TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Idon Fatima ya juye ta zube akan kujerar ta, Ruqayyah ta dora hannu aka tare da rafka salati, and then, Lawan driver ya juyo yanason yaga sakon da Minal take nunawa, wannan abinda yayi hadi da karar kwana, ya saka ya saki stirring kuma maimakon ya taka burki sai ya taka accelerator.

Motar tayi gaba kamar fitar kibiya, ta daki edge din titi sannan tayi adungure da sauri, kasanewar gurin slope ne mai tattare da duwatsu ya saka ta cigaba da gangarawa da sauri tana yin cikin daji. Babu mota a kusa dasu dan haka babu wanda yaga faruwar abin.

Ruqayyah tana salati, tana jiyo salatin drivern tare da Minal banda Fatima da already ta riga ta suma tun kafin abin ya faru, a haka har kanta yayi buguwar da ta daina ganin komai ta kuma daina jin komai. Ta suma.

Lokacin data farfaɗo jin kanta tayi yayi mata nauyi sosai. Ta saka hannu tana dafe kan tare da kokarin yin salati, amma sai taji ba wai kan bane kadai yayi nauyi gabaki daya jikin tane yayi nauyi, ta jima a kwance a inda take sannan ta fara samun karfin bude idonta, abinda ta fara lura dashi shine duhun da gari ya fara yi. Ta dafe kanta ta mike zaune tana numfashi da sauri da sauri har ta samu ta dawo hayyacin ta. Abu na farko da taji a jikinta shine azabar zafin da yake tahowa daga kafarta zuwa sauran sassan jikinta. Gabanta ya fadi tana kai duba izuwa kafafuwan ta. Wani karfe ta gani ya huda naman cinyarta ya wuce. Ta kama shi da hannu daya sannan ta dafe kafar da hannu daya ta zare shi daga jikin ta tana jin azaba tamkar ranta zai bar jikin ta. Sai ta samu kanta da godewa Allah da bata taho da Hussain karami ba. Ta yanki gefen dankwalin ta ta nannade ciwon tana tsayar da zubar jinin da yake yi.

Sai a lokacin tasamu damar karewa gurin da take kallo, motarsu tana can gefe ta daki wata bishiya ta tsaya a kife, tayoyinta a sama, daga inda take tana iya jiyo kauri kamar wani abu yana konewa. Ta mike a hankali tana dai-dai ta tsayuwar ta sannan ta fara jan kafa zuwa inda motar take ta leka ciki, sai ta dawo baya da sauri tana rufe bakinta idanuwan ta kamar zasu fado kasa, kallo daya tayi wa drivern ta san ya mutu saboda yadda wuyansa ya karkace gefe, ta hadiye kukan daya taso mata tana zagayawa barin da Minal take. Idanuwan ta a bude suna kallon Ruqayyah amma ita bata kallon ta, jini yana fita ta kunnen ta da hancin ta. Ta girgiza ta. “Minal, Minal, Minal” amma ita kanta tasan babu Minal ta tafi inda ba’a dawowa. “Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun” ta fada tana kallon katon cikin Minal din wanda ake saka ran haihuwarsa ko yau ko gobe. Ta zame gefe daya ta zauna hannun ta akan ta tana rusa kukan rashin kawarta aminiyarta tare da abinda yake cikinta.

Ta sake tashi tana leka bayan motar tana neman Fatima, babu ita babu alamun ta.

“Fatimah! Fatimah” ta fara kwalla kiran Fatima da duk iyakacin karfinta amma shiru. A lokacin ne ta lura da abinda yake kauri, motar ce take kamawa da wuta daga kasa, nan take tsoro ya kama ta fara kokarin jawo gawar Minal daga gurin da take dunkule a tsakanin karafunan inji amma ta kasa, duk da ita ba likita bace ba daga yanayin kwanciyar Minal din ta tabbatar tayi rugu rugu. Ta zagaya side din driver tayi kokarin fito dashi shima amma injin motar da kuma kujerar sa sun matse shi a guri ɗaya. Ta ja baya tana mayar da numfashi tana kallon yadda wutar take kara ruruwa har ta fara cin seat din baya, hasken ta yana haska gurin, a lokacin ta lura da alamar sawun mutum ya bar gurin motar ya shiga cikin bishiyoyi. Fara bin sawun tana kiran sunan Fatima, tana dauke ganin ta daga wutar da take cin gawawwakin a cikin mota.

A hanya taga wayar Fatima, ta dauka tana lura da cewa bata mutu ba duk da cewa screen din ya fashe amma tana ganin hoton Hussain a jikin screen din yanayi mata murmushi, ta tuna da labarin da Minal ta basu a mota wai Hussain ya mutu. Ta cigaba da kiran Fatima tana kara kutsa kai cikin bishiyoyi, suddenly ta ganta a gabanta kamar an jeho ta tana kallon ta da budaddun idanuwa tana cewa
“help me please, ki taimaka mini dan Allah”
gaban Ruqayyah ya fadi saboda fahimta da tayi cewa wadannan suna exact words din da Hassan ya gaya mata ranar da ta fara ganinsa a toilet din su, and it seemed like a long time ago amma shekaru biyu ne kawai. Ta rike ta “Fatima lafiya kike? Babu abinda ya same ki? Minal ta mutu ita da driver” Fatima tace “mafarki nake yi, ki tashe ni dan Allah. Mafarki nake yi wai Hussain ya mutu, wai munyi hatsari a hanyar Abuja, wai ina labor zan haihu a daji” sai a lokacin Ruqayyah ta lura da jinin da yake bin kafafuwan Fatima. “Innalillahi, na shiga uku, Fatima haihuwa zaki yi” Fatima tace “ki tashe ni daga bacci dan Allah, ki kira min Hussain dan Allah” surutai kawai take yi wanda Ruqayyah tabbatar ba a cikin hankalin ta take ba, ta jata gefe ta kwantar da ita, a haka ta haihu a hannun Ruqayyah, danta namiji katoto dashi lafiyayye.

Ruqayyah ta daga dan bayan mabiya ta fito , ita bata san yadda zata yi ta yanke masa cibiya ba dan batada wani abun da zata iya yanke cibiya dashi. Ta daga shi tana nuna wa Fatima, “gashi kin haihu, kin samu da namiji” Fatima ta karbe shi ta rungume shi a kirjinta duk da ba’a hayyacin ta take ba amma taji matsananciyar soyayyar abinda ta haifa. Hawaye ya zubo mata, Sai kuma ta mikawa Ruqayyah tace “ki kaiwa Hussain shi shima ya ganshi, burinsa kenan yaga abinda zan haifa. Bana so in ganshi ni kadai ba tare da shi ba” Ruqayyah ta karba tana kallon babyn, kamar an tsaka kara shida Hassan, hakan yana nufin kamannin Hussain ne dashi kuma da fatar Hassan tunda yafi Fatima ma duhun fata. Ta mayar da dubanta ga Fatima sai ta ji ta shiru, ta girgiza ta da hannu daya “Fatima Fatima” amma shiru.

Ta mike tsaye tana kallon Fatima sannan kuma ta kalli babyn da yake hannunta yana ta tsanyara kuka da dukkan karfin sa. Shikenan yanzu bashi da uba bashi da uwa kenan? Shikenan yanzu shine……. Sai kuma wani tunani ya fado mata. Yanzu wannan jaririn na hannunta shine sole heir na H and H and all its assets. Dogon gidan Hussain, tarin motocin sa, kamfanonin sa na shinkafa, fulawa, sukari, siminti duk yanzu na wannan yaron ne na hannun ta. Wannan yaron na hannunta shine kadai yanzu abinda yake tsakanin ta da H and H, tsakanin ta da zama matar CEO. Wannan yaron da bai fi ta taka shi ta wuce ba.

Tayi saurin katse wannan tunanin daga ranta tana realizing cewa wannan moment din da take ciki, right here right now shine maganar da malamin duban nan yayi mata. A yanzu tana da options guda biyu, ko dai ta tafi da yaron nan gida ta kaishi gurin Hassan da dauran yan uwa su raine shi ya girma su cigaba da rayuwar su a karkashin sa, maybe ma in ya girma ya wulakanta su tunda basu duka haife shi ba ko kuma ta bayar dashi right here and right now and her husband will have majority share ta H and H. Already ta haifa masa maza guda uku, already gidan sa nata ne.

Ta girgiza kanta da sauri, no no no, no matter how much take son dukiya, no matter how much take son ta zama mai kudi she can never kill for it, ko babba ba zata iya kashewa ba ballantana wannan dan jaririn. Ta tuna da maganar malamin “zabi ya rage naki” ta sake girgiza kai kamar yana kallonta, ta kalli Fatima, tana tunawa da Matsayin ta da martabar ta, sai ta tsallake ta ta wuce, ta fara tafiya a hankali har yanzu vata yanke shawarar abinda zata yi ba. Ta cire dankwalin kanta ta nannade jaririn tare da mahaifarsa a ciki sannan ta cigaba da tafiya, a haka ta fito bakin titi tana kallon motoci suna wucewa amma saboda bata yanke hukuncin abinda zata yi da jaririn hannunta ba sai ta kasa tsayar da mota ta nemi taimakon su, ta cigaba da tafiya a kafa ta cikin bishiyoyin bakin titi, tana cikin tafiyar ne taga wata mota kamar ta Hussain tazo wucewa, sai tayi sauri ta buya, jaririn hannunta ya fara kokarin kuka sai ta toshe masa baki, sai taga kamar motar tayi slowing down kamar zata tsaya sai ta kara shigewa cikin bishiyoyi da sauri.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button