TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ruqayyah bata iya motsawa ba, bata kuma iya cewa komai ba har taji sun tayar da Napep dinsu sannan yaji motsin bude gate din gidan alamun sun fita.

Sai bayan da su Inna suka bar gidan Baba sannan Hassan ya fito shima bayan Baba yayi masa doguwar nasiha akan yarda da kaddara da kuma mika lamura ga Ubangiji da neman zabinsa dan samun dacewa. Daga gidan Baba bai koma gida ba dan baya jin zai uya shiga gidan, sai ya tafi ya kama hotel ya zauna, ya kira Aunty ya gaya mata yana nan lafiya amma zai dan zauna a hotel kwana biyu, ita kuma Aunty sai ta dauka rigimar da suka yi da Ruqayyah akan tarewar da tayi a gidan Hussain ne ya saka shi yayi mata yaji, sai ta fara yi musu addu’ar samun fahimtar juna.

Sai da Hassan yayi sati guda a hotel din shi kadai. A cikin satin nan yayi abubuwa da yawa, na farko ya kara dawo da alakar sa da ubangiji, yayi Adduoi da dama akan rayuwarsa, ya nemi ubangiji yayi masa jagora ya bashi ikon cin dukkan jarabawowinsa, ya nemi zabin Allah a dukkan hukunce hukuncen da zaiyi a yanzu wadanda yasan zasu taba gaba ki dayan zuri’arsa kar karshen rayuwar su. A cikin satin yana daga hotel din ya yi abubuwa da yawa. Na farko ya siyar da share dinsa ta H and H kamar yadda yayi niyyar yi, sadakar nan da yayi niyyar yiwa Hussain sai ya yi ta babu fashi, abin mamaki sai Umar yayan Fatima wanda a lokacin shine yake tashen kudi a gidan sarkin kano ya siya. Sauran rabin kuma wanda shine na Hussain sai yasa aka kaiwa masana rabon gado suka raba, na Fatima Umar din ya sake siya, ya bawa iyayenta kudin. Wanda ya kasance nashi rabon kuma sai yace a barshi a cikin kamfanin a matsayin share.

Satin nayi daya fito sai yaji kamar duk wasu nauye nauye da yake jin su akan kafadar sa duk babu su kamar an dauke masa su. Yaji confidence a ransa, yaji a zuciyarsa kuma dukkan al’amuran suna warware masa da kansu.

Bai je gida ba sai daya je office ya aiwatar da duk abinda ya riga ya yanke hukuncin zai aiwata, sannan ya tafi gida. Direct part din Hussain ya tafi inda yasan acan ne zai samu Ruqayyah. A can kuwa ya same ta, tana dakin nan mai zanen sarauta tana feeding Hussain. Yana shiga ta dago kai tana kallonsa, idon ta kamar zai fado kasa, ta ajiye feeder a gefe cikin rawar murya tace “da gaske nake wallahi, duk abinda nace zan fada sai na fada wallahi. Har kafata, zan ce su suka shanye min kafata a gurin accident din suka mayar dani gurguwa” ga mamakin ta sai taga yayi murmushi ya samu guri ya zauna yana facing dinta yace “say whatever you want to say, do what ever you want to do. Hussain yana kabarin sa kuma duk maganganun ki ba zasu taba hurting dinsa ba dan he is out of your reach. Ko mutane sun tsine masa tsinuwar su ba zata taba yi masa komai ba saboda shi Ubangiji yasan gaskiya and that’s all that matters. In ma da akwai wanda abinda zaki fada zai yi hurting to nine, ni kuma zuciyata yanzu ta zama ta karfe babu abinda zai iya hudata balle ya dame ni” ta sake jawo little Hussain jikinta tace “ba zan fita ba, wallahi ba inda zanje, ai na haihu da kai dan haka I deserve something” sai ya gyada kai yace “haka ne, kin haifa min yara har gida uku sune kuma dalilin da yasa ba zan kira police yanzu su fitar da ke daga gidan nan ba, kuma sume dalilin da yasa nazo gurinki yanzu zamuyi magana” sai ya tura mata takardu gabanta yace “wannan takarda ce, na riga na saka hannu nayi komai akan cewa na baki dukkan abinda na gada na daga dukiyar Hussain. Share ce mai tsoka a kamfanin H and H. Ba’a siyar da kamfanin ba yana nan kuma a yanzu kece kike da share mafi girma a ciki, na kuma nema miki manager da zai runga gudanar miki da komai yana saka miki kudadenki a cikin account dinki” ta bude baki tana kallon sa sai kuma ta kalli takardar, ya mika mata ta karba da sauri, sai shi kuma ya saka hannu ya dauki little Hussain, ta kalle shi tace “me kake so to? Tunda kace baka damu da in yi shiru ko inyi magana akan abinda nace zan fada dangane da Hussain ba” sai yace “yayana nake so. Babu ke babu su, shine deal din” ta zaro ido “yayan nawa? Ni fa na haife su ta yaya zaka ce babu ni babu su?” Sai ya daga kafadar sa yace “zabi ya rage ya naki kuma, ko ya’ya ko dukiya, in baki yarda ba zan karbi takardata kuma zan saka a fitar min dake daga gidan nan ki tafi duk inda zaki je sannan kuma zan karbi yayana ta karfi, kinsan ina da karfi najiki dana aljihu, kuma a iyakacin sanin da nayi Baba da inna sunce babu su babu ke, zabi ya rage naki” ta fara kuka tana kallon Hussain tace “Hassan baka da imani” yayi murmushi yace “bana jin akwai wanda ya kai ki rashin imani Hassana. Wannan shi yasa zan raba ki da yayana saboda ke din macijiya ce mai dafi, bana son ki shafa wa yayana mugun dafin ki” tace “yayana ne nima ai, kuma ko ka raba ni dasu dole wata rana da kansu zasu neme ni” yace “tabbas haka ne, but before then sun mallaki hankalin kansu sun samu tarbiyya mai kyau”

A lokacin twins suka shigo dakin da gudu sunji labarin daddy ya zo, suka rungume shi sai yace “ku je maza Nanny ta hada muku kayan ku, ku gaya mata zamu je unguwa daku” suka fita da sauri suna murna. Ruqayyah ta dafa bango ta mike tsaye tana kallon sa, ya tako zuwa gabanta, ta mika hannu zata karbi Hussain sai ya matsar dashi gefe yace “for the sake of our children, for the sake of your parents, ina fatan watarana zaki dawo kan hanyar dai dai ki gyara kurakuren ki” ta kara sautin kukan ta. “Yanzu Hassan abinda zaka yi min kenan? Dan nakasa ta same ni? Wato na gama yi maka amfani kenan ko? Kaci moriyar ganga ko?” Ya gane abinda take kokarin yi, so take ta saka yayi feeling guilty kamar shine mai laifin ba ita ba. Bayan shi gani yake yi ba karamin adalci yayi mata ba.

Ya yanke hukuncin bata kudin ne saboda yana son ta fahimci wani abu a rayuwa, ta fahimci cewa kudi is nothing compared to love, ta fahimci cewa akwai abubuwa da dama wa’danda kudi basu isa su siya mata ba, idan ba haka yayi mata ba bazata taba fahimta ba, kuma no matter how he tried ba zai taba cire ta daga rayuwar sa ba ko da kuwa saki dubu yayi mata.

Bai kula ta ba sai ya fita yayi locking duk dakunan Hussain ya cire keys din ya saka a aljihunsa, ba dai babban gida take so da dogon bene da katon valcony ba? Gashi nan ta samu, ba dai H and H take so ba? Gata nan ya bata. Ya kuma barta da duniya.

Yana fitowa twins suna dawowa Nanny tana jan akwatin kayansu, yana kallon Ruqayyah ta jawo kafa zuwa bakin kofar dakin da take tana kallon su tana sheshshekar kuka. Har yaran zasu tafi gurinta sai ya rike su ya yaudare su da zancen ice cream suka sauka kasa da sauri, har sunje bakim kofa ya sake juyowa ya kalli Ruqayyah ya kama rails tana kallonsu, ta bude baki zata yi masa magana sai yayi sauri ya fita ya turo kofa.

Washegari da safe tana kwance duk da ba bacci take yi ba taji kara kamar ana gini, ta tashi da sauri ta ja kafa zuwa taga ta leka sai ta hango katanga ake ginawa ana raba tsakanin gidan Hassan da gidan Hussain, sannan kuma ana toshe karamin gate din daya hada gidajen gida biyu dana Aunty.

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button