AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da hanzari suheer ta matsar da kanta tana tunanin anya wannan rasheed ne kuwa kodai gizo idanunta ke mata, indai ta tabbata shine to tabbas akwai abunda yake kullawa. To menene wannan? bata da mai bata amsa dan haka taja bakinta tayi shiru.

Buba ne ya matso kusa da rasheed yace “boss iam confused, bayan wannan duka what do you exactly want?.

Karkata kai rasheed yayi yace, ” buba nima wannan tambayar nake so inje gida inyiwa kaina, Rasheed what do you really want? ya fada kamar yana tambayar kanshi.

Buba ya kuma cewa amma boss, kazo wurinnane da niyyar hana dina dinnan, gashi kana tsaye kuma al’amura sai tafiya sukeyi kuma kamar farin ciki kake yi da hakan.”

Tabe baki yayi yace “sam sam sam bana farin ciki, duba kaga, ya nuna mashi suheer dake murmushi fareeda na rankwafe a kanta kome take fada mata oho, yace gacan mai farin ciki, buba ya kumayin sauri yace “amma dole tayi farin ciki ai tunda yau ranarta ne.”

Rasheed yace “tabbas shiyasa na barta tayi farin ciki kafun gobe taji mummunan labarin da zai tarwatsa ta, hawaye zai ringa sauka akan wannan kyakyawar fuskar tata tamkar yadda ruwan sama mai zuba kamar da bakin kwarya ke saukowa daga sama, wannan shine kudirin rasheed, dan haka ne na barta ta more na yau kawai.

Mc ne ya kara kiran amarya da ango su fito tsakiyar fili, suheer gaba daya ta gaji da wannan kiraye kirayen da ake musu, haka dai ta mike suka fito suka tsaya, ita ba rawar take ba don kunya takeji amma kuma dole ta fito ta tsaya, bayan sun fito mc ya nemi uwar ango da ta fito ta nuna tata bajintar, aikuwa kamar jira asabe take yi ta bude jakar ta tadau sabbin yan dari bibbiyu dauri biyu ta fito. dj ne ya sake wakar uwar biki, nan asabe ta fara mannawa habeeb yan dari bibbiyunnan ko takan suheer bata bi ba, kamar batasan da wanzuwarta bama a wurin, wasu kawayen ammi biyu ne suka taso suma suka fara yiwa amarya liki, take wurin ya dau dumi yan mata da samari suna ta cashewa,

Mikawa buba hannu rasheed yayi take buba da ya gane abunda yake nufi ya fitar da mint na dollars har guda uku ya mika mishi.

Wurin da suke rawar Rasheed ya nufa cikin takun kasaita, ruwan daloli ya fara yiwa suheer wacce mamaki yake kokarin kashewa a wurin, asabe ne ta juyo da dan sauran canjin da ya rage a hannunta da baifi dari takwas ba da niyyan jefawa amarya, cikin matukar dimaucewa ta zaro ido ,tana mamakin me ya keyi anan, sake baki tayi kawai a ranta tace “what is he doing here”? gaba daya ta rikice ga wani kalan kudi da taga yake watsawa suheer kai da kagani kasan wannan kudaden turai ne don baiyi kama da kudin yankinmu ba, tsabar rikicewa bata san ta taka bayan rigar suheer dake jan kasa ba,….. a hankali take matsawa gefe rasheed ko yana kara binta yana mata yayyafin kudi, yayinda asabe ke tsaye kikam kamar statue ta danne harshen rigar tata da duk kafafunta biyu ba tare da tasan tayi hakan ba, taku biyu ta kara da niyyar kara matsawa tayi taga taga zata fadi sakamakon rigar ta da bai biyota ba, cikin zafin nama rasheed ya taro ta ta fada kan faffadan kirjinshi, tightly ya rike ta,….da sauri photographern ya kara gyara rikon da yayiwa kyamerarsa yana cigaba da daukan su.

Kokarin kwace kanta ta shiga yi hakan yasa ya saketa, wani jiri ne ya kuma dibar ta ta kara tafiya luuu zata fadi…..azamar tarota ya kuma yi, ta fado kan damtsen hannunshi, daya hannun yasa ya zagaye waist nata dashi, yayinda nata hannun ya samu masauki akan kirjinshi, dan rankwafowa yayi kanta suka zubawa juna ido………

To uwar khairat ga sakonki , nace aniyar moda tabi randa, bazan biye miki ba mu raba hali dake gaban surukai, haba dan adam bai isa ya kwanta rashin lafiya ba saiki wani ce ko ….ne to in kin manta in tuna miki uncle ASHRAF nawa watanshi shida cifff da sati daya ato, dan naga alama tsoron Allah yayi karanci a ranki, And zaki zone kimin bayani dallah dallah tunda Allah yayi ansallamoni ban wuce daga can ba.

My real fanss naga sakon addu’oinku ina godiya. My whatsapp people inaga oga bai san da wssap group ba shiyasa bai kai sanarwan can ba domin shi ya bawa yan fesbuk rahoto, kuyi manage da wnn, banson in stressing kaina da yawa kuma inkara koma wa asibiti domin gsky an karkade min file nawa mai kyau, saidai I thank God abun baiyi tsayi ba.

????????????Auren Fansa????????????

     By

Ummu Fadeela

Typing????

Book Two

Page 45/46.

……. Ido suka zubawa juna na tsawon lokaci, duk yadda taso janye nata idon domin ta mike daga jikinshi yaki bata daman hakan, a bangaren rasheed kuwa ya kasa sakinta ne sakamakon wani irin pulsing da yake ji a kasanshi tun fadowarta kan kirjinshi, tana matsawa daga jikinsa mutane zasu fahimci irin tazarcen da ya samu.

Rasheed was suprised that he got an eraction dan fadowar da yar yarinyar nan tayi a kanshi, tsaki yaja a ranshi “yanzu ya zanyi in fita a wurinnan a haka?” ya yiwa kanshi tambayar.

Fareeda ne ta iso wurin da dan sassarfa tun daga kan danne rigar suheer da asabe tayi, har zuwa kan faduwarta jikin rasheed fareeda ta gani, so tasan abun bawai intentionally ya faru ba, harda dan gudu ta hada tazo ta daga suheer daga jikin rasheed, tace “yallabai mun gode badan kaiba yau da anyi abun kunya amarya a kasa”,ko kallonta rasheed baiba ya nufi hanyan fita daga hall din cikin hanzari, baki buba ya bude galala ganin bakon al’amari a tattare da boss nashi, wani dariya yayi yace one one kenan , sai kuma ya rufe bakin da hannunshi da sauri yana dariya mara sauti.

Kallon suheer da jikinta keta mazari tun dazun fareeda tayi tace “sorry rabin jiki bakiji ciwo badai ko?” gyada kai tayi sai a lokacin habeeb ya juyo yana kallonsu da mamaki…..

Zama yayi cikin motar shi yana kokarin saisaita nutsuwar shi, da karfi ya bugi steering yace “bullshit wai har yar karamar yarinyar nan ta isa ta sani in……” sauran maganar tashi ce ta makale hango asabe da yayi tana ta leke ta cikin tinted glass din motar tashi, wani tsakin ya kuma ja a karo na ba adadi, glass din ya zuge, cikin fada fada yace ” ya akayi?” da dan rawan harshe asabe tace ranka ya dade ni sam ban fahimci abunda ya faru anan ba?”

Da masifa rasheed yace “wayace maki dole sai kin fahimci abinda ya faru”? ko kin manta cewa an damka miki miliyan goma ciff a hannunki?, to kawai malama ki koma gefe kiyi kallo, (ba kowanne kwai ne yake zama kaza ba, wani kwai din a cikin fry pan yake gama rayuwar shi ta hanyar soya shi a cinye, i hope u get it?” badon asabe ta fahimci hausar da yayi mata ba kawai ta gyada kai ta matsa gefe kafun yace bazai cika mata sauran kudinta ba, dan ita har ta fara hango kanta a dubai ta fara zuwa saro kaya irinna manyan hajiyoyi, da mugun speed yaja motar ya fice daga harabar wurin.

Allah ne ya kai rasheed gida lafiya, amma kam yasha zagi a kan hanya, isar shi gida da sassarfa ya haye sama inda yake hada steps bibbiyu har uku uku, baima ankara da ummien shi dake zaune palo tare da alhaji umar ba, da kallo ummie tabishi har ya bacewa ganinta.

Tundaga palo rasheed ya fara unbutonning din farar suit nashi, kana ya fizge necktie din da karfi kamar zai balla wuyarshi, yana kokarin zame wandonshi ya isa cikin daki duk akan gado ya watsardasu, sannan ya kwanta rub da ciki daga shi sai singlet da boxer yayinda ya mikar da hannunshi sosai kafafunshi ko suna lilo a kasa, ya dade kwance a haka still yaji bai masa ba, ga wani uban zufan da yake hadawa kamar ya hadiyi kunama, mikewa ya kuma yi ya wuce bathroom, ba tare da yabi takan bahon wanka ba kamar yadda ya saba kawai tsayuwa yayi a karkashin shower ya sakar wa kanshi ruwa kana ya dafa bango da duk hannunshi biyu, ruwan yana dukan bayanshi. tsawon lokaci ya dauka a haka kafun ya cire singlet nashi ya hada wani ruwa yayi wanka kana ya dauki babban towel ya daura ya kuma dauki karami yana goge kanshi zuwa fuskar shi dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button