AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Katse wayar tayi tana kokarin gyara zamanta da sauri ya juya ganin saura kaɗan ta kamashi yana kallonta sunɗan yi tafiya mai nisa sannan tacewa mai taxi ɗin anan zan sauƙa, cikin cool voice nashi ya” nima anan zan sauƙa ” da hanzari ta juyo jin muryar shi shikuma ya juya yana kallon waje hakan yasa iya gefen fuskar shi da ya ƙawatu da lallausan saje kawai ta samu damar kallo sauƙa tayi ta miƙawa mai taxi ɗin kuɗi ta fara takawa da ƙafa zuwa inda ƙofar shiga santar nasu ya ke kasancewar mota bata shiga har ciki domin hanyar yaɗan matse da ɗan sauri sauri take tafiya jin alamun ana binta a baya, ganin ta ƙara sauri ne yasashi ƙarawa shima, gudu ta fara sosai kan kace me ta afka get ɗin shiga santar kamar walƙiya, ɗan murmushi yayi ya ƙara sauri sosai shima, laɓewa tayi a bayan ƙofar haɗi da riƙe wani muƙeƙen sanda da ta gani a wurin, a hankali yasa ƙafar shi guda cikin wurin yana ƙare masa kallo ɗayar kadar ya jefo ya fara takawa taku ɗaya ,biyu, ana uku yaji sauƙar sanda a kafarshi unexpected hakan yasa shi kwala ihu haɗi da riƙe kafar. da sauri ta fito daga maɓoyar ta, tana ƙarewa kyakyawar fuskar shi kallo tace” gobe ma ka ƙara bin wata a kan hanya idan ka ganta sai ka samu mai raba ka da ƙafar gaba ɗaya,

Kallonta yayi da sanyin murya yace’kinji min ciwo fa duba ki gani har jini yana fita ashe soyayya yana zama rikici? “

“soyayya kuma?”

Yace “of course soyayya kallo ɗaya na miki naji kin sace ni gaba ɗaya hakan yasa nayi tattaki domin tabbatar da zuciya ta ta samu muradinta” suheer tayi dariya wanda dimples nata suka lotsa tace soyayya manya” to ni bana soyayya” miƙo mata hannu yayi gami karkatar da wuya yace to tunda bakya soyayya bani zuciya ta”, wani dariyan dake narkar dashi ta kuma ta na nuna kanta tace ” zuciyar ka kuma? a wurina “? yace ehh zuciya ta wanda kika yi nasarar sacewa daga shigar ki taxi zuwa yanzu. ni sunana HABEEB, amma zanyi matuƙar farin ciki inkika ƙirani da HABEEBI.

Bayan wata ɗaya a cikin wata ɗayar nan abubuwa daya wa sun faru ciki har da soyayya da ta fara nisa tsakanin habeeb da suheer, sannan a ɓangaren fareeda jaruma kuwa suna ta ƙoƙarin itada anty hafsa na ganin ta samu fitowa a wani shiri mai dogon zango wanda za’a fara ɗauka kuma RASHEED ne tauraro don haka kullum suna kan hanya cikin nasara kuma ta samu da ma, yanzu haka suna ƙoƙarin fara audition cikin kwana biyu masu zuwa. yauma kamar kullum habeeb ne zaune da suheer a compound nasu suna hira cikin nishaɗi da jin daɗi.

AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT KANO……

A hankali jirgin ya gama daidaita tsayuwar shi a kan doron ƙasa, bayan kwashe awanni yana shawagi a sararin subhana, jirgin ya taso ne daga kasar NEWZEALAND. maƙare da fasinjoji a hankali yake tako matattakalar jirgin yana sauƙowa kamar mai counting step nashi, haka yake tafiya kamar shikaɗai ne a kai ba wasu a bayanshi.wani sassanyan numfashi ya sauƙe gami da lumshe kyawawan idanunshi bayan ya shaƙi iskar kasar shi ta gado.

Fari ne ƙal, yana da tsawo sosai domin irinsu ne ake kira da giants yana da faffaɗan kirji dakuma kakkarfan jiki, kai da ka ganshi kasan yana bawa jikinshi hakkinsa ta hanyar exercise.sanye yake da wasu kananan kaya waɗanda suka yi matuƙar dacewa da jikinshi wando da riga da kuma p-cap, a gaban p-cap din anyi shape na star da zallar gwal, sai kuma wasu shegun sneakers hannunshi na hagu ɗauke da agogo da kuma zobe a yatsar shi na tsakiya dukkansu na diamond ne, yayinda hannunshi na dama ke daure da wani ɗan chain wanda kallo ɗaya zaka mishi ka fahimci da gwal aka ƙerashi, a kiyaste bazai haura shekaru 32 ba, duk inda ɗan gayu yakai to wannan ya wuce.

A raina nace woww ko waye wannan?

Ɗan juyawa yayi ya kalli wanda ya iso kusa dashi fuska a murtuƙe kamar wanda baitaɓa sanin wata kalma mai suna dariya ba , yace” what the hell buba me waɗannan sukeyi anan ya faɗa yana nuna taron yan jaridar dake wurin, bansanar da cewa kar wanda yasan da dawowa ta ayau ba? da rawan jiki buba wanda yakasance p.a nshine yace sorry boss amma ba wanda yasan da dawowar ka daga bakina saidai ko daga wani wurin, mtsssssw yaja wani dogon tsaki yace sai kaji dasu idan ka gama sai ka biyoni ya faɗa yana tafiya toward direction ɗin wata arniyar marcedes benz baƙa wuluk sai sheki take, da sauri wani ya fito yana ƙoƙarin buɗe mishi kofar baya ganin cincirindon yan jaridar ta tinkarosu, ɗaga mishi hannu yayi tare da buɗe front seat ya shiga yana miƙa mishi hannu alamar ya bashi makulli, miƙa mishi makullin yayi, domin ya fahimci yau boss shizai tuƙa kanshi kenan lokaci da dama yakanyi hakan idan yana cikin bacin rai.

Buba p.a ne yaba yan jaridar hakuri da cewa yau boss ya gaji da yawa.

wasu yan mata ne su biyu zaune a wurin suna jiran lokacin tashin jirginsu yayi dayar ta kalli ta kusa da ita tace wooww ƙawata waye kuma wannan, lan ajiyar zuciya tayi tace ” bakisan wannan ba? koda shike ina zaki sanshi keda baki cikakken sati inkinzo kuma sai ki dau shekara baki zoba, wannan shine RASHEED AHMAD MATAWALLE, Fittaccen jarumi wanda tauraronsa take haskawa, kuma marubuci, sannan mai shiryawa da daukar nauyi a masana’antar shirya fina finai ta KALLOWOOD. Sannan uwa uba shine mamalakin kantin nan na saida gwalagwalai mai suna R.A.M AND CO. GOLD, nasan kinsanshi baza’a rasa branch nashi a kasar da zaki koma ba domin ya mamaye duniya a ƙananan shekarunsa, sai dai masifaffen girman kaine dashi ga wulakanci amma duk da haka mata har kaimishi kansu suke amma ko kallo basu isheshiba. tace uhmm ke kuwa ba dole yayi girman kai ba kinga yadda ya haɗu kuwa?.

Da mugun speed Rasheed yaja motar yabar cikin airport ɗin ya hau kwalta yana ta sharara gudu tamkar nashine shi kaɗai.

Ɗan kallon suheer habeeb yayi bayan ya miƙe da niyyar tafiya yace”gimbiya ta babu rakiya ne?” irin dariyar da yake matuƙar so ta mishi sannan tace ” kaidai daɗi gaskiya kodai kodai” dariya yagi shima kana yace “ai ke ɗinne bana gajiya da kallonki wai meye sirrinne?

suna tafiya suke hirar har suka fito waje kasancewar a bakin kwalta gidan yake, kawai ya tsaya da niyyar tsaida abun hawa ya tafi domin baizo da mashin nashi ba yau, tsaye yake yana koƙarin tsaida taxi a gefe guda kuma yana ɗagawa suheer hannu alamun baibai itama tana ɗaga mishi da murmushi saman fuskar ta basuyi aune ba kawai suka ji wani wawan cin taya lokaci ɗaya kuma habeeb yayi sama sama ya dawo ƙasa timmm akan kwalta take jini ya ɓalle masa a ka, gyara hancin baka wuluk ɗin marcedes benz ɗin Rasheed yayi sannan ya kara yin ribas ya miƙe yaci gaba da gudu akan kwalta din kana ya sauƙe tinted glass ɗin motar ya sako hannun shi yayi wa mutanen da suka fara taruwa a wurin zagi irinna turawa, karaf akan idanun …….

TOHFA MASU KARATU ANZO WAJEN.

Ga dai Rasheed da kalan nashi halin, ga kuma jaruma fareeda a gefe ga kuma Suheer ta faɗo tsakiyar su rana tsaka.
A daure a ringa sharhi, sharhinku shi zai ƙara min karsashi. ONE LUV GUYS.
????????????AUREN FANSA????????????

BOOK ONE

TSARA LABARI DA RUBUTAWA

ASMA’U MAI ANGUWA
Ummu Fadeela.
Wnn shine wassap group namu kuyi joining????

https://chat.whatsapp.com/H75JKgUyzIuCXKhQCMfBO5

Page 20.

…. Zuro hannunshi yayi ta cikin bakin glass din motar da ya sauke hadi da ware dogayen yatsunshi biyu ya musu zagi irin na turawa, karaff akan idanun Suheer wacce tabi nomban motar da kallo ganin da gaske mamallakin motar guduwa yake ba gyara parking ba. Don ita duk tunanin ta zai gyara parking ne ya fito, kallo daya kuwa ta samu damar kwashe lambobin dake jikin plate din motar, Kafun ta karaso wurin da sassarfa tana kallon yadda mutane suka rufu akan habeeb wanda ba alamun numfashi a tattare dashi. Kowa a wurin yana tofa albarkacin bakinshi yayinda masu waya suke ta dauka domin baza wa duniya , masu karfin halin wurinne suka ciccibi habeeb suka sa a mota da nufin kaishi asibiti duk da cewa yanayinshi ya nuna kamar baya da rai amma yakamata likita ya ganshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button