TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan anyi duk abubuwan da akeyi na al’ada cikin barkwanci da wasa da dariya tsakanin bangarorin biyu sai aka bayar da Ruqayyah Aunty ta rungumo ta ta fito da ita ta saka ta a motar da tazo a cikinta ita da hajiyan kano da gwoggo Habibah sauran motocin da suka zo daukan yan uwan amarya suka mara musu baya.

Sumayya ta tambayi inna ta hada yan kayanta a karamar jaka, tana so zata raka Ruqayyah kano, so take sai an gama bikin gaba-daya sannan zata dawo gida. Tun da ta fito kofar gidan ta samu gefe daya ta tsaya hannunta rike da jakarta tana ta sharar hawayen ta tana bin mutanen da suke ta turereniyar shiga motoci da kallo, sai kuma taji tana jin haushin kanta na damuwar da tayi, ita me auren ma ko a jikinta dan ko digon kwalla bata gani a idanuwan ta ba amma ita har nata idanuwan sun kumbura saboda kuka.

Tana tsaye taji mutum a kusa da ita, ta gefen idonta ta gane namiji ne dan haka ta yi saurin juyowa side dinsa a tsorace, ya jefe ta da best smile dinsa, ta ji half of damuwarta ta tafi amma sai ta kara bata rai “har da kai aka zo za’a dauke min yar uwa ta ko Adam?” Yayi dariya “mu menene laifin mu? Gidan miji fa zamu kaita, at least ai yanzu zata daina runton kudin mota” Sumayya ta harare shi “be careful, matar ogan ka ce dai yanzu, or else you get fired” ya saka hannu ya kama bakinsa ya ce nayi shiru, ba zan kara cewa komai ba” Sumayya ta nuna shi tace “you better, kasan Hassan baya wasa da yara” yace “yeah, ba sai kin tuna min ba na sani, Hussain ne mai wasa da dariya, dadinta kuma shi na ke yiwa aiki ba Hassan ba” tace “amma Hassan din ne ya dauke ka aikin kuma he can fire you” yace “to mai mijin sister, naji, can we go now” yayi kasa kasa da murya yace “daga ni sai ke, na boye motar da nazo da ita” ya kashe mata ido.

Yayi gaba, da kamar ba zata bishi ba sai kuma ta juya tana waige waige sai data tabbatar babu wanda hankalin sa yake kanta sannan ta bishi inda taga yayi, tana zuwa ya zagayo ya bude mata kofar front seat ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga gurin driver ya tayar da motar. Sai kuma ta juyo tana kallonsa da budaddun idanunta tace “gidan amaryar zaka kaini ai ko?” Bai kalle ta ba yace “yeah, sure” ta kuma cewa “ba wani gurin zaka kaini ba ko?” Ya juyo yana kallonta da guntun murmushi a bakinsa yace “babu inda zan kaiki, daga nan straight zuwa gidan oga Hassan” tace “ka rantse” yace “I cross my heart and hope to die” ta bata rai tace “da Allah ai nace ka rantse” seriously yace “na rantse da Allah ba sace ki zanyi ba. Can we go now?”

Dogon convoy aka hada ana ta sharara gudu akan titinan garin Kaduna, manyan mata suna ta rangada guda yayinda samari da yammata kuma suke kara volume din kida suna rausaya a cikin motoci, amarya kuwa motarta na tsakiya tana jinta kamar a cikin gajimare take tafiya ba wai a cikin mota ba. Ta lullube fuskarta da mayafinta amma da yake ba mai duhu bane ba tana hango gabanta, a haka har suka isa low cost, har suka shiga jerin gidajen da a cikin films da kuma social media ne kawai take ganin irin su. Ta bude ido sosai zuciyarta tana bugawa da karfi tana son ganin wanne ne nata a ciki, a haka taga anzo kofar gidan tun daga wajensa zata iya cewa kaf jerin gidajen babu wanda ya kaishi kyau da tsari. Aka bude gate, mutane da yawa a ciki mata suna ta guda, wannan ya tabbatar mata da cewa wannan shine gidan nata, sai da motar taje gaban gidan sannan ta lura gidajen guda biyu ne a jere amma ko kusa basu yi kama da junan su ba, na farkon yayi ukun na biyun, tayi murmushi a ranta, maybe na biyun na Hussain ne, ko daga nan wannan so call gimbiyar zata gane tayi mata zarra.

Amma sai me, sai taga an wuce katon an tafi ga an karamin, sai a lokacin ta lura cewa kofofin katon a rufe suke fitulun sa a kashe karamin kum komai a bude yake tana iya hango mutane a ciki ma. Ta juya side din Aunty, zuciyarta tan agaya mata t tunawa Aunty cewa anyi mistake ba nan ne gidan Hassan ba nan gidan Hussain ne. Amma sai taji aunty tana cewa “alhamdulillah Ruqayyah Allah y kawo ki gidan ki lafiya, sai kiyi masa godiya sannan ki fito da kafar dama tare da bismillah” sai wata zuciyar ta gaya mata to ko nan part din Aunty da yara ne aka kawo ta ayi mata fada sannan a kaita part dinta? Yes, that must be it.

Ta fito da bismillah kamar yadda Aunty tace, sannan Hajiyan Kano ta kama hannayenta tana tafiya da ita yan uwanta ta suka rako ta suna take musu baya. A palo ne taga hoton su ita da Hassan wanda suka dauka last week yace enlargement za’a yi musu a kafe musu a palon su. Kafafuwanta taji sun kasa daukan ta, jikinta yayi sanyi kwakwalwar ta tana neman toshewa. Ta tafi kamar zata fadi, Aunty tayi saurin riketa “subhanallah. Ruqayyah lafiya? Sai ta taba wuyanta, wuyan da lokaci daya da dauki mugun zafi ta ce “ya salam, jikinta zafi, dama bata jin dadi?” Goggo Habibah yayar Inna Ade tace “anya kuwa, kamar lafiyar ta kalau” Ruqayyah ta fara kuka a hankali irin wanda sheshsheka ce kawai take fitowa, tana jin tamkar duniya ce gabaki daya take ruguzo mata aka, tana jin kamar duk mafarkanta suna tarwatsewa a gaban idonta. Zuciyarta tana rada mata wata magana, wata mummunar magana.

Hussain shine CEO na H and H ba Hassan ba.

And that explains alot of things. Tayi saurin tana girgiza kanta kamar mai fada fa zuciyar tata. No, no, no. Ta ringa maimaitawa

She felt her dreams shattering. Ta sake girgiza kanta trying to comport herself, wani barin na zuciyarta yana gaya mata “ba haka bane ba, kinsan Hassan da makale aljihu, shine zai zabi gina karamin gida ba wai dan ba shine mai Company ba” sai daya barin yace “kuma sai yabar kaninsa ya gina babban gidan da ya fi nashi?” Nan take sautin kukanta ya karu

Kuka take yi kamar ranta zai fita, Hassan ya yaudareta yaci amanar ta, yayi mata karya dan ya aureta. Zuciyarta zafi take mata, zuciyarta ciwo take yi mata, anya kuwa ba ciwon zuciya ne zai kama ta ba?

Tana jin maganganun mutane a kusa da ita, yawancin su hakuri suke bata, sama sama kuma tana jin dariyar wasu. Sai ta fahimci sun dauka kukan barin gida take yi. “Kaji yarinyar nan, har muna yabonta muna cewa yarinya karama amma bata yi kuka ba ashe kukan zuci take yi sai yanzu zata yi na fili” “kiyi hakuri Ruqayyah, muma duk da haka muka sossoma wai kuturu yaga mai kyasbi” suka kwashe da dariya wasu daga ciki suka yi guda, “ni sanda za’a kaini gidan nawa mijin ma guduwa nayi, sai da akayi ta nema na aka rasa har aka hakura sannan na dawo, ina dawowa kuwa aka kama ni aka kaini” aka sake wata dariyar.

Ruqayyah taji tamkar ta samu bindiga Ak47 duk ta bi su da bullet goma goma. Dan dai tasan sun fi ta karfi ne da babu Abinda zai hana ta tashi ta rufe duk mutanen gurin da duka. But bata son ta bata rawar ta da tsalle, zargi ne ai kawai take yi, bata tabbatar ba lokacin taji muryar Nafisa a kusa da ita, “kiyi hakuri kiyi shiru kinji yayata kar kanki yazo yana yi miki ciwo, kinga duk su Aunty tsokanar ki suke yi” sai itama tayi dariyar sannan kuma ta juya tana waigen neman Sumayya tace “ina Sumayya? Wata kila ita zata iya rarrashinta”

“Kaga Adam kazo ka mayar dani inda ka dauko ni ko kuma ka kaini inda zaka kaini, ka daina yawo dani a titi” yace “sai kinyi dariya tukunna. Haka kawai dan Ruqayyah tayi aure sai ki zauna kiyi ta kuka har idonki yayi wannan kumburin? Kinga fuskarki kuwa?” ta kuma hade rai “ni bana cikin mood din dariya, dan Allah ka rabu dani” yace “in rabu dake fa kika ce? Kamar fa kina nufin in rabu da wani sashe na jikina in daina amfani dashi kenan fa? Kina ganin haka zai yiwu?” Ta kara hade rai “kaga fa za’a neme ni a can, in aka fahimci yawo na tafi kuma za’a yi min fada. Dan Allah ka kaini, ni jikina bani yake yi kamar Ruqayyah tana nema na” yace “Ruqayyah da aka kai dakin miji, maybe ma suna can suna zuba soyayya ita da mijin ta ke kina nan kin hana ni ganin hakorinki” tace ” koma dai me take yi ni ka kaini in ganta, dan Allah” yace “sai kin yi dariya” ta sake hade rai yace “Please, pretty please!” Ta dauke kanta gefe daya sai ya saki stirring ya hade hannayensa alamar roko “Please Please Please” da sauri tace “Adam zaka yar da mu fa?” Yace “kiyi dariya to” ba shiri ta yangare baki daga gani kasan dariyar karya ce, ya kama stirring yana dariya yace “bara dai in kaiki, ba dan halinki ba” sannan ya juya kan motar zuwa gidan su Hussain.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button