TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Adam ya ciko mota passengers yana tukin sa a nutse kamar kullum, yaji vibration din yawarsa da take ajjiye akan dash board, ya kalle ta, sunan daya gani ne ya saka shi daga kafarsa yana kara rage gudun motar sannan ya sauka gefen titi yayi packing yana cewa “excuse me Please, I have to answer this” sannan ya daga wayar da sallama.

Hassan yayi mamakin sallamar da yaji amma sai ya maze yace “kazo gobe, around noon ina son ganinka” Adam yace “yes sir. Insha Allah” Hassan ya katse wayar still yana noticing insha Allah din da Adam yace.

A ranar da daddare Hassan yaje zance gurin Ruqayyah, suna zaune a dakin su Sulaiman kamar yadda suke zama kullum. Tana ta so ta shigar masa da maganar shirin biki amma ta rasa ta yadda zata fara ba tare data bata pentin da tayi wa kanta a gurin sa ba. Sumayya ta shigo da sallama ta zauna a hannun kujerar da Ruqayyah take zaune, ta gaishe da Hassan ya amsa yana tsokanar ta. “Ance min kina ta kuka wai ba kya son rabuwa da friends dinki” tayi ajjiyar zuciya, ita duk ba wannan ne problem dinta ba, ba shine abinda yake hana ta bacci tunda suka dawo ba.

Tace “yaya Hassan, dama tambayarka zanyi…….” Ya gyara zama yace “ina jinki” tace “yaje kuwa? Yaje office din naka kuwa?” Ruqayyah ta juyo tana kallon ta tace “wa? Waye zaije gurinsa?” Sumayya ta dauke kanta daga kallon ta ta sake mayarwa kansa tana jiran amsa, ya danyi murmushi duk da ya fahimci wa da take nufi amma sai yace “wa kenan fa?” Ta dan vata fuska tace “mutumin ranar nan” ko da wasa bata son Ruqayyah ta san maganar Adam.

Ruqayyah ta sake cewa “wai waye kike magana akan sa? Bashi da suna ne?” Sumayya tace “shi yasan maganar wanda nake yi ai” Hassan yayi yar dariya, ya fahimci Sumayya tana boyewa Ruqayyah wannan Igbon. Ya gyara zama da dariya a Muryar sa yace “yes, na gane wanda kike nufi, and yes, yaje munyi magan dashi” cikin zakuwa Sumayya tace “and?” Yace “and, sai gobe zai dawo mu karasa maganar” Sumayya tayi ajjiyar zuciya tace “okay, thank you. At least nasan yaje din, ina ta tunani ne kuma bani da hanyar sani shi yasa na tambaya” yace “kar ki damu. I have his phone number if you want” Sumayya tayi saurin miko wayarta da Baba ya dawo mata da ita bayan sun dawo sabon gidan tace “yauwa saka min Please” yana dariya yace “ko kunya babu” ya karba yana saka mata Ruqayyah tayi mata alamar tambaya da hannunta ita kuma sai ta dauke kai kamar bata gane me take nufi ba, ta san dai yau sai sunyi rigima a daki”.

Yana gama sakawa ya miko mata, tayi saving sannan tayi masa godiya ta fita, Ruqayyah ta jiyo tana kallon sa da alamar tambaya sai yace mata “wani aboki na ne”. Daga nan bata iya ce masa komai ba duk da bata yadda da amsar daya bata ba.

Sumayya direct dakin da yake matsayin nasu ita da Ruqayyah ta zarce, ta rufe kofa sannan ta zauna a bakin dago ta kira number din da aka saka mata. Ring biyu ya dauka da sallama kuma a take ta gane muryarsa. Yace “who is on the line please” sai data dan jima sannan tace “someone, da ka manta” ko a cikin mafarki ne zai gane muryarta. Ya matsa daga gurin da abokan su suke hira yana cewa “Sumayya? Ke ce da gaske? A ina kika samu number ta?” Bata bashi amsa ba sai kuma yake “ohhh I get it. Yazo zance…..” Ya fada da dariya a muryarsa.

Ta dan bata fuska tace “ni da na damu da inji yadda kake ai na ajiye kunya ta a gefe na nemi number dinka” yace “oh dear , you have no idea sau nawa nake zuwa unguwarku a rana. Sumayya kullum sai naje, kawai dai na kasa samun courage din da zan aika a kira ki tunda ranar nan kince min za’a yi miki fada, bana so ayi miki fada, bana so in jawo miki trouble. In naje kawai hoping nake ko zan ganki an aike ki ko kin fito unguwa”

Ta lumshe idonta tace “ni ba’a aike na, ni babu inda nake zuwa, sai in kwana biyu ban fita daga gida ba, dama zuwa school ne kuma yanzu bama zuwa, islamiyya ma a gida muke yi anan muke daukan karatu kuma mu dora wa yaran unguwa karatu” yace “wow, har karatu kuke koyarwa?” Tace “gidan mu ai makaranta ce, makarantar addini ce” sai taji yayi shiru har sai da tace “hello?” A hankali yace “zan iya shiga nima? Makarantar gidan ku zan iya shiga?” Tace “ban gane ba, ba ka yi sauka ba ko akwai littattafan da kake son sani?” Sai da ya danyi shiru sannan yace “banyi karatu ba ni. Bani da ilimin addini ni”

Overlook the typos please.

Wannan littafin na siyarwa ne, in kina so kiyi min magana ta wannan layin. 08067081020
Nineteen: The Real Princess

An kusa zuwa dai dai gurin. Lol

Jin tayi shiru bata ce komai ba ya saka yayi saurin chanza topic din. “Ina son ganinki sosai Sumayya, amma ban san yadda za’a yi in ganki ba. Ko kina da shawara?” Ta girgiza kanta tana kokarin kawar da shock din waccan maganar tace “bama gidan da ka sani yanzu mun tashi” ya ce “what? Kina nufin duk zaryar dana ringa yi da karawa wuyana tsaho ko zan hango ki a banza nayi ta kenan?” Tayi dariya shima yayi sannan tace “mun tashi daga unguwar” yace “to ina kuka koma?” Tace “naji Hassan yace gobe zaku hadu dashi, ka tambaye shi sai ya baka full address din, ni am not familiar with unguwar har yanzu dan haka ba zan iya yi maka kwatance ba” yace “wannan mutumin? A gurinku ne fa ku yammata yake sakin fuska har da dariya. Da naje office dinsa har na fito banga hakorinsa ba” Sumayya ta sake dariya tace “haba dai, yana da kirki fa sosai. Shi ya siya mana sabon gidan nan da muka dawo” Adam ya taya ta murna sannan ya bata labarin yadda suka yi da Hassan a office dinsa ranar nan, sannan ya kara da cewa “yace gobe inje in same shi. Maybe ya gama binciken nasa ne zan je inji result. Pray for me please”

Tayi masa alkawarin addu’a da kuma fatan alkhairi, a ransa yana so ya tambaye ta game da hadin Ruqayyah da Hassan da har zai siya musu gida amma sai yaji kamar yin haka zai zama stepping on the boundary tunda dai ba abinda ya shafe shi bane ba. Sun jima suna hira, yana ta bata labarin yadda yake zuwa unguwar su nemanta baya ganinta. Tana ta yi masa dariya yace “ni ko? Zan rama ne. Dadinta ma kema gashi kin kasa hakuri kin nemi number ta kin kira ni. But Wait, wai layin kine wannan?” Tace “oho maka. Tunda gori zakayi min” yace “to ko ba layin ki bane ba kiyi wa mai layin albishir cewa baccin sa is now limited, dan zanyi ta kira ne ba kakkautawa” sun jima suna hirar su freely like old friends, har sai da ta ji alamar shigowar Ruqayyah palo sannan tayi masa sallama ta kashe wayar, amma ta kasa cire murmushi daga fuskarta.

Ruqayyah ta shigo tana binta da kallo, sannan ta kalli wayar tace “sai yanzu kika gama wayar? Tun dazu wayar kike yi” Sumayya tace “a tambayo” tace “wa za’a tambaya? Ke nake tambaya ai” Sumayya tace “shi bai gaya miki number din waye ya bani ba?” Ruqayyah ta zauna tana cewa “ina zai gaya min? Shi bayan maqon kudi ma har maqon magana yake yi. Kwaji dashi daga ke har shi, shi ce min yayi wai wani abokin sa ne ni kuwa nasan ya za’a yi ni bansan kowa a abokan sa ba amma ke ki sani har kuke exchanging numbers” Sumayya bata kula ta ba ta fara chanja kayan ta zuwa na bacci, sai data gama sannan ta zauna a bakin gado tace da Sumayya “Sumayya so nake in ya sake dawowa jibi ki je gurin sa dan Allah kuyi maganar bikin nan, ni bansan me yake shirya wa ba kuma kinga lokaci yana ta kurewa. So nake ya bayar da kudin da za’a siyawa kawayen mu anko kowa a kai mata ba wai ace mutum ya siya ba, nima kuma ya bani kudin kayan fitar biki. Sannan kuyi maganar events din da za’ayi, da event centers din da za’a kama tunda kinga gidan nan ba zai isa ba. Ku dai yi maganar sosai Sumayya ni na kasa yi masa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button