TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A office din bayan sun gaisa da doctor din sai ya saka Hussain ya kwanta a kan wani gado ya mike kafafuwansa sosai sai doctor din ya tsaya a kusa dashi yana yi masa tambayoyi yana amsawa, sai ya dora hannunsa a kasan cikin Hussain ya dan danna da dan karfi, Hussain ya mike zaune da sauri yana damkar hannun doctor din ido a waje yace “ouch, zafi sosai fa” sai doctor din ya bishi da kallo kawai, Hassan ya mike da sauri yana rike hannun Hussain wanda lokaci data gumi ya rufe masa fuska, jikinsa har rawa yake yi.

Sai doctor din ya koma ya zauna yayi rubutu a takarda. Hassan ya koma gaban doctor din ido a bude yana tambayar, “yani zafi, me hakan yake nufi doctor?” Doctor ya dago yana kallon Hassan, ya kasa kallon Hussain yace “ba zan iya ce maka komai ba a yanzu. Zan tura ku dakin gwaje gwaje za’a yi hotuna kuma za’a dauki samples ayi gwaje gwaje. Sai result ya fito sannan zan iya cewa komai” Hassan ya karbi takardar da sanyin jiki sannan ya taimaka wa Hussain ya mike suka fita Hussain yana rike da marar sa. Wata maaikaciyar lafiya tayi musu jagora zuwa katon lab dinsu, inda aka fara gudanar da bincike sosai akan Hussain amma sai daya ja musu kunne kar wanda ya kuma danna masa marar sa, nurses din suka yi dariya suka ce ba zasu yi ba.

Har dare suna can, sai da suka yi exhausting energy din Hussain gaba ki daya sannan suka rabu dashi yana ta yi musu mita. Suka ce washegari ya dawo za’a yi mishi abinda suka kira da colonoscopy. Hassan dai ya lallaba shi suka tafi, a daren Hussain yayi ta bincike akan menene colonoscopy din sai ya fahimci zasu zura mishi micro cameras ne cikin hanjinsa ta yadda zadu ga ko menene a cikin hanjin a screen, anan zasu fi fahimtar in akwai ko babu kuma zasu san exact location din da ciwon yake da kuma stage din da yake ciki. Shi dai a ransa baya so, zuciyarsa tana ta gaya masa cewa ya hada kayansa cikin daren ya gudu ya dawo Nigeria amma yasan in ya gwada yin haka sai sunyi rigima da Hassan, kuma shi yayi alƙawarin ya daina fada da Hassan amma kuma yasan gobe za’a tabbatar masa da cewa yana da wannan ciwon, shi kuma baya son a tabbatar masa din saboda yana son ya cigaba da rayuwarsa freely har zuwa mutuwarsa, wadda yasan zata iya riskar sa gobe ko kuma nan da shekaru masu yawa, Allah ne kadai masani, akwai hikima a cikin tsarin ubangiji da ya hane mu da neman sanin gaibu dan ba zai yi maka dadi ba, ta yaya zaka iya rayuwa in aka gaya mata nan da wata biyu ko uku zaka mutu?

Bai gudun ba ya zauna, ranar da sassafe suka je suka zuwa akayi preparing Hussain aka yi masa allurar bacci, sai Hassan yaji zuciyarsa ta karye dan haka doctor din ya amince masa cewa zai iya shigowa ayi a gabansa. “It is not a surgery, we are just going to view the tumor on a screen and classify it. Then take a sample, that’s all”.

Hassan yana zaune rike da hannun Hussain aka gama procedure din, doctor din yana nuna masa abinda yake gani yana kuma yi masa bayani, ya nuna masa ciwon da idonsa ya gani ya kuma gaya masa tun jiya da yayi wa Hussain manual exam ya fahimci cewa akwai ciwon da gaske, ganin hankalin Hassan ya tashi sosai sai ya kwantar masa da hankali ta hanyar gaya masa cewa ba wani problem bane ba tunda an yi detecting da wuri kuma akwai means na neman magani babu wani problem, ya gaya masa kuma yayi iyakacin kokarin sa na ganin ya kwantar wa da Hussain hankali dan lokuta da dama tashin hankali shi yake kashe patient ba wai ainahin ciwon ba. Ya kuma jaddada masa muhimmancin jin surgery da wuri “ita cancer tana spreading ne, tana kara yaduwa, in aka barta zata ci gaba kuma ba zata tsaya a hanjin kadai ba zata taba wadyu vital organs din da suke cikinsa. Dan haka I suggest ayi surgery as soon as possible. Daga anyi surgery an cire tumor din sai kuma a kashe surrounding area din da radiotherapy yadda in akwai saura ma zata mutu” Hassan ya gyada kansa yana assuring doctor din cewa kafin su bar kasar za’a yi surgery din. Ba zai bar kasar ba sai da healthy Hussain.

Sanda Hussain ya farka, Hassan ya gani a gefensa rike da hannun sa ya kwantar da kansa a jikin gadon da Hussain yake kwance idonsa a rufe. Hussain ya dago hannunsa ya dan taba fuskarsa yace “hey bro” Hassan yayi saurin bude kumburarrun jajayen idanuwan sa ya dora akan Hussain, sai yaga Hussain din yayi masa dariya yace “have you been crying?” Ya sake dariya “sai na gaya wa Ruqayyah mijinta rago ne” Hassan ya harare shi ya tashi ya shiga toilet ya wanke fuskarsa ya fito sai ya tarar dashi yana kokarin tashi zaune sannan ya zare drip din da aka saka masa. Ya kamashi yana kokarin kwantar dashi amma yaki kwanciya ya tashi yana cewa “ni yunwa nake ji wallahi, kamar anyi min sata a hanji na” sai kuma ya bude ido yana kallon Hassan yace “gaya min gaskiya, ko har sun yanke hanjin ne?” Sai kawai yayi dariya ya kama hanyar fita.

Hassan ya bishi amma yaki dawowa, sai da ya tuna masa da cewa rigar asibitin ce a jikin sa sannan ya dawo briefly ya mayar da kayansa ya kuma fita. A dole Hassan ya dauko takardun su da kuma wayoyin su ya biyo shi a baya. Sai da suka je gurin cin abinci suka zauna suna ci sannan Hussain yace “na san abinda doctor yace, you don’t have to tell me, na riga na gaya maka dama kai ne baka yarda ba. Yanzu tunda ka yarda can we please go home? I have to get back to making that baby you know?”

Hassan ya dauke kansa gefe yace “babu wani home da zaka tafi, you are going to have a surgery next week. Na riga nayi filling takardu har na biya kudi” Hussain ya bude ido cikin mamaki yace “no, na riga na gaya maka am not going to go through that” ya ajiye spoon din hannunsa ya mike ya fice daga gurin. Hassan ya biya bill da sauri ya bishi a baya. Ya tarar dashi a hanya suka jera yana cewa “Hussain Please, doctor din nan fa yayi min bayani, ya nuna min komai a screen na gani ba wai wani guri ne mai yawa ba, yace da zarar sunyi surgery sun cire shikenan sai…….” Hussain yace “sai ayi radiology a kashe gurin sannan chemotherapy dan a tabbbar komai ya mutu, after three months kuma sai in dawo a sake wani colonoscopy din a gani idan bata yi regrowing ba, idan kuma tayi sai a sake going through that same precess, a haka har sai hanjin ya kare yadda babu abinda za’a kuma yankewa, ko kuma in ta taba wani vital organ din, sai kuma abar mutum ya karasa mutuwa, yes I know about all the process and no am not going through that. Na gaya maka tun acan”.

Haka suka yi ta fama har suka je hotel din da suka sauka, suna ziwa Hussain ya fara hada kaya yana zubawa a jaka Hassan kuma yana kashewa yana mayar wa gurin ajjiyar kaya, “waye ya gaya maka zata sake regrowing? Dan ta wasu tayi that doesn’t mean taka ma zata yi. Doctor din fa yace tana stage 2, he is 90% sure cewa zai iya cire ta completely” Hussain yace “I am sorry but I don’t believe him. Tunda za’a bashi kudin sa ya karbe ai zai fadi haka dama. Ni ba zan bari likitoci su mayar dani lab animal dinsu ba”.

Hassan ya koma ya zauna yana kallon Hussain, he have been stubborn and strong headed tun suna yara, anty ma da kanta ta sha ba da labarin irin taurin kansa da yadda yake bata wahala kafin ta juya shi, in yasa kansa abu to kuwa sai da dabara kafin a iya hana shi. Sai ya dauko wayarsa yace “shikenan tunda kaki jin magana ta, bara in kira Fatima in gaya mata halin da ake ciki watakila in ita tayi maka magana zaka ji” sai Hussain ya tsaya daga hadan kayan da yake yi yana kallon Hassan yace “you won’t do that, ai amana na baka maganar nan, kana nufin zaka karya alkawarin da kayi min na cewa ba zaka gaya wa kowa ba?” Hassan ya daga kafada yace “yes of course, idan har hakan yana nufin saving life dinka ne zanyi. Kuma try me ka gani idan ba da gaske nake ba” Hussain ya tsaya yana kallonsa, baiga alamar wasa a fuskarsa ba sai ya ajiye kayan hannunsa ya hau kan gado ya kwanta, sai kuma ya tashi ta shiga toilet yayo alwala ya fito ya tayar da sallah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button