TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Hassan yana ta fama da tarin kudin siyan kayan babies yana lissafin nawa ne zasu isa nawa ne ba zasu isa ba sai gashi rana daya Hussain da Fatima sunyi wata tafiya suka dawo musu da komai da ake bukata na haihuwa. Komai da komai, tun daga kan crib har kan diaper kuma komai na twins. And knowing the Hussain we know, komai na zamani ya siya kuma komai mai tsada. Rashin sanin gender ya saka suka siyo gender neutral, suna dawowa aka shiryawa babies din nursery dinsu a kasa using grey color da theme na forest. Duk rashin godiyar Ruqayyah sai da tasan cewa sun kyautata musu dan dakin babies dinta ko a films ita dai bata ga irin sa ba, hatta nata kaya bukatun na haihuwa an siyo mata, sannan Hussain yace Fatima ta tambayeta in akwai wani abu kuma daban da take bukata ta fada ayi mata. Sai kuma yayi suggesting in watan haihuwarta yayi a fita da ita waje ta gaihu a can dan tafi samun medical care mai kyau.

Tashin farko Hassan yace a’a “idan masu kudi suna fitar da matan su waje in zasu haihu ka gaya min ta yadda za’a gyara asibitocin kasar nan” Hussain yace “ohhh. Takan matarka za’a fara misali kenan? Sai ka bari idan matar president ta haihu a Nigeria sai kaima taka ta haihu a nan, at least sai in san footsteps din shugabanni kake bi” Hassan yace “ni ban damu da shugabanni ba fa, ni kaina na sani and I know that I can make a difference. Idan da kowa a Nigeria zai saka a ransa cewa zaiyi making a difference, zaiyi setting good example, dana tabbatar abubuwa zasu yi mana sauki a kasar nan” Hussain yace “to Allah ya bada saa good samaritan, ni dai duk ranar da matata zata haihu to sai na samu asibitin da yake one of the best a duniya sannan zan kaita ta haihu” Hassan yace “a dawo lafiya, mu muna nan kuma in dai an haihu lafiya din ai shine abinda ake nema”

Duk da cewa a tare take da Aunty, ga kuma yaran da suke gidan ta amma da watan haihuwar yazo sai da Hassan ya roki Baba akan cewa Sumayya ta dawo gidan su da zama saboda ba’a san sanda haihuwar zata zo ba. Allah yasa su Sumayya suna hutun semester dan haka ta taho din dan itama tana son ayi komai a gabanta da inda hali ita mai iya karbar wa yar uwarta wani part na ciwon haihuwar ne. Tare suke wuni da rana, da dare kuma Ruqayyah ta tafi gurin mijinta su kwana tare, wanda duk juyi sai ya tambaye ta ko akwai abinda take buƙata. Da ranar ma kuma haka Sumayya take lallabata tana koya mata irin abubuwan da take koyo a makaranta da kuma abubuwan da suke haduwa suyi browsing tare da al’amuran da suka shafi ciki, haihuwa da kuma prenatal. Suka yi installing wani application mai suna Baby Center wanda yake taimakawa masu juna biyu sosai gurin tracking cikin su sunan kowanne stage da kuma abinda ya kamata suyi expecting a stage din, akwai tips na abubuwan da zasu kara wa mai ciki lafiya da kuma abinda ya kamata ta guda wadanda zasu iya harming dinta ko abinda yake cikin ta. Sannan kuma akwai signs and symptoms na labour, yadda mace zata banbance true labor da false labor, yadda zata ke timing contractions dinta dan tasan how far along in labor take da kuma yadda zata ke counting baby kicks dan ta tabbatar da lafiyar abinda yake cikinta. (Try using it in kina da ciki, am sure zaki ji dadin app din)

Sanda Sumayya take yi mata wannan bayanin sai Ruqayyah ta tabe baki tace “they are always kicking, bana jin ina bukatar wannan”. Wannan ilimin data samu ya saka laborn yana zuwa ta fahimci shine, anan ne kuma hankalin ta ya fara tashi tana jin tsoron wahalar haihuwar amma kuma bata jin tsoron mutuwa “in na mutu a haihuwa nayi mutuwar shahada kenan”

Tun safe ta fara, ita da Sumayya suna ta timing contractions din suna son sai ciwon ya fara zuwa kurkusa sannan zasu fada wa Aunty, dan haka wajen azahar Sumayya ta kira Aunty ta gaya mata, ai kuwa sai gata da kanta tazo, tana ganin yadda Hassana already ta fara shan wahala sai ta kamata da kanta ta saka ta a mota, Sumayya ta debo kayan da suka hada a jaka na zuwa asibiti suka tafi, dama Hussain da Fatima basa kasar a lokacin. Duk sun dauka ba zasu dade a can din ba Ruqayyah zata haihu amma sai gasu har magrib, dole suka kira Hassan suka gaya masa dan kar yaje gida ya tarar basa nan, amma duk da haka aunty tace kar a gaya wa Inna saboda kar hankalin ta ya tashi gwara a bari sai ta haihu tukunna a kira ayi musu albishir.

Karfe goma sha biyu na dare Ruqayyah ta haifi santalelen jaririnta namiji, bayan ta leka lahira ta dawo, karfe daya na dare kuma ta haifi na biyu, shima namiji, dukkanin su masu kama da baban su da yake tsaye a bakin kofa cikin dimuwa yana jira.

Sorry for the typos

Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kina son ki karanta halaliyar ki ki neme ni through WhatsApp ta wannan number din 08067081020Unveiled

Bakin Aunty har kunnen ta saboda murna, aka miko mata na biyun ma ta hada dana farkon ta rungume a jikinta tana jin hawayen dadi yana taruwa a idonta, ganin jariran sai ya tuna mata da ranar da aka haifi Hassan da Hussain, sai ta tuno da yar uwarta, take taji son yaran ya shiga ranta kamar yadda taji tana son Hassan da Hussain lokacin da aka haife su. Ta juya tana kallon Ruqayyah wadda take ta mazar kwalla ana yi mata dinki, tabbas ta jinjina wa kokarin yarinyar yadda ta haifi yan biyu da kanta duk da karancin shekarun ta. Sai dai fa tabbas ita kanta auntyn ta san ta sha wahala ba kadan ba. Duk da azabar da take sha amma bai hana ta tambayar Aunty ba “aunty me na haifa?” Aunty ta shafa kanta tana murmushi tace “duk maza ne Ruqayyah”

Ruqayyah ta sauke ajjiyar zuciya, deep down tana jin dadi saboda hakan yana nufin sauran maganar mai duban nan itama gaskiya ce, zata yi kudi fiye da wanda take saka rai. And she just can’t wait. Ko ma menene option din tasan zata yi decision mai kyau wanda zai amfane ta ya amfani ahlinta baki daya, ya amfani twins dinta.

Ta fita da yaran a hannunta zuwa waiting room inda Hassan yake ta faman safa da marwa dan kunyar Aunty ce kawai ta hana shi shiga ayi labor din tare dashi. Yana ganin ta da yaran ya tafi gurin ta da sauri yana mika hannu sai kuma ya janye hannun yana murmushi, tayi dariya “karbi abinka, ai kayi kokari, da wancan marar kunyar ne da har ciki zai bini yace in fito in basu guri” yayi murmushi yana mika hannayensa duk biyun ita kuma ta saka masa yaran a kowanne side, ba zai iya misalta farin cikin da zuciyarsa take ciki a lokacin ba, ba zai iya misalta soyayyar yaran da yaji a cikin zuciyarsa ba tun daya dora idanuwan sa akan su. Sumayya ta leko da kanta ta gefensa tana kallon babies din tana murmushi, hannunta yana yi mata kaikayi tana so ta dauke su, ta miko hannu amma sai ya maze yayi kamar bai ganta ba. Dole ta hakura ta cigaba da leken su ta gefensa. Ya dago kai yana kallonta yace “suna da kyau ko?” Ta gyada kai da sauri tace “suna da kyau sosai ma. Kama suke yi da kai” ya girgiza kansa yace “no, da Hussain suke kama” tayi dariya, “da Hussain da kai ai duk kamar ku daya” shima sai yayi dariya yace “da yana nan da kunyi fada yanzu, zai ce ya fini kyau ai” ita ma tayi dariya tana shafa hannun daya daga cikin babies din, sai kuma ya bata daya ya zauna da dayan a hannunsa yana yi masa kiran sallah a kunnuwan sa. Ya gama ya miko mata shi ya karbi na hannun nata shima yayi masa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button