AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan wani lokaci alaji sama’ila ya ƙara kyallara ido a kan wata bafullatana mai kawo tallan nono garin goruba, mai suna mallejo, ya aurota, ashe da niyyan damfara ta shigo gidan tana ta plan na yadda zata kwashi arziki ta yi gaba wata rana Allah ya tona mata asiri, domin kuwa wata rana alaji ya shigo ɗakinta ba tare da ta sani ba yaji ta tana waya da kawar ta na yadda zasu yi, bai jira jin wani abu ba ya mata saki uku ta tattara ta koma garinsu.

Saidai inda gizo ke saƙan ashe lokaci da ya sake ta, tana da juna biyu na yan makwanni ba tare da ita ma kanta ta sani ba, haka ta je tayi ta renon cikinta.

A ɓangaren alaji kuma wani auren ya kuma nema na wata yarinya dake gidan mai gari, ADAMA yarinya ce kyakyawa fara sol dan har wani yellow take tsabar hasken fatar ta kallo ɗaya zaka mata ka fahimci balarabiya ce.marainiya ce ita ba uwa ba uba, kuma ba wanda ta sani a Nigeria sannan bata da yanda zatayi ta koma kasar su, koda ace ta koma ma ba yadda zata gane danginta domin tun tana karama suka bar kasar,

Asalinsu larabawan morocco ne babanta makiyayin raƙuma ne ya shigo nigeria ne da niyyan neman yar uwarshi da wani bawan Allah ya auro daga can morocco, amma tsawon shekaru bataje gida ba kuma ba wanda yasan mutumin ɗan ina ne, saidai a hanyar su ta zuwa ya haɗu da yan fashin daji a kusa da kamaru suka kwace duk wani abu daya mallaka da kyar ya tsira da ranshi da matar shi da kuma yarsu guda ɗaya, rashin kuɗin komawa gida yasa su yada zango a wani gari dake tsakanin nigeria da kamaru, a haka ya fara neman kuɗi har Allah ya jefoshi ƙauyen goruba, ganin irin ni’iman da Allah ya yiwa darinne yasa shi zama har ya fara noma ba laifi kuma yana samun na rufin asiri, saidai ya kasa samun ƙuɗin komawa kasar su kuma ya rasa ta inda zai fara neman yar uwarshi kasancewar komai yanzu sai kana da hanya da kuma masu gidan rana.

A haka har adama ta fara girma ta kai shekara goma sha huɗu a duniya, wani shekara annobar amai da gudawa ya ɓarke a garin , mutane da dama sun riga mu gidan gaskiya ciki har da iyayen adama, wannan gasa riƙon adama ya dawo hannun mai gari, saidah kafun rasuwar iyayenta babanta ya bata wani zobe wanda ya shaida mata zai taimaka mata wurin gano yar uwar shi da kuma danginsu. yanzu shekara uku kenan da faruwar lamarin adama tana da shekaru goma sha bakwai alaji samaila yazo neman aurenta.

Nisawa mai gari yayi kana ya dubi alaji samaila yace” wani hanzari ba gudu ba sarkin noma kasan dai yarinyar marainiya ce ba uwa ba uba kuma ba wanda yasan inda danginta suke,” alaji yana gyaɗa kai yace” duk nasan wannan mai gari Insha Allah zamu riƙe amana,” mai gari ya kaɗa kai alamun gamsuwa da bayaninshi yana ɗan murmushi kuma yace ” to gadai yar uwar ta nan zaune uwani mizai hana ka haɗa su ka aura lokaci guda, tunda ai gida bai koshi ba ba’akai dawa ba, (Uwani ɗiyar mai gari ce yanzu haka tana da shekaru ashirin da biyar amma bata taba aure ba abun yana damun iyayenta sosai amma ba yadda suka iya.)

Alaji yace” a yi haka ranka ya daɗe ” mai gari yace ” ba komai duk yi wa kaine” wannan shine silan auren adama da uwani gidan Alaji samaila sarkin noman goruba .

Bayan wattani da auren suna zaman lafiya sosai domin adama bata da hayaniya, tabawa kuma bata da sa ido, uwani ne mai ɗan guntun munafurci itama bata ga fuska ba, so zamannasu saisa saisa suke yinshi.

Wata rana suna zaune, sai ga mallejo kamar an jefota ta shigo da jaririya a hannunta , da a ka kira alaji daga fadar sa yaga mallejo da jaririya ba ƙaramin kaɗuwa yayi ba, ta aje musu jaririyar a ƙasa kan tabarma, tace” ga ɗiyar ka nan na kawo maka anyi suna jiya ansaka mata suna fareeda, wani irin ashar alaji samaila ya kawo yalabta yace ƙarya take ahi bashi da wata ƴa baisan wannan zance ba,

Ba karamar rigima aka sha ba kafun ya karɓi yarinyar don saida ta kaisu ga zuwa kotu, daga karshe akayi DNA test aka tabbatar ɗiyar shi ce. ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba, ba shiri suka rankaya wurin boka shida bala, boka ya tabbatar musu da tunda an haife ta da zaran ta cika shekara biyar a duniya ya kawo ta zai bawa dodon tsafinsu.

Wannan shine silar ƙiyayyar da ke tsakanin alaji samaila da diyar sa fareeda, shi yana ganinta a matsayin cewa ba ɗiyar shi bace.

A nan tsakar gida aka barta sai adama ce taji tausayin yarinyar ta ɗauke ta da haka riƙonta ya koma hannunta Allah kuma ya raya ta da koko ba tare da nonon uwa ba shisa har yau take ganin adama ce amminta kamar yadda take ƙiranta bata taɓa sanin ba ita ta haife ta ba.har tsawon shekara uku ba wacce ta samu ciki tsakanin adama da uwani abun yana damun alaji kullum sai ya musu gori, wani tafiyar da yayi duba gidan gonar sa ne ya daɗe a can da ya dawo ya samu adama da ciki, Wannan kenan.

    ......  CIGABAN     LABARI.....

A hankali ta rufe idanunta lokacin da motar su ta harba kan titi, tana kallon bishiyoyin dake wucewa shuuuu tana tunanin rayuwa, fareeda ne ta fara kuka yunwa tana cewa ” ammi zanci abinci” lallashinta adama ta hauyi da cewa ta bari sai sun iso amma kamar daɗa tunzura ta take yi, ganin haka wata mata dake kusa dasu ta ciro biscuit a jakarta ra miƙawa fareeda, take ta karba ta hau cin abunta, sai wurin karfe biyar na yammaci suka iso kano danma suntsaya cin abinci da sallah a hanya, duk sanda aka tsaya cin abinci kuwa adama kam sai yan idanuwa domin ba kudi a hannunta sai ɗari da hamsin wannan baiwar Allahn dake kusa da ita, ita take sammu su duk abunda ta saya.

Lokacin da suka sauƙa a kano baki adama ta sake domin bata taɓa ganin babban gari irin wannan ba a tsayin rayuwar ta ba inda ta sani sai ƙauyen goruba da mutanen cikinta. ganin da tayi kowa yana kama gabansa ne yasa ta kamo hannun fareeda suka fita tashar ba tare da tasaan inda ta nufa ba, tafiya kawai sukeyi a gefen dogon kwaltan mai cike da cunkoson ababen hawa, har magriba ya cimma su suna tafiya akan titin, ga haske tarwai ta ko ina kai kace rana ne. kukan fareeda ne ya dawor da adama hayyacinta na tunanin inda zasu nufa ga wani uban yunwar da ke kwakulanta, abunda ke cikinta sai ball yake yi, yana alamta mata shima yana jin yunwa,.

Ta ɗan karkato kaɗan tace yayane mamana? kin gaji ko? gyaɗa mata kai fareeda tayi. tace ” yi shirru abunki saura kaɗan mu iso kinji, Allah bazai barmu haka ba yasan yadda zaiyi damu Insha Allah” cikin muryar ta na yara tace ” inajin yunwa zanci abinci? ɗan tsayawa kaɗan adama tayi , sai kuma ta ja hannunta zuwa cikin wasu rukunen shaguna da ta gani a wurin, shago ɗaya ta shiga ta kunto dari da hamsin ɗin dake kulle a bakin zaninta ta miƙawa mai shagon, karba yayi yace me za’a baki hajiya, ta buɗe bakinta wanda leɓunanta sun bushe kyamas tsabar wahala da yunwa tace “abunda zamu ci ” kallonta yayi sosai sannan yadau leda ya zuba mata cincin dake cikin wani farin bucket guda biyar a leda sai ruwan pure water guda biyu, ta amsa suka fito, ɗan gefen shagon suka samu suka zauna ta buɗe ledan ta ɗau cincin ɗaya ta turawa fareeda sauran gabanta haɗi da miƙa mata ruwa guda ɗaya, ta koma gefe ta zauna tana cin wanda ta ɗauka,

Guda biyu fareda ta cinye taji ta koshi kuma taɗau ruwa tasha, wani almajiri ta gani zaune yana ta kallonta suna haɗa ido ya miƙo mata hannu haɗe da rausayar da wuya alamar ta ɗammishi ledan ta ɗauka ta mika mishi da sauran ruwan karaf akan idon adama da ta miƙe da niyyar karawa domin juyin da cikinta yake yi bayan ta cinye guda ɗaya da ta ɗauka, da sauri ta matso ta fara faɗa baki da hankali ne zaki kyautar alhali muma bamu ci ba faɗa take yi sosai don har idonta yana rufewa fareeda dai na zaune dai yan idanu take zarewa domin bata taɓa ganin amminta tayi fushi tana masifa haka ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button