TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk mutanen gurin suka kwashe da dariya. “Wallahi to kowa ya jika a gurin nan har su Aunty” ya kashe wayar yana dariya. Kowa a gurin jan su yake a jiki, ana ta nan nan dasu, aunty tayi wa Sumayya godiya data zauna a tare da Ruqayyah. “In kina nan zata fi sakin jikin ta, tunda ita ba mai magana ba ce ba sosai”

Suka yi breakfast tare da family ga baki daya, sannan aka fara shirye shiryen tafiya, aka kai su Ruqayyah dakin yaya Hassana akace su shirya a can. Suna ta tunanin wadanna kayan zasu saka, su a niyyar si na jikinsu da shi zasu tafi dan a cikin sababbin kayansu suka dauko, amma sai sukaji ance suje su canja kaya su shirya. Ma’ana na jikin nasu basu yi ba. Suna cikin tunani sai ga kaya an kawo wa Ruqayyah, iri daya Aunty tayi musu ita da Hassana tunda sune amare, Ruqayyah ta saka doguwar rigar jan lace din mai kwalli tana kallon kanta a mudubi, tana noticing yadda shape din jikinta mai kyau ya fito sosai a jikin rigar, ashe duk tailors din da suke yi mata dinki bata mata kaya suke yi?

Ita kanta tasan tayi kyau sosai duk da bata yi kwalliya ba, amma kuma sai taji a ranta tana tunanin ko gimbiya fatima zata fita kyau? Ta dai ga tana da kyan fuska a hoto, ko tana da kyan jiki irin nata? Sai kuma taji tana fatan ya kasance bata da shi din da at least ya kasance ta fita da wani abu. “Ai babu wanda yake perfect” ta gaya wa kanta. Bayan ta gama shiryawa ne sai akace tazo ayi mata kwalliya, mai kwalliya ce aka dauko ta Musamman zata yiwa amare sannan da wata wadda zata yi wa sauran mutane duk mai so. Aka yiwa Hassana sannan aka yiwa Ruqayyah aka daura mata head, Ruqayyah ita kanta data kalli kanta a madubi bata gane kanta ba. “Dama haka take da kyau amma tsumma ya boye mata shi?” Tayi murmushi, tabbas tasan tafi gimbiya Fatima kyau.

Sumayya ma taje aka gyara mata tata fuskar akayi mata simple makeup, tayi kyawunta ita ma sosai da sosai. Ana ta hidimar shiryawa sai ga angwaye sun shigo tare da abokan su, suka je gurin su Aunty suka gaishe su aka yi ta saka musu albarka sannan akayi hotuna, Aunty ta aika aka kirawo su Ruqayyah, Ruqayyah ta taho idonta a kasa hannunta rike da jakarta, tana takawa a hankali yadda duk hankalin mutanen gurin ya dawo kanta. Hassan ya juyo ya kalle tavsai ya dauke kai, sai kuma ya sake juyowa da sauri yana kallon ta, wai Hassanar sa ce wannan, jinyake kamar ya rashi yaje gurinta ya gaya mata irin kyawun da tayi a idonsa amma yana jin nauyin iyayensa da suke gurin, sai ya bo ta da idanu kawai, a ransa yana jin dadin mayafin data saka ta rage bayyanar surarta. Nan akayi ta jera su ana daukan hotuna dasu, iyaye kowa ya shigo ayi dashi haka kanne ma da sauran yan’uwa. Anan Ruqayyah taga Hussain. Kaya iri daya suka saka shi da Hassan amma sai taga kamar tasa shaddar tafi haske ta Hassan tayi duhu, ko dan hasken fatarsa ne? Ko kuma a idonta ne taga hakan. Fuskarsa cike da annuri, idanunsa suna haske, dimple dinsa yaki komawa saboda murmushin da yaki daukewa daga fuskarsa. Kowa a gurin in ya gaishe shi sai ya ambaci sunansa kuma ya tambaye shi a game da wani abu daya shafe shi, ma’ana yasan kowa kenan, yasan affairs din kowa, kuma sai taga kamar yan uwan sunfi tafiya inda Hussain yake akan inda Hassan yake, ko ita ce take ganin haka?

Sai da aka shigo aka tuna musu da cewa lokaci fa yana tafiya sannan suka bar hotunan haka. Sai a lokacin Hassan ya samu magana da Ruqayyah. Yana kallon fuskarta yace “kinyi kyau sosai matata” tayi murmushi tace “kaima kayi kyau mijina” ya danyi gajeriyar dariya yace “maimaita in kara ji” ta saka hannu ta rufe fuskarta tare da dan juya bayanta kadan. Yayi dariya “zanji ne ai, one way or another. Kinsan wani abu?” Ta bude fuskar tana girgiza kai, yace “ji nake kamar in fasa zama in biku kanon nan” ta ji ranta ya fara baci “zaka bi mu kuma? Kai fa kace hutawa zaka yi” yace “yadda naga kwalliyar nan anya zan iya zama in sake kwana ina rungumar pillow” ta sake juya masa baya “kai dan Allah!” Sai kuma ta juyo tace “In ka bimu ma fa ba tare zamu zauna ba, ku kuma waje ko kuma kuna hotel mu muna cikin gida. Ni nafi si kayi zamanka anan kar kabi Hussain da abokansa su zo suyi ta wahalar da kai” yana murmushin gefen baki yace “really?” Tace “eh mana. Kaga gobe daurin aure biyu ne daku ga dinner da dare. You rest today” ya daga murya yana kiran Hussain “ka ga inda aka damu dani ake so in huta, kai kana mitar nace ba zan je ba ita tana cewa inyi zamana in huta” Hussain ya juyi yana kallon su sannan yace “soyayyar da muke yi maka ce daban daban, ni nafi sonka by my side through thick and thin, ita kuma ta fi son ta sha wahala ita kadai kai kuma ka huta” ya dauke kansa, Hassan yayi dariya yana ce mata “fushi yake yi wai nace ba zan je ba. I think zan je ɗin kawai, kar ransa ya kara baci” tayi shiru tana hararar bayan Hussain a fakaice, shine zai zamanto obstacle dinta kamar yadda gidan sa ta toshe mata ganin ta. Ya kuma tsaya mata a zuciyarta.

Har an fara fita ana shiga motocin da zasu tafi dasu airport sai Aunty ta kira Hassan dakinta suka tsaya tace “nace ka sallami Ruqayyah kuwa?” Yace “sallama kamar yaya?” Aunty tace “eh mana, zaka bata kudi sanoda liƙi da sauran abubuwa” ya zauna akan kujera yana dafe kanta “Aunty ita tace miki tana bukatar tayi liki? Shin wai ma menene amfanin yin likin? Yana daga cikin sharudan biki?” Aunty ta hade rai “to mu dai ko kayi mana wa’azi dai sai munyi, ya zamu je gidan biki gidan fitar kunya kuma na tabbatar za’a yi kida sannan kace ba zamu fita muyi wa amarya da ango liki ba? Ita kuma ya kake so tayi? So kake ta zauna ta zuba tagumi tana kallon mu muna yi?” Yace “Aunty, ke kinfi kowa sanin dalilin da yasa tuntuni naki auren yayan masu kudi saboda bana son macen data saba da barnar kudi da saka kaya masu tsada da sauran su, saboda a hala zata tarbiyyan tar da yaya na, a haka family na zasu tashi. Kuma babu wanda yasan abinda gobe zata zo mana dashi. Ni daban Hussain daban, kudi na daban na Hussain daban. Ranar da bani dashi kuma yaya zanyi dasu aunty? Shi yasa nayi murna da Allah ya hada ni da Hassana saboda background dinta da kuma halayyar ta sannan da yarintar ta yadda zanji dadin tarbiyyan tar da ita akan tsarin rayuwa ta ita kuma ta tarbiyyan tar da yaya na. To yanzu idan kuma na fara nuna mata zubar da kudi a kasa a gurin biki dole ne me akayi kenan? Ai anyi ba’a yi ba ko?”

Aunty tace “to mister smart, komai sai ka nuna wa mutane kai kamar ka fimu iyawa. Wannan dai biki ne, kuma har yanzu bikin ku ne ba’a gama ba, ka dauko kudin liki ka bata tun muna shaida juna ni da kai” yayi ajjiyar zuciya yana shafa aljihun sa sannan yace “i don’t have cash on me, in na fita zan samu sai in bata” ta nuna masa kofa, “jeka daki ka dauko ka kawo mata ina nan ina jiran ka” yayi murmushi yana karya wuya, tace “ai na fika wayo, ni na haife ka fa ba kai ka haife ni ba”. Dole ya tashi yana murmushi ya tafi tsohon dakin sa, ya bude drawer ya dauko kudi yana jujjuya, ya gama plan din abinda zaiyi da kudin nan, yayi tsaki sannan ya mike ya fita.

Yau dai sai ga Ruqayyah da Sumayya a jirgi. Ruqayyah ta maze wai dan kar tayi kauyanci ayi mata dariya amma lokacin da jirgi zai tashi ji tayi kamar dodon kunnen ta ne ya fashe a cikin kunnen, amma taki tabawa dan kar wani ya gani yace tayi kauyenci, ta kankame rigarta cike da tsoro amma fuskarta babu ko alamar tsoro a ciki. Ta shanye kayanta. Suna sauka suka tarar an aiko da motocin da zasu tafi dasu gidan sarautar kano, suka shiga aka kaisu sannan akayi musu jagora har masaukin su, daga nan aka shiga hidimar kawo musu abinciccika na alfarma irin na sarauta, wani kalar abincin ma Ruqayyah bata taba ganin sa ba. Nan take bayi da hadiman gida suka fara saving dinsu, daga kinyi motsi za’a ce “me kike so? Me za’a karo miki? Ko kafafuwan ki sun gaji a tausa miki su?” A haka har sai da aka tabbatar kowa is fully satisfied sannan aka yi musu jagora zuwa wani katon palo da yafi kama da hall din taro amma yasha shimfidu da kujeru na alfarma. Anan Ruqayyah take tambayar kanta ko wannan ce fadar? Amma kuma bata ga karagar sarki ba, sai taga an nuna musu kujerun suka zazzauna sannan sai ga matan gidan suna isowa daya bayan daya ana gaisawa dasu cikin mutunta juna da karramawa. Duk inda Aunty zata je hannunta yana rike dana Ruqayyah, duk Wadda suka gaisa kuma zata nuna mata Ruqayyah tace “ga daya ƴar tawa, matar Hassan ce, jiya aka kawo ta” nan da nan sai taga an jata an rungume “ga yar uwar Fatima” “Allah ya baku zaman lafiya” “Masha Allah, kyakykyawa daita kuwa, ya sunan ki?” A haka a haka har laasar tayi, Ruqayyah tana cewa “wato ita ogar ba zata fito ba ko?” Bakin cikinta kawai kar kwalliyar ta ta karasa lalacewa ba tare da Fatima ta fito ta ganta ba, kar ta raina ta, tunda taji ance first impression matters alot.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button