AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lallabawa tayi tana kama gini har ta isa closet ta dau wani jallabiya mara nauyi ta zura kana ta dawo gadon ta kwanta hadi da jan duvet ta rufa har kanta tana rufe idanu da fatan samun saukin radadi da zogin da kasan ta ke mata, rasheed yana tsaye inda ta barshi tamkar statue, ba karamin bugu kalamanta suka mishi ba take yaji zazzabinsa yana kara hauhawa, a hankali ya dawo bakin gadon ya zauna ya kuma dafe kansa tsawon lokaci yana zaune ba tare ya san tunanin da yake ba, saukar numfashinta a hankali ne yasashi tabbatar da tayi bacci, kwanciya yayi gafenta shima yaja duvet din ya san da idanunta biyu hakan bazai taba faruwa ba, kusan minti goma da kwanciyar sa amma ba alamar bacci zai daukesa sai aikin yawo da maganganun ta suke masa a kwanya, lallabowa yayi kusa da ita ya kwanta bayan ya kashe wutar dakin gami da jawo ta cikin jikinsa ya manneta gam tamkar zai maida ta cikin kirjinsa kana ya ja musu duvet .

Suheer ne ta fara farkawa da misalin hudu da rabi na asuba, kasancewar rasheed bai samu bacci da wuri ba. Idanunta da taji tamkar an daura wa bulo inci tara take kokarin budewa amma ta kasa, Daga hannunta ta fara kokarin yi amma taji shi kamar an daure da igiyoyi masu karfin gaske, tayi dabaran motsa kafafunta shima jinshi tayi tamkar bishiyar gamjin da ya shimfida jijiyoyinsa a cikin kasa,wani irin kuka ta sake mai ban tausayi,wadda take ji gaba daya gidan ya dau sauyin kukan, amma a zahiri rasheed da take jikinsa ma ciki ciki yake jin kukan tsabar dashewar da muryarta yayi.

A hankali ya bude idanunsa shima yana jin ciwon kansa yana dawowa sabo fil dan jijjigata ya fara yi yana shafa jikinta da ya dume da zazzabi alamar lallashi amma kamar dada tunzurata yake yi, ganin bazata yi shiru ba gashi shima yana fama yasa shi lallabawa ya sauka gadon jiri na debarshi ya nufi bathroom da kyar ya iya yin wanka da ruwan zafi gami da dauro alwala zuwa lokacin an fara kiraye kirayen sallah,…Duk kokarin da yayi na tafiya masjid bayan ya zura jallabiya kasawa yayi dole anan yayi sallah, wani irin makyarkyata jikin suheer ya fara har hakoranta na karo da juna, Cikin rudani rasheed ya lalubo wayar sa yana furta “Ya Allah.” layin family dr nasu ya nema amma not reachable, hakan yasa ya karkata akalar kiran kan buba, bugu biyu ya dauka daga jin muryan rasheed yasan ba lafiya, “kazo da sauri zaka kaini asibiti” shine abunda ya fada ya yanke wayar, bayan kamar minti biyar ta tura kofar dakin cikin sa’a kuwa ya budu ummie ta shigo buba ne ya kirata ya sanar da ita rasheed ba lafiya hakan yasa ta shigo domin hankalinta ya kasa kwanciya.

Cikin sauri ta nufe shi ganin sa kwance akan pray mat,turus tayi ganin suheer dake jijjiga akan gado, da hanzari ta canza hanya zuwa kan ta, tana yaye duvet din da ta rufu dashi, hannu ta kai forehead dinta tajishi zau da zafi, Subhanallah ta fada, Aysha me ya sameki? tun yaushe kike kwance? shiru ba amsa sai faman karkarwa take.

Cikin karfin hali rasheed ya mike saidai abin mamaki duk yadda yaso hada idanu da ummie kasawa yayi domin wani irin kunyarta ya ke ji. Da murya kasa kasa yace “buba yana zuwa zamu tafi asibiti, na kira dr jameel amma bai wucewa”.

Da mamaki take kallonshi jin yayi responding maganarta yau, saidai yanayin muryar shi ya tsoratata, tace “son! what happen to both of you?.”

Kara sunkuyar da kanshi yayi, baice komai ba….Duk yadda ummie tayi dabaran ganin suheer ta taka kafarta zuwa wurin mota bayan isowar buba hakan gagararta yayi wani irin ciwo takeji ga cinyoyinta da suka budu dan ba karamin karfi yasa mata ba,. Da kyar da sudin goshi suheer taje motar tuni ummie ta fahimci abinda ya faru saidai ta rasa farin ciki zatayi ko bakin cikin yajiwa yar mutane ciwo,…Sosai likitar ta ringa masifa ganin irin barnar da rasheed yayi ba karamin ciwo yaji mata ba, dole aka bata gado dan sai anyi treating wajen sosai,a bangaren rasheed ma karin ruwa aka sama sa badon ya soba,…Kwana hudu cur suheer ta kwashe a asibitin kafun aka sallamosu, yayinda rasheed tun a ranar da ruwan ya kare ya dan samu karfin jiki aka sallameshi.Ummie ne tayi jinyarta na tsawon kwanaki hudun,zuwa lokacin tsanar da suheer ta yiwa rasheed ya ninku sau ba adadi, tanajin inda za abata bindiga ba abunda zai hana harbinshi, wani alwashin da tasha shine bazata kara koda kwana daya ba a gidan don haka ta shirya tsab tana jiran lokaci.

Misalin biyar na yamma ta mike takardar dake hannunta ta ajiye kan gado yadda mutum zai gani kana ta nufi hanyar fita daga ita sai kayan jikinta,tasan a lokacin ummie tana bangarenta, rasheed kuwa lokacin zaman shi a garden kenan…..Cikin nasara suheer ta bar gidan ba tare da kowa ya ganta ba bata samu matsala da mai gadi ba don ya santa don haka bai tsananta bincike ba…Bayan sallan maghrib rasheed ya shigo dakin da nufin dubata amma wayam babu ita babu alamarta, bayi ya bude nanma bata nan, ya juya da nufin shiga closet ko tana ciki yayi arba da farar papern da ke shimfide saman gado, da sassarfa ya dauko ya bude ya fara karanta content din,…Rasheed ya karanta papern ya kai sau bakwai amma ya kasa fahimtar me ta kunsa, tsabar yadda ya rude, sake karantawa yayi a karo na takwas harbawa zuciyar sa ta kara yi a karo na ba adadi cikin hanzari ya nufi kofa ya fita, lungu da sako na gidan ya ringa bi yana nemanta amma bai ganta ba,…Bugawar kirjinsa ne ya tsananta lokacinda mai gadi ke sanar masa ai tunda yamma ta fice daga gidan…Da tafiya mai kama da dan gudu gudu ya koma main house din direct part na ummie ya wuce abunda bai taba yiba tsawon rayuwar su a gidan, ummie na zaune a palonta saman kujera rike da carbi kawai taga mutum ya fado mata gabanta ya karaso ya zube kan guiwowinsa idanunsa sun kada sunyi jawur ga jijiyan kanshi da suka tashi rado rado bakinsa yana son yin magana amma ya kasa, ummie da yanayinsa yake bata tsoro kwana biyun nan ta kamo hannunsa duka biyu tace “me ya faru Son? mai neman kuka ne dama aka jefesa da kashin awaki kawai sai ya kifa kansa akan cinyarta cikin rawar murya mai cike da raunin zuciya yace. “Ummie, she’s left,ta tafi ta barni, wai bazata zauna dani ba kuma”.

????????AUREN~FANSA????????

Page 75 / 76

      By

Ummu Fadeela.

Suheer tayi tafiya mai nisan gaske akan kafarta kafun ta samu adaidaita tsabar shirun unguwar.Tafiyar da tayi ya dan motsa mata jikinta da dama ba gama warkewa yayi ba,…Cikin sanyin murya tacewa mai napep din “bari in shiga ciki in kawo maka kudinka”.

Ammi na zaune palo ta baza uban tagumi, tunanin lamido, suheer, da kuma maganganun da sukayi da ammar akan yanason hada zuriya da ita ne suka mata rubdugu.fareeda na kwance saman three seater tana bacci,tunda ta fara shan drugs da injections da ammar yayi prescribing mata ta fara dawowa normal self nata cikin ikon Allah,

Kwatsam suheer ta fado dakin kamar an jehota, da dan tsoro kadan ammi ta mike sai kuma ta isa wajenta da sauri ganin yadda yar tata ta rame tayi wani fayau da ita, rungumeta suheer tayi ta fashe da kuka, shafa bayanta ammi ta fara yi amma bata ce komai ba sai kirjinta dake sama da kasa, cikin muryar kuka tace “ammi banba dan sahu kudi ba”. Saketa ammi tayi ta nufi purse nata dake saman fridge ta fitar da dari biyar ta fita waje, sai a lokacin suheer ta lura da fareeda da ta tashi sakamakon kukan da taji, kureta da ido tayi ganin yadda ta rame kamar marar lafiya,calmly fareeda tace “Rabin jiki” dummm suheer taji a kunnenta yaushe rabon fareeda ta kira sunanta haka, “why are you crying?” ta kuma jeho mata tambayar, suheer bata yi wata wata ba taje ta rungume ta tana cewa “i missed you sweetheart” ta ci gaba da kuka, a haka ammi ta dawo ta same su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button