TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Hassan ya fitar da kudi masu dan kauri ya bawa Sumayya wai ko zata yi wasu events haka, amma sai taki karba tace ita babu abinda zata yi, sai yaji bai ji dadin haka ba tunda shi yasan ita din mai son kashe kudi a biki ce, sai yayi tunanin ko dan bata son sa ne ya saka ba zata yi ba? Sai ya bawa Zulaihat ta kawo mata kuma ta roke ta on his behalf ta karba, ita kuma sai ta karba din dan bata son ayi ta jayayya musamman tunda ya saka Zulaihat a ciki. Sai bayan Zulaihat ta tafi sannan ta kira shi tayi masa godiya yace “ko kefa, har na fara tunanin ko laifi na ne ya shafi bikina” tace “wanne laifi kayi kuma? Kawai dai babu abinda zanyi dasu ne shi yasa” yace “duk son ki da biki kuma sai a naki zaki ce ba kya so” tace “haka ne ina son biki, ina son ayi ta hidima haka da mutane ayi ta abubuwa amma ba hakan yana nufin ni ina da ra’ayin shiryawa da kaina ba. Kuma ni bani ma da kawayen da zanyi wa wata hidima” yace “ina kawayen ku? Wadanda kika gayyato da wancan bikin?” Baya son ambatar sunan Ruqayyah a duk lokacin da suke tare da Sumayya saboda baya son ya tuna mata tsohon matsayin sa a gurin ta. Tace “wai da bikin Ruqayyah? Ni ban san su ba fa, ita ta nemo abin ta, duk kawayen mu ma na school kin gayyatar su tayi tace basu kai matsayi ba” yayi shiru yana cihe baki, he thought as much, but so yake ya tabbatar, ya sake cewa “ohh na dauka naki ne ai, tunda naga ke ce kirjin biki a lokacin, harda yi min text din in kara muku kudin biki” ya danyi dariya “shi yasa nayi mamaki yanzu da kika ce ba kya so” ta bata rai kamar yana ganin ta tace “wanne text? Wanne kudi?” Tun kafin ya bata amsa yasan inda maganar ta dosa, ya fahimci Ruqayyah ce tayi masa text da number din Sumayya dan ta cigaba da yaudarar sa da kyawawan halaye, what more ne Ruqayyah tayi wanda bai sani ba? Sai yaji yana jin tsoron sanin wannan amsar.

Yayi saurin cewa “forget about it, ki bar maganar kawai, and saboda ina son in faranta miki duk abinda kika shirya zanzo” tace “a’a fa, kayi zamanka kawai, babu abinda zanyi sai walima tare da few friends dina shikenan, sai abinda zasu yi a gida kawai”

A dole ya hakura ya rabi da ita duk da dai yaso ace ta saki jiki tayi bikinta sosai, amma ita kuma a nata bangaren ta ki yin komai a bikin ne dan bata son maganganun da mutane suke yi akan auren, ta san duk kawayensu na unguwa da na primary da secondary school duk sun san mijin Ruqayyah zata aura dan haka duk ba zata gayyace su ba dan kar suzo su kara mata wani takaicin akan wani, kawayenta na jami’a kadai zata gayyata suyi walimar su a nutse inda Inna Ade da kanta zata yi hosting walimar ta kuma yi musu wa’azi akan zaman aure a musulunci. Yan uwa da abokan arziki ma dukka are invited dan walimar ita zata yi serving a matsayin yini, bayan ita kuma sai ayi kamu da daurin aure shikenan da dare akai amarya. Ita albarkar auren take nema, tana kuma neman Allah ya bata ikon cin jarabawar ta dan wannan auren ta san shine jarabawarta. Ta kuma daura damarar karbar sa hannu bibbiyu da fatan samum dacewa albarkar biyayyar da zata yiwa iyayenta.

Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya inji Hausawa, ranar da aka saka tazo kuma aka daura auren Hassan Aminu Abdullahi da Sumayya Yusuf. Sumayya ta sha kuka kamar ranta zai fita duk dauriyar da ta ringa yi akan maganar amma labarin daurin aure ta yana zuwa kunnenta ta fara kuka, dan wannan labarin shi yake tabbatar mata da cewa tayi bye bye da Adam, ita dashi sai dai wata kaddarar da ita kanta bata yiwa kanta fatan ta dan zata so ace zaman auren su da Hassan ya dore har tsufansu, sai ta samu kanta da tambayar kanta ko yaya Adam zai kalli auren nata in labari ya je masa? Musamman in ya san wanda ta aura din? Shin zai fahimci maganar ko kuma zai saka ta a matsayin cin amana? Kamar yadda tunda aka fara maganar take tunanin Ruqayyah a zuciyarta, shin tasan da maganar ko bata sani ba? Ya zata dauki maganar?

Ita ta fi kowa sanin cewa Ruqayyah bata son Hassan, tun sanda suna gida kafin ayi aurenta ta san bata son Hassan kudinsa take so kuma yanzu ta samu kudin, shin zata damu idan taji cewa twin sister dinta ta auri tsohon mijinta uban ƴaƴan ta. How will she reacts?

Ai kuwa dai Ruqayyah bata da labari sam dan ita gidanta kamar kango yake, ga shi dai hadadde kayatacce amma kuma babu kowa sai yan aiki, su kadai suke bidirin su a gidan dan ita sai ta kwana biyu ma bata sauko kasa ba dan yanzu saukowar tana yi mata wahala sosai, sai dai da safe a shiga a gyara mata dakunan ta sannan akai mata breakfast, in an gama na rana ma akai mata, duk abinda babu kuma a gaya mata ta bayar da kudi a siyo.

Sometimes sai take wondering wai kudin nan ma kamar yan aikin ne suke cinye su dan ko ba komai abincin da take siya duk wata ba ita take cin kashi daya cikin goman shi ba, bata so kuma ta matsa musu kar su tarwatse su barta, ga kuma albashi da take basu duk wata. Wannan yasa kudin da take son tarawa dan ta nemi magani suka gaza taruwa tunda duk wata sai ta fitar da kudin wancan cima zaunen ta tura masa.

A ranar da aka daura auren ne bayan tayi sallar magrib tana ta shige da fice a social media, dan yanzu nan ne gurin hirarta a nan ne kawai take ɗebe kewarta sai taga Khadijah ta saka hoton Hassan da Sumayya, a kasan hoton ta saka “Allah ya sanya alkhairi yaya H1, Allah yasa abokiyar tsufaka ce” ta tashi tana murza idonta dan ta tabbatar da abinda idon nata yake nuna mata, ko dak shima idon ya fara samun matsala ne kamar yadda kafarta da kunnenta suka samu?

Still dai hoton Sumayyan ta sake gani taci kwalliya irin ta amare tana murmushi duk da dai fuskarta ta dan kumbura kamar tayi kuka sosai, Hassan kuma a gefenta bakinsa har kunne. Ta mike da sauri, tama manta cewa yanzu bata iya mikewa tsaye sai da croches, wannan yasa ta fadi flat akan fuskarta akan tiles din falon, a take bakinta da hancinta suka kama zubar da jini amma ba shine abinda yafi daga mata hankali ba, wayar ta ta sake laluba tana kuma kallon hoton Hassan mijinta uban ƴaƴan ta da kuma Sumayya kanwarta twin sister dinta. Da sauri ta shiga comments taga mutane suna ta addu’ar fatan alkhairi, ta fita ta fara laluben accounts din sauran kannen Hassan, duk sai taga suna ta celebrating abin ba wai Khadijah ce kadai ba.

Ta lalubi crutches dinta ta mike da sauri ta bude kofar da zata sadata da valcony din dake hade da palon da take zaune a ciki, ta fita tana leken gidan Aunty sai ta ganshi a cike da motoci, mutane suka ta hada hadarsu, can da nisa ta jiyo wata ta rangada guda. Ta girgiza kanta tare da marin kanta kadan dan ko zata farka daga mafarkin da take yi “no!” Ta fada da dan karfi, it can never be, ta yaya mijinta zai auri twin sister dinta alhalin gata da ranta tana numfashi? Ta yaya haka zata kasance?

Ta juya da sauri ta dauki hanyar fita, ba zata iya kirga yawan faduwar da tayi ba kafin ta sauka palon kasa sannan ta tsare yan aikinta da suke zaune rashe rashe a kan kujeru a palo suna kallo tace “bikin wa ake yi a gidan Aunty?” Tayi maganar da karfi tana goge jinin da ya fito daga bakin ta. Duk suka kalli juna sannan suka kalle ta, wai dama bata sani ba? “Ba tambayarku nake yi ba? Bikin wa ake yi?” Saya daga cikin su tace “daddyn su Yusuf naji ance an daurawa aure dazu da safe, amma ban san wa ya aura ba” tayi kokarin damko wadda tayi maganar amma saboda cika crutch din da tayi sai ta tafi zata fadi, suka rike ta “karya kike yi kice baki san wadda ya aura ba, kuna sane baku gaya min ba, kuna sane kuka bari mijina ya auri kanwata”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button