TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana komawa gida ta tarar da Sumayya a zaune a daki ita kadai, daga ganin fuskarta tasan akwai problem, tace “ke kuma fa? Lafiya?” Sumayya ta dauko farar envelope ta miko mata tace “wannan kudin na gani a cikin rigar ki, kudin menene” Ruqayyah ta bata rai tana miko hannu tace “kudi nane, bani abina? Sumayya tace “a ina kika same su? Yaushe aka baki su” Ruqayyah tace “a cikin kayan nan aka sako su, inna tana gani nasan Baba zata bawa ninkuma ina bukatar su shi yasa na boye” Sumayya taji ranta ya kuma baci tace “tun yanzu? Tun yanzu Ruqayyah har zaki fara boye abin duniya dan kar family dinki su mora, nan gaba me zai faru kenan?” Ruqayyah ta warce kudin tace “ai na bayar da wancan, wannan kuma ina bukatar sa kuma bazan bayar ba” Sumayya tace “kin duba kinga yawan kudin nan kuwa? Na tabbatar kudin sun isa ayi katangar gidan nan dasu, kinga ai kema in Hassan yazo ba zaki ji kunya gidan ku babu katangar arziki ba” Ruqayyah ta daga kafada tace “a haka ya ganni, a haka kuma yace yana sona. In baya son gani gidan nan ya gina mana wani”.

A ranar bayan Baba ya dawo gida Sumayya ta dauki wayarta ta kai masa “Baba ga wannan, ni babu abinda zanyi da ita kuma naga kamar zata yi tsada sosai, a siyar da ita mu gani ko kudin zai isa ayi katangar gidan nan” Baba ya karbi wayar yana jujjuya ta sannan yace “Nagode sosai Hussaina. Allah yayi miki albarka”.

Kwana biyu bayan nan Hassan ya zo gurin Ruqayyah zance, sai yayi mata bayanin cewa a karshen satin nan suke saka ran zuwa Gombe gabaki dayansu shi da yan’uwansa, idan kuma sunje zai shigar da maganar auren su dan azo a nema masa.

Ruqayyah murna kamar tayi rawa amma ta maze tace “da wuri haka? Da ka bari ai an dan kara kwana biyu mun kara fahimtar juna ko?” Yace “menene baki fahimta nawa ba in fahimtar dake yanzu? Ni dai a bangare na babu wani abu da nake ganin ya kamata in kara sani, abinda na sani ya gamsar dani sosai”

Kamar ranar nan, suna yin sallama tana shiga gida sai ga Adam a tashi motar yayi packing a kusa da Hassan. Hassan ya gane motar, Adam kuma ya gane Ruqayyah duk da bai ga fuskarta ba, a ransa yace “ta tabbata zance yake zuwa” ya fito kamar ranar nan suka gaisa da Hassan sai yace “ashe zance kake zuwa gidan nan? Gurin Ruqayyah” Hassan ya rungume hannunsa a kirjinsa yana studying yaron gabansa yace “kai kuma zance kake zuwa gurin Sumayya” Adam yayi dariya “noo, ba zance nake zuwa, na shigo ta nan layin ne kawai dan maybe in samu in ganta, but in na aika ba lallai ma a barta ta fito ba dan ranar nan ma da kyar aka barta ta fito” Hassan yace “and you want to see her?” Adam yace “yes, I do. I really do. But I guess babu bahaushe Musulmin da zai bar yarsa take kulani ko”.

Hassan yace “no, no, no. Kar kace haka. Babansu yana da kirki sosai. In baka shawara? Kayi kokari ka ganshi ka gaya masa abinda yake ranka, bana jin zai ki amincewa. Ina iyayenka?” Yace “basa nan” sai ya dauke kansa gefe, Hassan yace “a ina kake da zama” yace “daki nake renting, ni da friend dina” Hassan yace “school fa?” Adam yace “na gama secondary, zan cigaba in na tara kudin”.

Hassan ya dauko wayarsa ya kira layin Ruqayyah. “Sorry na danyi mantuwa. Turo min Sumayya Please” sai ya kashe ya mayar da ita aljihu yace “gata nan fitowa, you can see her” Adam yayi murmushi, Hassan yana lura da yadda yaji dadi sosai.

Ruqayyah ta ajiye wayar tana cewa “yes! Sumayya kije waje Hassan yana kiranki, sako zaki karbo min” Sumayya bata ce komai ba ta dauki hijab dinta ta fito, har yanzu haushin yaruwarta take ji na hana babansu kudi duk da tasan yana bukatar su.

Tana fitowa taga Adam a tsaye tare da Hassan, take taji bakin cikin ta ya yaye farin ciki ya maye gurbin sa, ta rufe baki tana dariya, shima dariyar yake yi yana tahowa inda take. Sai Hassan yaga sun bashi sha’awa sosai, Sumayya tace “Adam? You are here” yace “yes am here, na shigo layin, hoping to see you sai wannan bawan Allah ya taimake ni ya kira min ke. Da fatan ranar nan ba’a yi miki fada ba” tace “no, ai cewa tayi kar in dade kuma ban dade ba”

Ta juya tana kallon Hassan tace “ina yini” yace “hmmm. Sai yanzu kika ganni? Ai ni har nayi fushi” ta karaso tana cewa “ayi hakuri babban yaya, ya zanyi in kasa ganinka bayan gaka a gabana?” Yace “na sani ko wani ya rufe miki ganin ki?” Ta danji kunya kadan tace “haba dai”.

Ya danyi murmushi sai ya dauko complimentary card dinsa ya mika wa Adam yace “come to my office duk sanda ka samu dama, I might get something for you” ya karbi katin yana kallon sunan sai yayi dariya yana rike baki, ya juya kamar wanda zai rungume Sumayya sai kuma ya rungume hannunsa, yace “thank you sir, thank you so much. Amma bani da credentials din da zaka bani aiki dasu”

Hassan yace “I am already getting an idea na aikin da zan baka, ba ka iya driving ba?” Adam ya kalli motarsa yace “sosai ma kuwa” Hassan yace “hmmmm, then maybe it is about time da ya kamata Hussain ya samu personal driver. Yana dawowa daga wannan tafiyar zan zuga shi ince bai kamata dangoten Kaduna yake driving kansa a mota ba, he will like you, tunda naga kana da tsafta da gayu, a matsayin drivern Hussain zaka sami daki a gidan mu, zaka ke samun abinci kaga baka da wannan matsalar, Hussain ba mazauni bane ba, dan haka you will have alot of hutu im baya nan, in yana nan ma am sure sometimes mantawa zai ke yi da kai. Motar ka sai ka vayar ana yi maka haya ana kawo ma ka balance, that, plus albashinka and all the goodies da za kake samu daga gurin Hussain zai ishe ka kayi sponsoring karatun ka”

Adam daya kasa rufe baki ya juya ya kalli Sumayya ita ma da take ta murmushi yace “sai in biya mana makaranta ni da Sumayya mu tafi tare” Hassan ya gyada kai yace “I like you, I really like you”.Sixteen : The Houses

Bayan Hassan ya tafi Sumayya tace wa Adam “ka je fa ka same shi din, yana da kirki sosai” yace “zan je, gobe weekend amma ranar Monday first thing in the morning zanje in same shi” ya sake jujjuya card din a hannunsa yace “H & H fa” tace “yes, tashi ce” yace “to who is Hussain?” Tace “dan gayun brother dinsa” suka yi dariya gaba ki daya.

Yace “yanzu in zan iya biya mana school tare, Baba zai barki ki je?” Tace “it is so nice of you to say that Adam. But bana jin Baba zai yarda ka ce zaka boya min. Shima yana da burin ya biya mana muyi karatu sannan kuma Baba mutum ne da bai fiya son ayi masa abu ba, yafi son komai yayi da kansa in dai zai iya” yace “Ruqayyah fa? Ita ma zata yi karatun? Naga…..” Ya nuna inda Hassan ya tsaya, ta dan bata rai tace “tare muke da niyyar zuwa, but yanzu all of a sudden Hassan yazo da maganar aure kuma nasan ba zai jira ta gama makaranta ba, to gaskiya ban sani ba ko zai barta bayan aure ta cigaba da karatu”

Adam yace “yanzu misali, just for example, idan….. Idan na aure ki nima, kinga ai ni zan biya miki karatu ko?” Tayi dariya, “Adam kenan, aure fa kace” ya dan hade rai “aure fa, ko ba zaki auri Igbo ba” ta dago kai tana kallonsa, ita dai tun ganinsa na farko ta san ba Bahaushe bane ba amma bata iya tayi placing yarensa ba. Kuma bata tantance ko musulmi ne ko akasin haka ba. To yanzu gashi ya fada mata, Igbo. Akwai kabilar da suka fi Igbo samun sabani da hausawa kuwa?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button