TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Hassan ya jinjina maganar Hussain a ransa, to ko dai ya bawa Baba gidan nan ne yanzu? Yana tunanin rikicin da zasu yi akan gidan kafin ya karba amma kuma sai ya yanke wata shawara. A iya kacin saninsa da Baba yasan babu abinda yake so sama da iyalinsa, dan haka dasu zaiyi amfani. Ya gama shirinsa tsaf sannan ya yiwa Ruqayyah waya “hello sweetie. Ya gida” ta gyara kwanciyarta tace “lafiya kalau. Ya office?” Yace “na dawo ai tun dazu. Baba yana gida kuwa?” Tace “eh, ya dawo” yace “Okay, ko zaku tambayeshi dake da Sumayya da su Zunnur ku shirya zan zo in dauke ku mu tafi unguwa” ta mike zaune daga kwanciyar da take tace “ina zamu je?” Yayi murmushi “it is going to be a surprise” tace “ina ne dan Allah” yace “to in na gaya miki kuma ai bai zama surprise din ba kenan”

Tayi rolling idonta cikin takaici, ita bata taba ganin mai zurfin ciki irin Hassan ba, baya taba gaya mata komai, shi hirar sa kawai ta kalaman soyayya ce wanda dasu da kuma kwarjinin sa yake amfani gurin kashe mata baki ta kasa challenging dinsa, amma sam bata jin dadin yadda alakar su take tafiya, sam bata jin dadin abubuwan da take fahimta a tare dashi sai dai ba zata yi magana, ko da zata iya challenging din nasa ma ba zata yi ba saboda kar ya fahimci true color dinta yace ya fasa. Target dinta daya shine a daura auren dai, in ta riga ta shiga gidan sa a matsayin matarsa kuma ai shikenan tana da control over duk wani abu da yake nasa.

Ta tashi ta fita tsakar gida in da sauran yan gidan suke, Baba ya a magana “Zunnur in na dauki albashin wannan watan keke zan siya maka. Saboda ka rage wahalar zuwa makaranta” Zunnur ya tashi da murna yan uwansa suna taya shi, Ruqayyah ta tabe baki, su keke manya.

Ta durkusa a gaban Baba “Baba dama Hassan ne yayo waya yace mu shirya ni da sauran yara zai zo ya dauke mu zamu je unguwa” Baba ya bata fuska “unguwa kuma? Wacce unguwa?” Ta tabe Baki “nima bai gaya min ba fa, ya dai ce wai wani mamaki zai bamu. Ba zai wuce shopping ne zai kai mu ba” a ranta ta karasa da cewa “it is about time daya kamata ya bude wannan matsatstsen aljihun nasa”

Baba yayi shiru bai ce komai ba, Inna Ade tace “tunda da sauran yara zasu je ai ina ganin babu komai ko Baban biyu? Kaga bikin ya fara matsowa sosai yanzu haka wani abu ne daya shafi bikin nasu” Sumayya cikin doki tace “baba mu shirya, yanzu haka gidan da zasu zauna zai kai mu mu gani” Inna Ade tace “haka ne kuwa, shi din nema yanzu haka” Baba yace “sai ku tashi ku shirya ai, ku bi a hankali, banda rawar kai banda kwadayi”.

Ai kuwa cikin murna suka mike da sauri suka shirya, su Ruqayyah suka yi dressing daga cikin sababbin kayan su suka yi wa juna kwalliy mai kyau, sunyi kuma matukar kyau da yanayin su mai daukan hankali. Sun gama shiryawa kenan Hassan yayo waya cewa gashi nan ya kara so, suka yi wa Inna sallama suka fita tana yi musu fatan alkhairi.

Suna fita ya bude musu mota suka shiga. Ruqayyah ta zauna a gaba kusa dashi su kuma duk suka shiga baya suna hada baƙi gurin gaishe shi. Ya amsa musu individually kowa yana tambayarshi makaranta, sai da suka nutsu suna kus kus a tsakanin su suna santin motar sannan ya juya side din Ruqayyah yace “ranki ya dade” tayi murmushi tana sunkuyar da kanta tace “tare da naka” daga nan bata kuma cewa komai ba, hankalin ta yana kan titinan da suke bi tana lissafin wanne mall zasu je, wanne nema wanda yake tashe yanzu?

Sama sama Hassan yaje hira da kannen Ruqayyah, lokaci zuwa lokaci kuma yana juyo wa ya kalle ta yayi mata murmushi itama ta mayar masa, shi shirun ta da nutsuwarta suna burge shi sosai, wannan yana nuna cewa bata da hayaniya kamar yadda yake so sannan kuma bata da mita.

A kofar gidan ya tsaya, duk suka juya suna kallon gidan with different thought a zuciyoyin su.
Ruqayyah “wait! What? Ba dai nanne gidan da zamu zauna din ba”
Sumayya “kai!!!, Ji wani gida mai kyau”
Sulaiman “duk sanda na tashi yin gidana irin wannan kofar zan saka”
Zunnur “me muke yi anan?”

Hassan ya bude motar yana cewa “okay, we are here, kowa ya fito” suka fara fitowa daya bayan daya duk idon su akan gidan, Ruqayyah trying so hard not to scream. Ya dauko key ya bude gidan fuskarsa cike da farin ciki yace “ku shigo, kowa ya zagaya ya gaya min view dinsa akan gidan nan”.

Ruqayyah a tsakar gida ta tsaya tana jin kamar kafafuwanta ba zasu iya kaita double door din da taga sun shiga ba, sai da Sumayya ta dawo da sauri ta ja hannun ta. “Zo ki gani, Ruqayyah, har furnitures an saka” Ruqayyah bata ce komai ba ta dai bita a baya kirjinta yana bugawa.

Ɗakunan guda uku duk an saka musu set din gado masu kyau da labulaye, falon ma an saka set din kujeru irin wadanda ita kanta Ruqayyah ta san cewa bata taba hawa irin wannan kujerar ba amma duk da haka ji tayi sam basu yi mata ba, sam basu dace da ceo na H and H ba. Ga set din kayan kallo, plasma tv ce amma Ruqayyah a idonta sai taga it is not big enough, ita katuwa ta ke so.

Hassan sai murmushi yake yi yadda yaga yaran suna zagaya gidan cikin murna, ko bai tambaya ba yasan cewa gidan yayi musu. Yaga Ruqayyah a tsaye a falo tana daddanna wayarta sai ya saka hannu ya karbe wayar yana cewa “I am here, ba sai kin kalli hotuna na ba” ta dan yi murmushi tace “to ai baka tsaya na kalle ka ba, kana ta zagaye” yace “ke ma ba sai ki zo muyi zagayen ba?”

Tace “bana jin dadi ne, kafafuwana suke ciwo” taga yanayinsa ya chanja, ya durkusa a gabanta yana kallon kafafuwanta da suke sanye da takalmi tace “subhanallah. Wacce ce daga ciki take yin ciwon?” ta kara jan skirt dinta kasa tana kuma rufe kafafuwanta tace “ba nan bane ai yake ciwon” ya dago kai yana kallon ta yace “ina ne yake ciwon?” Ta juya masa baya tana jin zuciyarta tana zafi, kamar zata yi kuka take ji.

A lokacin ne su Sumayya suka fito daga dakin da suka shiga na karshe, suka dawo palo, Zunnur yace “kai! Wannan tv da girma take, zata yi dadin kallon ball” Hassan yayi dariya yace “you like it?” Duk suka amsa da yes banda Ruqayyah data juya musu baya tana kokarin rike hawayen ta. Sumayya tace masa “nan ne gidan ka? Anan zaku zauna da Rukee?” Yace “yaya Ruqayyah, yaya Ruqayyah zaki ke ce mata ba Rukee ba, and no, ba gida na bane ba kuma ba anan zamu zauna ba” Ruqayyah ta juyo tana jin kamar an yaye mata wani abu a kirjinta. Yace ” wannan sabon gidan ku ne dana siya muku , nan nake so ku dawo tare da Baba da Inna ku cigaba da rayuwar ku anan”.

Yaran suka dauki sowa gaba ki daya, Ruqayyah ma ta rufe bakinta tana dariya, wannan ce dariya ta farko data yi tunda suka shigo gidan, Hassan yace da samarin “ga naku dakin can a soro, akwai tvn ku a ciki da zaku yi ta kallon ku a ciki. Ku zo muje in nuna muku” suka bishi a baya da sauri suna hada hanya.

Sai a lokacin Sumayya ta zagaya da Ruqayyah ta ga gidan, sai a lokacin taga kayan sunyi mata kyau amma da duk dusu dusu ta gan su. Sai a lokacin ta lura da cewa toilets din modern ne. Suka fito suka yi joining sauran a dakin soro inda aka yi masa tsarin samari da toilet dinsu. Sai da suka gama sannan suka fito, ya rufe gidan suka shiga mota suka juya suna barin gurin. Ruqayyah ta juya tana kallon gidan, sai taga baiyi mata kama da gidan su matar mamallakin H and H ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button