TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A bangaren Ruqayyah kuma mafarki take yi, mafarki take yi wai gata a cikin daki tana karbar haihuwar Fatima sai Fatima ta miko mata babyn “in go shi ki kaishi gurin Hussain. Ki kaiwa Hussain shima ya ganshi” sai ta barta a gurin ta juya ta kama hanya tana tafiya da sauri tana waige, sai kawai taga orphanage a gabanta, ba tare da tunanin komai ba ta ajiye babyn a kofar orphanage din yana ta kuka ta juya da sauri amma bata fi taku biyar ba sai kafarta ta makale, tayi tayi ta kasa tafiya ga kukan babyn ya cika mata kunnuwan ta tana kokarin ya fasa mata dodon kunne, sai kuma kafafuwan ta suka fara motsewa a hankali suna komawa kanana, a hankali har suka komawa irin na jarirai, har ta fadi kasa tana birgima tana kuka irin na jarirai, sai kuma taga jaririn data ajiye shi kuma yana girma yana girma har ya zama katoton namiji mai cikar kamala da kwarjini, sai ya taso ya taho inda take ya tsaya a kanta yana kare mata kallo, kamannin sa sak irin na Hassan sai kuma ya rikide ya koma Hussain sannan ya daga kafarsa wadda take sanye ta wani kafcecen takalmi ya sai ta tada niyyar talitse ta.

Ta farka a firgice tare kwalla kara “Hussain” amma kuma sai taji bata ji muryar tata ba, bata ji komai ba sai wani irin duumm marar dadi mai shiga har cikin kwakwalwar mutum. Ta bude idanuwan ta tana numfashi sama sama, sai ta ga Sumayya a zaune kamar kuka take yi tunda ga hawaye nan a idonta amma kuma bata jin karar kukan nata, ta ji an taba ta sai ta zabura ta waiga taga Hassan, me Hassan yake yi a nan? Ita dai a saninta sun bar shi a kaduna su sun tafi Germany inda zata ga likitan kafa. Ina ne kuma nan? Mai suke yi anan tare da Hassan?

Tayi kokarin tambaya “me muke yi anan? Ina ne nan?” Amma sai taji bata jin maganar tata. Sai ta tuna da abinda ya faru da ita a jirgi, the pain, the blood, sai ta saka hannayenta biyu tana dukan kunnuwan ta dasu “menene ya samu kunne na? Wayyo Allah na na shiga uku, menene a kunne na? Hassan, mijina ka taimaka min wani abu ya shigar min kunne na” Hassan ya fara kokarin kamata, yana yi mata magana, tana ganin bakinsa yana motsawa amma sam bata jin abinda yake fada, tana ganin Sumayya tana kuka tana magana amma ita ma bata jin abinda take fada. Ta kara rikicewa, ta mirgino ta fado daga kan gadon, ta fara kokarin tashi amma kafa taki cooperating. Hassan yayi sauri ya daga ta yana kokarin rungume ta ya lallashe ta amma taki barin shi, kuka take yi tana magana da karfi tamkar zata tsaga masa nasa dodon kunnen, babu shiri Sumayya ta kwantar da Hussain shima da hayaniyar uwar ta sa ta tashe shi ya fara kuka ta fita waje da sauri ta samo nurse, haka suka hadu da kyar suka rirrike Ruqayyah sannan suka sake yi mata wata allurar baccin ta koma.

Kafin dare labari ya iske gida, Aunty ta hada Nafisa da Zulaihat sannan suka biya suka dauko Inna da sassafe suka taho Abuja, lokacin da suka isa har an shiga da Ruqayyah dakin da za’a yi mata aiki dan haka sai suka hadu da Sumayya suka zauna zaman jira kawai da addu’a a bakin ta na samun nasarar yin aikin. Nafisa tace “ni ban taba ji ba, ko a labarai ban taba jin wanda ya samu irin wannan problem din ba kawai dan ya hau jirgi. Kuma jirgin nan ba yau ta fara hawansa ba da duk bai sa mata ciwon ba sai yau?” Sumayya tace “doctor din yace ana samu but it is very very rear. Amma yana saka ran success a surgery din sai dai kuma babu sake shiga jirgi a gun Ruqayyah” Zulaihat tace “to wa yake ta shiga jirgi kuma? Ana maganar lafiya? Fatan mu dai kawai ta samu lafiya dan itace tafi komai muhimmanci yanzu a gare ta” Sumayya ta gyada kai, amma a ranta tasan maganar shiga jirgin nan ba karamin taba zuciyar Ruqayyah zata yi ba. She is not going to like the news.

Alhamdulillah anyi aiki lafiya an kuma gama lafiya, aka turo Ruqayyah aka fito da ita yan uwanta suna ta bin ta da addu’a kowa yana cikin alhini da tausayin ta. Inna kuma ta na tayi mata addu’ar Allah ya bata karfin zuciyar da zata karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu. A haka har ta farka, ta gansu a zagaye da ita suna kallon ta, Sumayya ido ya kumbura saboda kuka, still tana jin wannan feeling din marar dadi a kunnenta. Ta saka hannu da niyyar bubbuga kunnen wai ko zai bude amma sai ta ji su a nannade da bandage, sai a lokacin tunani yazo mata, tunanin irin azabar da taji a kunnenta lokacin da jirgin su ya tashi da kuma yaddata taba taji jini yana fitowa daga kunnen. Bata bukatar tambaya tasan ta samu matsala a kunnenta, bata bukatar tambaya tasan tafiyarta zuwa Germany ganin likitan kafa bata yi ba, sai ta fara kuka a hankali ba irin na jiya ba, tana kallon yadda bakunan su suke motsawa tasan sannu suke yi mata da kuma kokarin bata hakuri amma sai ta mayar da idonta ta rufe tana cigaba da kukan ta dan ba jin abinda suke cewa take yi ba. Wannan wacce irin mummunar kaddara ce? Ita Ruqayyan ita ce ta kurumce bayan kuma kafar ta da har yanzu aka kasa gane menene matsalar ta?

Babu wanda bai tausayawa halin da Ruqayyah take ciki ba musanman Hassan wanda bayan ta tashi ya fahimci bata jin abinda suke cewa sai ya koma gurin doctor da complain, amma sai doctor din yace masa ai ba yanzu ne zata ji din ba sai aikin yayi healing an kunce bandage din. Sai nan da sati biyu masu zuwa tukunna sannan za’a tabbatar da success din surgery din ko akasin haka.

A cikin sati biyun nan Hassan da Sumayya sun kasance tare da Ruqayyah, supporting her, encouraging her tayi accepting duk abinda result din ya nuna amma ita ta tubure so take yi su bar asibitin, su bar Nigeria gabaki daya su tafi kasar waje tunda ita a ganinta acan ne zata samu lafiya, gani take nan kawai karasa lalata mata kunnen zasu yi ga kuma kafarta da take getting worst everyday. Sai dai har yanzu Hassan ya kasa samun courage din gaya mata abinda likita yace, tausayinta yake ji, ya kasa samun right time da zai ganta cikin mood mai kyau yayi mata bayani, kullum cikin kuka take, kullum cikin mita take. Ga magana da karfi in ya nuna mata ta rage Muryar ta sai ta fara kuka tana ganin kamar yana mocking dinta ne. In zasuyi mata magana a takarda suke rubuta mata, in zata basu amsa kuma sai ta fada, da karfi kamar zata tsaga dakin. Ta zama very edgy, abu kadan sai fada sai kuka shi har tsoron shiga dakin yake yi gurinta shi yasa yake jinjinawa kokarin Sumayya dan tunda suka zo tana tare da Ruqayyah ko nan da can bata zuwa tana ta hidima da Hussain ga kuma nata ciwon da yake cin zuciyarta na rashin sanin inda Adam yake. Amma bai taba jin tayi complain ba ko sau daya. Wannan yasa ya karbi Hussain daga hannunta ya mayar dashi Kaduna gurin Inna aka cigaba da bashi madara dan ga uwar tasa nan amma ba samun shan nonon yake yi ba madarar ake bashi.

Ranar da sati biyun suka cika a ranar ne aka budewa Ruqayyah bandage din kunnen ta, doctor din ya kunce tare da wanke kunnen a gaban Hassan da Sumayya sannan ya gwada yiwa Ruqayyah magana “Hajiya Ruqayyah, can you hear me?” Ta juyo tana kallon sa, tana ganin bakin sa yana motsawa sannan tana jiyo Maganar sa can nesa kamar irin ana hira a makota din nan. Bata fahimtar abinda yake cewa sai data tattara dukkan hankalin ta a guri daya sannan ta fahimce shi, ta rufe idonta hawaye yana zuba, tace “ina jin ka, amma bana fahimtar ka, maganar bata clear” sai doctor din yayi murmushi cikin jin dadi yace “alhamdulillah. An samu nasara kenan” duk suka kalle shi cikin mamaki, Hassan yace “an samu nasara fa kace, bayan kana jin tace bata fahimta? Menene amfanin ji idan ba’a fahimta?” Doctor din yace “jin shine babbar nasarar da muka samu, ear drum din ya gyaru kenan ya fara receiving sound. Clearing sound din kuma sai anyi mata taimako da hearing aid. Zai kara enhancing ya kuma kara clearing din sounds yadda weak ear drums dinta zasu karbe shi sosai”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button