TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan littafin na siyarwa ne, duk wanda yake so ya neme ni through WhatsApp ta wannan number din 08067081020

Wannan littafin na siyarwa ne, in kina so WhatsApp 08067081020Episode Twenty Two: Envious

Overlook the typos please………….too lazy to edit.

Thank you so much for the birthday wishes. I had a great day, and you guys contributed a lot to that.

Nayi mistake din numbering, na shekaran jiya twenty ne na jiya twenty one na yau kuma twenty two.

Muna ta Allah wadai da halayen Ruqayyah, ina fatan muna tsintar pieces of halayyar mu a cikin nata.
Idan kina jin haushi a yayin da wani ya samu daukaka kina jin ina ma ke ce ba shi bane ba.
Idan kina kallon saurayin kawarki kina jin ina ma dai naki ne ba nata ba.
Idan kina jin bacin rai idan kika ga business din wata ya bunkasa ba naki ba, ko wata ta chanja kayan dakinta ke bami chanja ba, ko wata ta sayi kaya ke kuma baki da kudin siya.
Idan kina jin dadi a ranki idan wani ya samu wata matsala.
Wadannan duk kadan ne daga cikin siffofin hassada.

Hassada daban kishin kai daban, kishin kai shine ki nemi na kanki a lokaci guda kuma kina yiwa sauran masu neman na kansu wadanda suke sama da ke da wadanda suke kasa dake fatan alkhairi.

Yar uwa, a duk lokacin da kike kallon na sama dake a samun abin duniya to zai toshe miki idanuwanki ki daina ganin kyawun abinda yake gabanki, abinda kike dashi, wannan kuma shi zai sa ki zamanto marar godiyar ubangiji.

Yar uwa ki kalli na kasa dake, ki duba dubunnan mutanen da suke fatan su samu daukaka irin taki, wannan zai saka ki samu wadatar zuci.

Irin wadannan halayen baka sanin kana dasu har sai kayi nisa a cikin su. A lokacin kuma sun riga sun bi jini da tsokar jikin ka.

Yes, akwai mutane irin Ruqayyah and they walk amongst us

           *******************

Da kyar Sumayya ta samu ta lallaba kawayen da mostly Ruqayyah hayar su tayo, ta gaya musu babu siyan baki yau sai ranar lahadi, farko suka ki tafiya suka ce ai dare yayi sai dai su kwana da safe sa tafi, ita kuma tasan indai suka kwana din to kuwa cewa zasuyi sai anje dasu kano kuma Allah kadai yasan abinda zasu aikata acan din. Ba zata dauki wannan chance din ba, dan haka ta koma sama ta samu kudi a gurin Ruqayyah ta kuma lallabasu dashi, sannan ta fita waje ta samu Adam “Adam da Allah a cikin drivers din gidan nan ka samu wani ya mayar da mutanen Ruqayyah gida” yace “ohhh okay, gani ai, kim manta nima drivern gidan ne?” Ta nuna shi tace “banda kai, someone else” yana murmushi yace “why? Ba kya so insha wahala?” ta juya kamar zata bar gurin sannan ta juyo tace “saboda yammata ne” ta shige da sauri tana jin sa yana mata dariya.

Washegari da sassafe aka aiko su bayar da kayansu, wai kayan duk a mota za’a hada su tare da motar da zata dauki kayan lefe, su kuma in sun shirya sai su bi jirgi. Ruqayyah ko hada kayan bata yi ba, sai a lokacin Sumayya ta taimaka mata suka debi wadanda ta saka da bikinta tunda bata dinka lefe ba kuma kayanta na gida duk ta barsu a gida saboda bata bukatar su. Suka hada akan kayan Sumayya a yar karamar jakarta suka bayar. Sai a lokacin sannan Sumayya ta jawo Ruqayyah da kyar suka fito zasu zagaya gida. Tun daga kan Bedroom din da suka kwana a ciki, daya Bedroom din wanda suke tunanin na Hassan ne amma daga alama shima bai tare ba tunda babu kayansa komai a ciki sai dai set din furniture shigen nata sai banbancin design da color. Suka zagaya katon palon da yake sama mai hade da dining room, su kansu set din dining din abin kallo ne, sannan suka sauko kasa suka duba three bedrooms din da suke kasan kowanne in suka shiga sai Sumayya taga kamar yafi ba baya kyau, Ruqayyah kawai binta take yi fuskarta babu yabo babu fallasa, suka dawo falon farko komai Sumayya ta gani sai tayi ta kambamawa dan ta jawo hankalin Ruqayyah har ta samu ta dan fara yabawa da kalmomi irin ” eh, yayi kyau” duk kuwa da cewa bata bata ganin makamancin shi ba ballantana wanda ya fishi.

Suka shiga kitchen Sumayya tana ta santin kitchen din da duk kayan da suke ciki, sannan suka fita waje ta kofar baya Sumayya tana yaba shuke shuken da akayi a surrounding area din, flowers masu kyau da kamshi aka zagaye backyard din gidan dasu, gidan Hassan mai kyau ne, mai matukar kyau ne, sai dai ace masa karami, kankantar ma za’a fada ne in akayi comparing da gidan Hussain. Amma sai Ruqayyah ta daga kanta kana kallon gidan Hussain, ita so take ta shiga ciki taga menene a cikin wannan katoton gidan, tasan anyi wa gimbiya jere so take taga dame dame aka saka mata, so take taga sun kai nata kyau ko kuma sunfi nata? Sumayya ta kama hannun ta suka koma, tanata yi mata hirar yadda mutane suka yi ta santin gidan har suka koma dakin ta sannan Sumayya ta cire kayanta ta shiga bandaki zata yi wanka. Kayan bandakin ma sai data yi ta gwadawa kafin ta iya gane yadda zata yi amfani dasu. Bayan ta shiga toilet din ne sai Ruqayyah taga kofa a tsakanin windows, ta saka hannu ta bude ta shiga. Nan take taji farin ciki ya kamata “a balcony!” Madaidaicin balcony ne mai kyau da tsari, railers din sa kawai abin kallo ne ga set din kujerun hutawa da dan karamin teburin su. Ta zauna akan kujera daya tana murmushi, sai ta juya da niyyar ganin gari, da niyyar ganin Kaduna a kasan ta amma sai taga gidan Hussain yayi bakevake ya tare mata hanya. Ta daga kanta tana hango karshen gidan sai taga balcony a can karshe, meaning idan matar Hussain ta fito ita ma ta fito to matar Hussain zata ke hango ta a kasanta. Taji zuciyarta ta buga, ranta ya baci, hankalin ta ya tashi. Ita gidan Hussain take so, wancan balcony na sama shi take so ba wannan ba. Ta mike da sauri ta shige ciki ta rufe kofar ta murda key sannan tazo ta wuce Sumayya da take ta santin closet din data bude duk da babu kaya a cikin ta, ta shiga toilet, ta jefa key din a toilet tayi flushing dinsa.

Suna gama wanka Aunty ta sake aikowa tace su tafi can main house din suyi breakfast, suka shirya sama sama sannan suka fita tare da yar aiken data ce musu ita cousin din su Hassan ce. “Mamana ita ce Hussainar Maman su yaya H1” ta fada proudly, kawai sai Ruqayyah taji yarinyar bata yi mata ba duk kuwa da cewa bata yi mata komai ba. Sumayya tace “hmmm. Lallai kice akwai twins da yawa a wannan family din” ai kuwa kamar ta tsokano Magana sai ta fara lissafa mata su, gidan Aunty wance gidan gwoggo wance gidan auncle wane, Sumayya tace “haka kuke da yawa ashe? Lallai Ruqayyah kina da aiki a gaban ki. Duk sai kinyi kokari kin gane su saboda gaba” yarinyar tace “au wai ba ke ce yayar tamu ba? Ni fa ba gane ku nake yi ba” Ruqayyah tace “in dai kika yi magana kika ji an cika miki kunne da surutu to ba ni bace ba” Sumayya tace “in dai kika yi magana kika ji an baki amsa gida daya an dauke kai to ita ce yayar taki” duk sukayi dariya. Suka wuce ta gaban gidan Hussain sannan suka shiga wani dan karamin gate da akayi a tsakanin gidajen guda niyu yadda ba sai an zagaya ta babban gate ba, suka shiga main gidan su Hassan, inda Aunty take.

Suna shiga suka tarar gidan a cike da yan uwa, ana ta hayaniya. Nan da nan aka fara drama din banbance Ruqayyah da Sumayya, a karshe har sai da aka kira Hassan a waya aka ce ya fadi bambanci guda biyar. Nan ya fara jero musu “nutsuwa, kunya……” Suka katse shi, physical banbanci muke so kafada mana ba abstract ba” yayi dariya yace “let me close my eyes and think. Kunga na farko fuskar Ruqayyah tafi ta Sumayya tsaho, idanuwan Ruqayyah kwantattu ne na Sumayya kuma zagayayyu ne, lips dinsu ma ba iri daya bane, na Ruqayyah sunfi siranta na Sumayya sunfi kauri. Sannan Sumayya ta danfi Ruqayyah kiba kadanita kuma Ruqayyah tadan fi ta tsaho kadan. Hassana ta bata da yawan magana sosai, tana dai da yawan murmushi, Sumayya kuma tana dariya as much as she talks”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button