TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Dare yana yi yabi shawarar da Gimbiya ta bashi, ya kira Salisu ya taya shi hada kayansa sannan ya zame jikinsa ya bar hotel din ba tare da sanin kowa ba, ya koma wani hotel din ya saka Salisu yayi masa reserving daki secrectly ya shiga yayi zamansa.

Washegari da safe wani message din ya shigo.

“Ka dauki kudin, da karfe goma sha biyu na dare ka saka a back seat din motarka ka fita kai kadai, make sure police basu bi ka ba, kaje kofar companyn ka, inda muka dauki Hassan kayi packing motar daga gefen katanga ka bar key a jiki ka fita ka hau babur ka koma gida. Ko Aunty ka gaya wa zamu sani”

Ya karanta sannan ya ajiye wayar, a ransa yana noticing yadda suka ambaci Aunty da sunan Aunty.

Sai ya dauki wayar yayi musu reply

“Then how do I get my brother?”

Suka amsa

“Zai dawo gida da ƙafafuwan sa, that’s in kayi abinda mukace, if not, zaka tsince shi somewhere”

Hussain bai kira commissioner ba kuma bai yi niyyar kira ba. Da magrib ya fita shi kadai a mota ya koma gidan su, an tafi masallaci dan haka mai gadi ne kadai yaga shigarsa shima kuma ya gaya masa kar ya gaya wa kowa yazo. A dakinsa bayan yayi sallah ya bude safe box dinsa ya dauko jakar da ya zuba kudin ya sake kirgasu ya tabbatar sun cika sannan ya ajiye ya kwanta akan gado ya rufe idonsa.

Sai karfe goma ya tashi yayi wanka yayi sallar ishai sannan ya zauna yana kallon agogo yana ticking har ya sauka kan 12 sannan ya mike ya dauki jakar ya fita. Babu wanda ya ganshi sai salisu sai kuma mai gadi. Ya dauki hanya har zuwa inda suka gaya masa yayi packing ya tabbatar babu wanda yake ganinsa sannan ya fita ya danyi tafiya a kasa sannan ya tari babur ya hau ya koma gida, yana sauka sako yazo masa “very good boy, aikin ka yayi kyau. Ka zauna ka jira zuwan danuwanka”.

Ya mayar da wayar cikin aljihun sa ya shiga gida ya zarce Bedroom dinsa ya sake wanka ya zabi kaya masu kyau ya saka, ya saka hula, agogo, socks da takalmi ya fesa turare ya dawo palor ya zauna, idanunsa akan kofa, waiting……

Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only

???????? TAGWAYE ????????

By

Maman Maama

Episode Ten: Brave and Selfless

Last free Episode

“Please, help me. Dan Allah, ki taimaka min” Sai kuma ya cika ta a hankali ya bi jikin katangar ya fadi kasa.

Sai data ja numfashi sosai ta dawo cikin hayyacin ta sannan ta juyo tana kallonsa daga tsayen da take a kansa, sai kuma ta sunkuyo sosai tana kare masa kallo, he looked dirty and terrible. Ta kuma lura da ciwon da uake fitar da jini a wuyansa. But there is something about him, something da yake ta fincikar zuciyarta zuwa gare shi ta kuma kasa fahimtar menene, ta durkusa tana karewa fuskarsa kallo ko zata fahimci ko ta sanshi somewhere amma taga cewa bata taba ganin wannan fuskar ba. But something a zuciyarta keeps screaming “money” ta kuma rasa a ina money din yake.

Tayi analysing situation din. Ta tuno da sautukan da suka ji a daki masu kama dana harbin bindiga, ta kuma tuno da mutanen da taji sun wuce ta kusa da gidan su kuma da alama wani suke nema, ta kalli Hassan tana tabbatar wa da kanta cewa shi ne wanda suke nema, kuma sune suka ji masa ciwon jikinsa. Amma me yasa? Waye shi su kuma su waye? Zata iya yiwuwa shi mugu ne su kuma police, za kuma ta iya yiwuwa sune mugaye shi kuma victim dinsu. ” A kidnapped victim” zuciyarta ta gaya mata. Ta kalli kayan jikinsa, duk da cukurkudewar su amma ta fahimci masu tsada ne, meaning shi din mai kudi ne.

Ta girgiza kanta tana son ta saita tunanin ta. “Uwar biyu an sace yaron nan, yaron da yayi mana interview wai ana tunanin masu garkuwa da mutane ne suka dauke shi” ta tuno da maganar Baba tun last week, dazu da yamma ma sai da taji yayi maganar “yaron nan har yanzu ba’a ganshi ba uwar biyu, dogo ne baki mai matsakaiciyar kiba da kyakkyawar fuska. Har yanzu ina ganinsa a idona. Allah ya bayyana shi”

Ta sake kallon Hassan, he fits the description. Akwai kyakkyawar fuska kam babu laifi. She might be wrong but she is going to help him, tasan in taci nasara zata samu reward mai kyau. Bata san ta yadda zata taimaka masa ita kadai ba kuma bata son taso mutanen gidan su saboda tana son ya san ita kadai ta taimaka masa saboda yafi ganin kokarin ta sosai dan tafi samun reward mai kyau. Abinda zata yi din yana da hatsari but she is going to do it. Ruqayyah ce fa, Ruqayyah kuma bata jin tsoro.

Ta tattaba fuskarsa, ya dan bude ido yana kallon fuskarta ta cikin hasken farin wata kamar yadda itama take kallon tasa fuskar tace “zan taimaka maka. Bansan ko waye kai ba za kuma ka iya cuta ta na sani amma na fahimci kana bukatar taimako dan haka zan taimaka maka dan Allah ba dan komai ba”.

Ta cire dankwalin kanta ta yaga shi gida biyu ta ninke part daya ta dora a ciwon wuyansa sannan ta daure wuyan da dayan part din. Ta taba jikinsa taji ya dauki zafi alamar zazzaɓi ya fara saukar masa. Ta rafa lissafin abin yi. A lokacin taji maganganun mutanen sun kuma dawo wa farkon layin daya yana cewa “police might be on their way. Wani zai iya reporting harbin” dayan yace “not Nigerian police. Am not leaving unguwar nan sai na mayar dashi gawa. Gida gida zamu bi. Am sure na ganshi ya shigo layin nan na tabbatar he is hiding a cikin wani gidan. Ta nan farkon layin zamu fara” ya fada yana knocking kofar gidan da yake opposite nasu da karfi yace “open this door ko mu fasa ta”.

Hassan ya kamo Ruqayyah jikinsa, idonsa yana kokarin juyewa, jini yana dibansa ya sake cewa “help me please. Ki kai ni gurin Hussain” dusu dusu yake ganin ta. Ta cire hannun sa daga jikinta tana jin wani iri, ita tun da take namiji bai taba taba ta ba, ko brothers dinsu basa irin wannan wasan saboda sun samu tarbiyya mai kyau a gurin Inna ade da Baba. Ta rada masa. “Ka kwanta anan, kar kaje ko’ina. Kar kayi motsi. Ina zuwa” sai ta mike zuciyarta tana yi mata plan na abinda zata yi. Ba tare da tsoro ko shayi ko kokwanto ko kuma tunanin komai ba ta zagaya ta daya side din toilet din ta taka bucket ta kama katanga ta haura, Hassan ya bi katangar da kallo sannan ya mayar da idonsa ya rufe yana jin tunanin sa yana barin kwakwalwar sa.

Ruqayyah ta dira a bayan gidan su, tana jin kafarta tana amsawa ta dan jima har taji kafar ta saki, tana jin maganganun mutanen a daya side din gidan daga dukkan alamu an bude musu kofar gidan sun shiga. Ta ja dogon numfashi sannan ta fita a guje tamkar yar tseren gudu, dogayen ƙafafuwan ta suna taimaka mata gurin covering distance mai yawa cikin lokaci kankani taje karshen layin bayansu sannan ta zagayo kan layin su gaban gidan dayake karshe, ta durkusa tana mayar da numfashi sannan ta mike tsaye tayi gyaran murya ta bude muryarta da dukkanin karfinta ta fara ihu “wayyo Allah jama’a ku taimaka min ga wani ya shigo min daki. Wayyo Allah gardi a dakina. Jama’a ku taimaka min jini ne a jikinsa”!

Ta ringa fada tana maimaita wa, daga can ta hango mutanen sun fito da sauri daga gidan da suka shiga suna hasko inda take da fitila, sai kuma taga sun taho a guje zuwa wajenta. Daya da touchlight a hannun sa dayan kuma da bindiga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button