinda baka so, dan Allah ka bar min kayana Baba” Inna Ade ta taya ta roko “ko ba zaka bar musu wayar ba ka bar musu kayan suma su samu suyi kwalliya, ba rokon su suka yi ba kyauta ce suka basu kuma shima Hassan din ai zai so ya ganta fes fes, gashi yan’uwansa suna zuwa, dan Allah Baban biyu kayi hakuri ka bar musu” yace “wato da saka hannunki kenan ko? Shikenan, su rike kaya amma babu ruwana”

Ya juya ya saka takalmi ya fita, Inna Ade tasan fushi yayi amma kuma bata son abinda zai kara hargitsa tsakanin sa da Ruqayyah, kuma ita tana ganin babu laifi in an karbi kayan.

Bayan ya tafi suka zauna suna dudduba kayan duk da dai duk jikinsu a sanyaye yake da fadan da Baba yayi, banda Ruqayyah da take ta lissafin wanne tailor ne yafi kowa iya dinki a kaduna? Gurinsa zata kai dinki. Ta dora wata doguwar riga kenan a cinyarta sai wata envelope ta fado daga cikinta, ta duba ta lura babu wanda ya gani sai ta zare ta ta saka a rigar ta. Tasan kudi ne a ciki, maybe kudin dinki, Bata so Inna Ade ta gani dan in ta gani karba zata yi kuma ba zata bata wani abin kirki ba kamar yadda wancan dubu ashirin din da Hassan ya ajiye musu duk Baba aka bawa ya siyo musu kayan abinci.

Bayan sun gama suka tattara kayan suka mayar ,inna tace sai da safe sai su dauki wanda zasuyi amfani dashi su kai gurin dinki “sai dai kuma sai an nemo kudin dinkin” inji Inna.

A daki bayan sun kwanta ita da Sumayya ne tace “Sumayya, kina ganin Hassan zai iya cewa ya fasa aure na?” Sumayya ta juyo tana kallonta tace “me yasa kike tambaya?” Tace “kawai dai. Baba baya son auren nan. Bansan me zai faru ba, ina jin tsoro” Sumayya tace “ki ji tsoron Allah. Kiyi ta addu’a” suka yi shiru kowa yana tunanin sa, har bacci ya fara daukan Sumayya sai Ruqayyah ta kuma cewa “Sumayya? Ya kika ga Hussain dazu?

Sumayya tace “ya kuwa na ganshi? He is okay” Ruqayyah tace “ba haka nake nufi ba, ina nufin yafi Hassan haduwa ko?” Sumayya ta mike zaune tana kallon ta tace “no……bai fishi haduwa ba, kar ma ki sake wannan tunanin dan Allah” Ruqayyah ta mike itama zaunen tace “ba wani abun nace ba ai, kawai dai kamar ya fishi…..” Sumayya tace “gayu? Ko kuma bagu da mota da kaya masu kyau da sababbin kudi” Ruqayyah ta fadi abinda yake ranta “ya fishi kyau” Sumayya ta runtse idonta tana jin zafin abinda yar uwarta take neman yiwa Hassan tace “bai fishi kyau ba. Ya dai fishi fari” Ruqayyah tace “ya fishi fari ko kuma dai kice shi fari ne shi kuma baƙi?” Sumayya tace “fari da baƙi duk halittar Allah ce, amma ni personally ma nafi son bakin mutum akan farin. Sannan ni bayan kalar fata banga wani banbancin halitta a tsakanin su ba dan kamannin su har abin mamaki ne dashi, hanci, baki, ido, shape din fuska, tsaho kirar jikinsu duk iri daya. Kuma Hassan yafi kama da matured kamilallen mutum shi kuma Hussain yafi kama da ladies man, ni in nice da zabi zan zabi Hassan sau goma kafin in zabi Hussain sau daya” ta koma ta kwanta tare da juya wa Ruqayyah baya cikin jin zafin maganar ta. Tana jin Ruqayyah tayi addu’a sannan ta kwanta, sai kuma tace “har dimple ne dashi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button