AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Balki ne ta kira shi a karo na uku tun bayan daya kafeta da ido . firgigit ya kalleta tace “alaji tunanin me kake yi haka ina ta magana baka jina”

Yace” am a’a na’am me kika faɗa?duk ya ruɗe tace “vewa nayi me wannan a hannunka ? kuma me kazo ka tasa ni gaba da kallo kamar mai min kallon bankwana? a ɗan tsorace ya yace “haba balki wane irinkallon bankwana kuma? kinga taso wani magani na amso miki na mayu, kinsan ku masu juna sai an haɗa da maganin idi domin kar suke kallon ku, ” ya karishe gami da ajiye kofin gaban madubi kana ya ciro maganin daga cikin babbar rigarshi , damko mgnin mai ɗan yawa yayi da yatsunshi bayan ya kwance ledar ya barbaɗa a kan kunun sannan ya ɗau cokali ya jujjuya kunun ya matsi kusa da ita yace” kinga maza taso kisha tun yana da duminshi ” yana miƙa mata kofin da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma yana ƙoƙarin taimaka mata ta tashi.

Ba musu ta kama hannun ta tashi, a hankali ta zauna jin zuciyar ta na bugawa da karfi , gyara mata zama yayi sannan ya miko mata kofin yana cewa” shanya kiban kofin yanzu yanzu”

Kirjinta ne ya tsananta bugu fat fat fat, yayin da tayi arba da bakin kunun dake cikin kofin ba kyan gani, kai ta juya tace “alaji bazan iya sha ba amai zanyi kuma fa ban daɗe da cin abinci ba bana jin yunwa ni kam.

Ido ya zaro mata cikin faɗa yace ” shanye maza ki bani kofin wannan maganine ba abinci ba kina dai ganin yadda mayu suka yi yawa a garinnan duk inda ka motsa sune, ku mata dama bakusan inda ke muku ciwo ba, sai abu ya baci kuzo kuna kuka da faɗin ba’a kula da ku, ya faɗa cike da borin kunya, karbi ki shanye kiban kofin.

Hannu biyu ta sa ta amshi kofin takai baki haɗi da rumtse idanunta da karfi, wani wawan numfashi yaja wanda yasa ta buɗe idanu da sauri tace “lafiya kam”?
Lafiya lau ya bata amsa. sake rufe idanu tayi ta kai kofin bakinta ta rike numfashinta gam, domin harga Allah kunun wari ya ke mata. saida ta sha fiye da rabin kunun sannan ta sauƙe kofin, ido ya zuba mata haɗe da cewa shanye mana ,mema ya rage shanye kawai ki karashe ladanki ” fuska ta kwabe kamar zata yi kuka tace ” Allah na koshi zanyi amai fa ” da sauri ya amshi kofin ya aje gaban madubi, ya kuma dawowa kusa da ita ya kama ta ya kwantar da ita sannan ya ringa shafa bayanta gently yana faɗin kar kiyi amai kinjiko, ganin da yayi tana ta haɗa uban gumi ne yasa shi daukan abun firfita yana fifita ta, lokaci kaɗan bacci mai ɗan karen daɗi ya kwasheta, yana ta zaune wurin har tsawon minti goma baiga wani alamun zubewar ciki ba hakan yasa ya miƙe da nufin zuwa watsa ruwa matuƙar ya dawo ba wani alama to dole ne ya ƙara mata wani. har ya iso bakin kofa , kuma me ya tuna ya dawo cikin ɗakin ya gyara mata kwanciya yadda zataji dadin domin duk a takure take, ya juya ya ɗau sauran kunun dake kofin ya fita ya zubar sannan ya wanke kofin tas.

Ido suka haɗa da tabawa da ke zaune inda ya barta tace” lafiya kuwa alaji” yace ehh to kusan dai lafiyar amma balki bata ji daɗi ba shisa na karɓo mata magani tasha, yanzu haka ma ta samu bacci. cike da jimami tabawa tace ashha Allah ya bata lafiya kasan masu juna sai a hankali dama . shiyasa yau banga gilmawarta ba ashe tun safe.ameen yace yana nufar hanyar ɗakinshi.

Sanda balki ta kwashe awa ɗaya da rabi tana bacci, a cikin awa da rabinnan kuwa alaji ya shigo duba ta ya kusan sau goma har hakan yaba tabawa dake aikace aikace tsakar gida mamaki.

Cikin bacci balki taji kamar a na tuƙa tuwo a cikin cikinta a tsorace ta farka jin ciwo sai gaba gaba yake, cikin matuƙar azaba ta yunkura da nufin tashi zaune amma hakan ya gagareta domin wani irin azaba ta keji marar misali, ga wani tuƙawa da cikinta keyi kamar ansa injin markaɗe ana markaɗa kayan cikinta . cikin karfin hali ta ƙara yunƙurin mikewa, wannan karon kam ji tayi kamar ansa scissors andatse duk wani jijiya dake jikinta hakan yasa ta danne bedside da sauran karfin da ya rage mata ta miƙe luuu wani jiri ya kwasheta ta tafi gaba gaba ta bugu da jikin mirror nta gab ta zube a ƙasa ,INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN. ta ambata daidai lokacin da taji wani ruwa mai dumi yana bin ƙafafunta take komai na jikinta ya sake komai ya tsaya mata chak kamar andauke wuta. da gudu tabawa ta shigo dakin jin karan faɗuwan abu da kuma salatin balki. chabak taji ta tsunduma kafarta cikin………

LIKE COMMENT AND SHARE

Masoya AUREN FANSA ina kaunar ku lodi lodi, kubini a hankali domin ba’a fara tafiyarba. ONE LOVE FANS.
Bismillahir Rahmanir-Raheem.

????????????AUREN FANSA????????????

BOOK ONE

        NA 

ASMA’U MAI ANGUWA

  (Ummu Fadeela)

Wannan labari kirƙirarren labari ne idan yayi kama da rayuwarki/ka to arashi ne.

Masoya littafin auren fansa ina alfahari daku, domin ba wai auren fansa kawai kuke so ba a’a har da Ummu fadeela, ina fatan alherin Allah yakai muku duk inda kuke ILVYSM guys,???? ku cigaba da nuna ƙauna wa littafin.????

TYPING????

Page 8 & 9

……Chabak taji ta taka abu mai yauƙi, wanda santsin yaɗe beta saura kiris ta faɗi, tayi saurin riƙe bango kana ta kai dubanta kasa don son ganin me ta taka, ido ta zaro cikin firgici ganin jini ne ke malale tsakar ɗakin tamkar an kunna famfo, ido tabi jinin dashi don son fahimtar daga inda yake fitowa aiko tayi mummunan gani domin balki ta hango kwance cikin jini ba alamar rai tattare da ita,.

A zabure ta karisa dakin haɗi da kwala ihun da kiran sunanta, balki! balki! meya sameki? tashi mana, duk ta rikice a guje ta kuma nufar waje domin kiran alaji, karap suka yi karo da shi yana kokarin shigowa cikin sauri domin jiyo ihun tabawa da yayi tana kiran sunan balki.

Cikin firgici tace” alaji balk….jin….balki jinii ..balki” duk ta rikice, ba tare da ya tsaya jin abunda take faɗa ba ya afka ɗakin gaba ɗaya ya tsorata da halin da ya ga balki a ciki, bai tsammaci abun zaikai haka ba, dabarar yayyafa mata ruwa ne yazo mishi, da sauri ya debo ruwa mai sanyi ya kwara mata a fuska amma shiru ko gezau bata yi ba, tabawa dake sheshekar kuka ne tace” alaji mutafi asibiti yafi, dubi yadda take zubar da jini fa”,

Cikin rashin sanin abunyi ya nufi waje domin fidda abun hawa, fitar shi keda wuya balki ta fara sauke wani irin wahalallen numfashi, a hankali ta buɗe idanunta da suka mata nauyi ta sauke su kan tabawa da ke zaune kusa da ita tana kuka , cikin muryar dake bayyana tsananin wahalan da ta kesha tace “yaya tabawa ” da sauri tabawa ta juyokana ta matso kusa da ita “yaya tabawa zan sha ruwa” ta kuma faɗa murya a disashe.

Ruwan ta ɗebo takawo ta tallabi kanta ta fara bata baifi kurbi uku tayi ba, ta fa fara wani irin azababben tari, duk tarin da tayi jini ne ke sauka ta kasanta dunƙule dunƙule take dakin ya kuma cika da jini tamkar an yanka bujumin sa,

Hakan kuwa yayi daidai da shigowar alaji sama’ila wanda tashin hankali ke rubuce saman fuskar sa yana faɗin ” tabawa kamata mu……sauran maganan maƙalewa yayi saman lips nashi ganin halin da suke ciki, karfin halin karasowa yayi ya zubawa jinin dake ɗiɗɗikowa duk tarin da tayi ido , kirjinshi na bugawa da sauri sauri, tarinne ya lafa sai kuma ta fara wani irin shakuwa harshenta na sarkewa ta ɗago kai da kyar ta kafe alaji da idanu, a hankali ta furta kalmar shahada, tana kaiwa karshe jikinta ya saki idanunta dake kallon fuskar sama’ila suka kafe chakk. Inna lillahi wa’inna ilaihi raji’un.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button