TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Su dai yan aiki basu ce komai ba dan basu da abin cewa, wannan magana ba tasu bace ba, amma sun san wadda aka aura din dan tun satin da ya wuce ake ta tsegumin abin a tsakanin yan aikin gidajen da drivers da masu gadi, kowa yana fadar albarkacin bakinsa wasu suna ganin kamar hakan ma ba musulunci ba ne ba. Amma ganin ita din wadda aka yi wa rashin kyautawar bata ce komai ba yasa suma basu ce mata komai ba, ashe bata sani ba.

Har ga Allah su tausayin ta suke ji dan aganin su karshen rashin adalci anyi mata, saboda ta zama musaka sai mijinta ua sake ta ya raba ta da yayanta sannan ya auri kanwarta? Wannan wanbe irin rashin adalci ne?

Jin sunyi shiru yasa Ruqayyah ta tabbatar da maganar, ta tabbatar kuma sun sani, sau ta kwace daga hannun su ta zauna a kasa ta dira hannu aka ta fara rusa kuka da duk iyakacin karfin ta, tasan waye ya kulla wannan abin, tasan Baba ne,dama ai ba tun yanzu yake ikirarin aurawa Hassan Sumayya ba saboda ita baya sonta ya tsaneta, saboda ya fi son Sumayya akan ta, wannan kawai shine dalilin sa ba wai wani abu ba.

Ba zasu kyale ta da bakin cikin shakulatin bangaro da suka yi da rayuwar ta ba a matsayin su na iyayenta duk da cewa sun san tana bukatar kulawar su a halin da take ciki amma shine zasu yi mata bi ta da kulli da wannan mummunan lamarin? Ita kuma Sumayya, munafuka, bayan alkawarin da tayi mata shine ta karya ta aure mata mijinta? Wanny shine dalilin da yasa tayi blocking dinta a waya saboda tana busy yaudarar Hassan da nuna masa cewa ita ta Allah ce kamar yadda ta saba yi tun suna yara.

Shi kuma Hassan, munafiki, dama can watakila yana som Sumayyan shine ma dililin da yasa yayi sauri sakin ta kuma har saki uku a lokaci daya dan yaje ya hada baki da Baba ya auri kanwarta. Wallahi basu isa ba, sai ta yi maganin su gaba ki daya, sai ta hana su zaman lafiya, wannan auren ba zasu zauna ba.

Ta sake jiyo wata gudar, kamar kuma a gidan Hassan, wato gyaran data lura ana tayi a gidan kenan? Ita da taga ana aikin ta dauka siyar da gidan zaiyi shima ya sake yin wata sadakar ashe munafikin aure zaiyi, auren ma kuma twin sister dinta.

Tana son ta fita taje ta tara musu mutane akan su kowa ya fahimci irin cin amanar da akayi mata amma kuma bata son fita a yanayin da take ciki, tunda ta sami nakasa ta rasa self confidence dinta, bata son shiga mutane dukda cewa dama can ita ba mai son mutanen bace ba, yanzu kuwa sai take ganin kamar duk wanda suka hadu dashi kallon yamusashshiyar kafarta yake yi.

A gidan Hassan kuwa gida ya cika makil da mutane, kowa sai fadan albarkacin bakinsa yake yi a game da irin chanjin da gidan ya samu, ba zata taba cewa wancan gidan bane ba dan komai an chanja masa tsari. Yanuwan Hassan sunje sun dauko Sumayya wadda tasha nasihohi da adduoi da kuma tarin albarka daga gurin iyayenta da duk yanuwan da suka san gaskiyar abinda ya faru.

Zuciyarta wata iri take jinta tayi mata wani irin nauyi saboda kukan da tasha, tun safe take kuka har dare, sai dai bata tare da bakin ciki, ita kanta tasan biyayyar da tayi insha Allah ubangiji ba zai barta ta tabe ba, tasan Allah zai sanyaya mata zuciyarta ya cire mata son Adam ya saka mata son mijinta wanda ita kanta tasan shi din already ya fara sonta saboda yadda ta lura yana lallaba ta.

Kamar yadda Aunty da hajiyan kano suka kamo Ruqayyah haka suka kamo Sumayya wannan karon ma, karkashin rakiyar gwoggo Habibah da matar kawu Sama’ila har zuwa gidan mijinta, suna shigowa duk da chanjin da akayi wa gidan sai da Sumayya ta tuna da ranar da aka kawo Ruqayyah, ta tuna da kukan da tayi a ranar da yawon da Adam ya tafi da ita har sai da ya ga tayi murmushi sannan ya dawo da ita gidan, ta tuno da yadda ta shigo ta tarra Ruqayyah tana ta gursheken kukan bakin cikin gidan Hussain yafi na Hassan kyau.

Sai ta daga kanta tana kallon gidan Hussain, tana jin a ranta cewa yanzu twin sister dinta kuma tsohuwar matar mijinta tana cikin wannan gidan, zasu yi kuma zaman makotaka, a matsayin su na wadanda suka hada miji a mabanbanta lokuta kuma a matsayin su na tagwaye.

Aka shigar da ita da kafar dama da bismillah zuwa gidan ta, da fatan sai mutuwa ce zata fitar da ita daga gidan. A palo aka zaunar da ita akan kujera, Yusuf a hannun ta na dama Aminu a hannun ta na hagu ga kuma Hussain akan cinyarta, fuskarta da jikinta gaba ki daya katon farin mayafin ta. Yan uwa ana ta daukan hotuna da ita, masu nasiha nayi masu saka albarka nayi.

A lokacin ne suka ji kururuwar Ruqayyah ta shigo, muryarta har ta dashe saboda kuka, “wallahi baku isa ba, karya kuke yi munafukai, azzalumai, maciya amana, almurai, wallahi kunyi kadan ku yi min wannan cin mutuncin” a bakin gate take amma har cikin gidan ana jiyo ta. Nan take jama’a suka dunguma suka fita kwallon ta, masu kokarin bata hakuri suna yi masu tsegumi suna yi. Kokari take lallai sai ta shigo ana riketa, yan uwan Baba dana Inna Ade ne masu kokarin riketa su hana ta shiga ciki yayinda yan uwan Hassan suka zama yan kallo, ita kuma ga babu kafa, ga masifa tana cinta, so take ta shiga ciki ta kalli idon Sumayya, ta kalli idon munafuka.

Sumayya tana jin ta amma bata ko motsa daga inda take zaune ba kuma bata bar yaran sun motsa ba suma, amma duk abinda Ruqayyah take fada tana ji, kuma munanan kalaman ta suna taba har cikin zuciyarta. A lokacin ne ta jiyo murya kamar ta Hassan, ita bata san ma yana gidan ba ko kuma kirawo shi akayi ya taho oho.

“Ki kama hanya ki fitar min daga gida Hassana, kar ki sake ambaton matata da wata kalma marar dadi idan kuma kika sake wallahi sai na yi miki marin da zaki rasa idanuwan ki bayan rashin kunne da kafa. Waye yaci amanar ki? Ke kika ci amanar kanki, ke kika zabi kudi a madadin ni mijin ki da yayan ki da iyayenki da yan uwanki. Bakin cikin abinda kika yi ya saka babanki ya bani kanwarki ita kuma ta karba saboda ta faranta zuciyoyin iyayen ku da kika riga kika bata. Kin zabi kudi, na baki kudi, me kuma ya rage a tsakanin mu? Menene kuma abinda ya rage wanda zaki zo ki karba a hannuna?”

Hassan ya kula ta yabata amsa ne saboda yana son ya wanke Sumayya dashi kansa a idon mutane, yana so ya gaya wa mutane ita ta zabi kudi a kansa ba wai dan ta nakasa bane yarabu da ita ba.

Ta yi kokarin kamo hannunsa “mijina, kar kayi min haka, ni na hakura da kudin da Allah kar ka auri kanwata, dan Allah Hassan, wallahi ina sonka, na hakura da kudin ka mayar da ni dakina dan Allah, na gaji da wannan rayuwar Hassan ka tausaya min dan Allah. Yanzu bana son kudin, bama ni nake cin kudin ba dan Allah ka saurare ni mijina. Wai ina son da kake yi min ne? Ta fada cikin matsanancin kuka

Yace “so? Wanne irin so kike magana akan shi? Ni wadda naso kuma nake so ba ke bace ba, I fell in love with halayen da nayi tunanin naki ne ashe ba naki bane ba, ashe na yar uwarki ne kika ara kika yafa wa kanki, sai yanzu na fahimci dama can ashe Sumayya nake so bake ba, rabo ne yahada ni da ke kuma rabo ya kare tsakanin mu”.

Sumayya duk tana jin su, hawaye yana zubowa daga idanunwanta yana sauka akan rigar Hussain da yake kan cinyarta. Bata taba jin Hassan yana fada ba sai yau, ashe dama fada ne dashi haka? Tana ji har hayaniyar ta lafa daga alama an fitar da Ruqayyah daga gidan amma ita tasan this is not the end but the beginning, tafi kowa sanin hali da kuma masifar Ruqayyah tasan tabbas zata dawo ko ba yau ba ko gobe ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button