TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai dare Ruqayyan ta koma gida, bata shiga gurin Aunty ba dan kar tayi mata fadan ina taje ymtayi dare haka sai ta wuce part dinta ta hau sama direct tunda ta riga taci abincin ta a can gidan. Tayi wa yaranta wanka tana ta yi musu wasa suna dariya gabaki daya, tana jin son si sosai a zuciyarta irin son da bata taba yi wa kowa irinsa a duniya ba. Sai dai kuma a ranta tasan bata son su taso a karkashin masu kudi, tafi son su taso a matsayin masu kudi kuma tasan she is going to make the right decision at the right time. Ta dauki wayarta ta kira layin Hassan na india. Kullum kamar lokacin suke yin waya duk da shi a gurinsa cikin dare ne amma ta fahimci kamar baya bacci sosai, ko kuma da rana yake baccin ne oho.

Ring daya ya dauka yace “yanzu nake tunanin kiran ku inji yadda yarana suka wuni” ta bata rai kamar yana kallonta tace “yaranka kadai? Ni ba zaka ji yadda na wuni ba? Allah sarki ni babu mai sona” ya danyi murmushi yace “ni na isa ince haka? Kin san yadda kike hana min bacci kuwa?” Tace “kamar gaske, baya ka fin ku tafin ma wani shashshare ni kake yi” yace “na tuba ai, kwana biyu da babu ke ai jiki na ya gayamin” tace “kai da baka da lafiya? Ko dama ciwon na yan gayu ne” ya danyi dariya, sai taji wani iri, yaushe rabon da taji yayi dariya ko a wayar ne tana iya jiyo rashin nutsuwa a muryarsa, tace “masha Allah, jiki yayi sauki kenan” ya juya ya kalli Hussain da yake ta danne danne a wayarsa, yace “sosai ma, alhamdulillah is all we can say” tace “alhamdulillah. Sai shirin dawowa kenan ko? Kaga ni ina son mijina ya dawo fa” ta fada da shagwaba, ya sake dariya “ki sha kurumin ki yarinya, in nazo har sai kin gaji dani”. Suka jima suna hirar su, ko da wasa bata gaya masa taje unguwa ba, ta kara wa yaran wayar duk da basu san me take yi ba amma shi ya jiyo motsinsu kuma yaji dadi a ransa. Tabbas yaya rahama ne dan komai bacin ra sa ko zancen su yaji anyi sai yaji ransa yayi dadi. He can’t imagine zuciyar Hussain, bayan wannan ciwon kuma ga babu haihuwa yet.

Washegari ta tashi da gyaran dakinsa tunda taji yace sun kusa dawowa. Duk da dai ba wani datti dakin yayi ba dan fes ya tafi ya barshi kuma tunda ya tafi bata bude dakin ba. Ta dan karkade kura ta gyara abinda yake bukatar gyara sai ta bari da niyyar sai ana gobe zasu dawo sai ta kuma gyarawa ta wanke toilet. Anan taga system dinsa a kan study table dibsa tare da takardu, ita ta dauka da ita ya tafi dan haka bata lura ma da ita a gurin ba, sai kawai ta dauka ta hau kan gado ta bude ta fara dudduba abubuwan ciki, babu komai dan shi ko irin videos din nan ma ba ajjiyewa yake yi ba duk yawancin tarkacen kayan office ne, har tayi kamar zata rufe sai kuma zuciyarta ta raya mata cewa ta duba e-mail dinsa, maybe ta samu something interesting. Ta bude ta fara bin mails din briefly, suma duk tarkacen office ne dan ba ma gane me ake cewa take yi ba. Sai kuma idonta ya sauka akan wani “re_suspected Cancer patient” ta bude ta karanta, ta kuma karantawa tana so ta fahimta, ta dauko wayarta tana duba ma’anar wasu daga cikin kalmomin da akyi amfani dasu, sai da tayi wa e-mail din filla filla sannan ta fahimci cewa wani doctor ne a india ya rubuto yana gayyatar “Hussain Aminu Abdullahi” yaje za’a yi masa gajin cancer. Ta duba date din taga kwanaki kadan kafin tafiyar su, sai kuma taga wani email ne na Hassan wanda ya turawa doctor din akan yana son ganinsa amma kuma info din na Hussain ne.

Ta cigaba da bincike amma takasa samun wani abu da zai kara fahimtar da ita cikakken ma’anar abinda ta karanta din, Cancer, Hussain, India. Haka ta wuni da abin a ranta kuma can kasan zuciyarta tana jin wani excitement yana taso mata. Tana jin maanar abin tana kwanta mata a zuciyarta, Hussain yana fama da cutar cancer, wannan shine dalilin zuwansu India ba wai zazzabin da Hassan yayi ba. Yes, ta samu wannan information din amma me ya kamata tayi dashi? Ta yaya zata yi amfani dashi to her own advantage?

Sai dare sannan ta yanke shawara. Dakin Hassan ta koma ta samu wata newspaper ta zauna tana duba front page din a hankali har taga hotline dinsu, ta dauka a wayarta sannan ta sauka kasa ta aika a ka siyo mata sabon sim card, ta dawo dakinta ta zauna ta saka a wayarta sannan ta nemo waccan number din data yi saving ta tura message.

“Hussain Aminu Abdullahi, the CEO of H and H is suffering from cancer and currently receiving treatment in india”

sai ta rubuta address din asibitin data gane tare da email din ta tura. Sai data tabbatar ya tafi sannan ta zare sim card din ta balla shi ya jefar. Tayi murmushi yana jujjuya wayar a hannunta. “Let’s see how Fatima will react to this”.

**. **. *

Tun tafiyar su Hussain Fatima bata jin dadi, ji take gabaki daya kamar duniyar tayi mata zafi duk kuwa da cewa kullum suna makale a waya amma empty take jin duniyar ta. Wannan yasa ta roke shi akan zata je kano ta dan zauna kafin ya dawo, bai yi tunanin komai ba ya bar ta ta tafi saboda tunda akayi auren su bata taba zuwa ta zauna a gida ba, on few occasions ne yake barin ta tayi weekend kuma yasan tana missing gidan sosai duk da bata taba yi masa complain ba. Babu bata lokaci ta shirya ta tafi, sai ta dauki Khadijah suka tafi tare dan babu abinda take yi a gida a lokacin.

Satin ta daya a gida, kullum sai sunyi video call da Hussain sau uku kamar yadda yayi mata alkawari kuma hakan yana debe mata kewa sosai. Sai dai problem dinta daya shine yadda taga kamar yana ramewa, tayi complain sai yace mata ai kewarta ce take damun sa. “To ku dawo mana” ta fada kamar zata yi kuka “bana jin dadi da baka nan, kullum zuciya ta sai in ringa ji kamar wani abin yana faruwa wallahi, ga faduwar gaba, kuma duk dan baka nan ne” yace “ya zanyi in taho in bar Hassan baya bashi da lafiya? Kimga ai ban kyau ta ba ko? Gashi ciwon nasa kamar karuwa yake yi ni duk hankali na a tashe yake, an bamu wasu test da za’a yi da hotuna da za’a tabbatar da me yake damunsa” sai kuma taji babu dadi, kamar ba ta kyauta ba da take cewa Hussain ya bar dan uwansa ya dawo gurinta. Tace “to maybe ma damuwar hakan ce ta saka nake ganin kamar ka rame, ka daina damuwa sosai kaji Mi Amour? Zai samu sauki kaji?” Yace “insha Allah. Amma duk da haka a zamu dade ba nan gaba, in anyi test din zamu taho in results ya fito ma dawo” tace “noo, ku tsaya kawai a bashi kulawa sosai. In abun zai dauki lokaci sai in dauko Ruqayyah muntaho tare kawai, na tabbatar shima zai bukaci matarsa a kusa dashi” Hussain yace “yeah right. Nima kuma ina bukatar matata a kusa dani.”

A hankali take lura da yadda nayayin sa yake cigaba da kalacewa, kullum kuma sai tayi masa complain, hakan yasa ana gobe za’a yi masa aikin yace mata wayarsa ta lalace ba zata yi video call ba sai dai suyi voice. Wannan yasa ta sake tabbatarwa da cewa something is definitely wrong, tasan cewa karya yake yi mata amma sai ta kasa karyata shi din. Babu yadda za’ayi Hussain ya zauna da lalatacciyar waya, wayar da bata yi komai bama Hussain yana chanjata zuwa sabuwar yayi ballantana ace wayar da tayi lalacewar da zata hana shi ganin ta? He is definitely hiding something.

Wannan yasa ta tattara ta dauki Khadijah suka koma Kaduna, ta samu Aunty ta zayyana mata abinda suka yi da Hussain ita ma kuma auntyn ta tabbatar da maganar Fatima sai dai sun kasa gane dalilinsa na yin hakan, sai Aunty kawai ta bawa Fatima shawarar su yi ta addua, dan Hussain ba mutum ne mai boye boye ba tunda har ya boye to abu ne mai muhimmanci a gurinsa, ta tabbatar duk abinda yake boyewa in ya dawo a hankali zasu sani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button