AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaba daya suheer bata fahimci zancenshi ba, cikin fushi tace “ya kamata ka sawa rubutun naka wasali ta yadda zan fahimce shi da kyau, duk da dai na hango akwai cin zarafi a ciki”. “Bravo” sannan yaci gaba so nake mu yi hadin guiwa wajen warware matsalar mu, dan jimmm yayi yana ta nanata abunda yake son fada a ranshi, zuwa can yayi karfin halin cewa, “ma’ana inason muyi auren yarjejeniya dake domin in dawor da martaba ta a idon duniya, wani irin dagowa suheer tayi kirjinta na dukan tara tara ta bude baki da niyyar fada mishi maganar da har ya mutu bazai manta da ita ba, amma sai maganar da ya cigaba dayi ya dakatar daita, diff”in kin amince ni kuma zan biya kudin aikin da za’a yiwa mahaifinki wanda yake between life and death, har naira miliyan arba’in, ciffff.

Zaro ido tayi kamar zasu fado kasa, take wasu hawaye masu dumi suka fara ambaliya a fuskarta, ba abunda take gani a idonta sai kawu lamido kwance akan gado kamar gawa, in badon life support mashine da aka makala masa yake aiki ba zaka dauka baya numfashi, tabbas zata iya yin koma menene domin samun saukin lamido mutumin da yadauke musu kewar uba, ya musu dukkan gatan da uba na gari yake yiwa yayanshi, takan tuna duk sanda anty hafsa ta mishi gorin aure saidai yayi dariya yace, ” (hafsatu kenan duk macen dana karo cikinku to tabbas zata raba min kan zuriya, ku kadai kun isheni rayuwa)wani kuka ne ya kwace mata tabbas mutumin da ya musu wnn yanzu ne lokacinda ya dace su saka mishi, sai kuma amminta abun alfaharinta gaba daya ta fita a hayyacinta na tunanin yadda zasu fitar da lamido a halin da yake ciki, ga uwa uba anty hafsa idan ka ganta kasan karfin hali kawai take yi, ga kuma sweetheart inna lillahi ta ambata tunawa da cewa ba namijin da fareeda ke so irin rasheed a rayuwarta, amincewa da kudurin rasheed means yaki tsakaninta da sweetheart, tabbas rayuwar ahalinta ya shiga garari, ga dama kuma ta samu saidai………Think suheer think, shine abunda kwakwalwarta ke fada mata.

Rasheed dai zuba mata ido yayi a ranshi yana mamakin saurin kuka irinna mata,… wani tunani ne ya fado mata, da sauri tace “why not kuyi yarjejeniyar da yayata fareeda, tunda dama akwai alaka a tsakaninku, dukda dai har yau baku fara daukan fim din tare ba kasancewar abubuwan da suka dinga faruwa. Kallon baki da hankali ya mata, zuwa lokacin ya riga da ya gama gundira da hirar, karfin hali kawai yake yi, bata sani bane kawai he is boiling inside, yana jin kukanda ya sata bai isheshi ba, yana son ya ganta cikin tashin hankalin da ya fi wadda take ciki yanzu, saita rasa sukuni kamar yadda tasa shi ya rasa nashi sukunin a lokacinda a ka sashi jail ta dalilinta.

Yamutsa fuska yayi yace “you need to back on your sense baby girl, aure da fareeda kara bata komai zaiyi, dake akamana bidiyon bada so called fareeda ba, dan haka na baki lokaci kije kiyi tunani, saidai ina miki tuni da mahaifinki baida isashshen lokaci, zaki iya tafiya, akwai mai jiranki a waje zai maida ki gida, idan kin yanke hukunci zaki iya sanar dani ya taso ya damka mata wani paper a hannu kana ya juya ya nufi daya daga cikin dakunan da suke jere a palon……….Har suheer ta iso gida tunanin maganganun rasheed kawai take yi, saidai ta kasa samun mafita, da zaran tsanar rasheed ya taso mata sai kuma hoton kawu lamido kwance jikinshi duk inji ya fado mata, Har direban ya sauke ta kofar gidansu bata san sun iso ba, saida ya mata magana kafun ta kama murfin motar ta fita.

Zaune ta ganshi ya zubawa motar da ta sauke ta ido kamar yau ya fara ganin mota, duk ya rame ya zabge shima kamar ba habeebinta dan gayu da kwalisa ba duk ya kare sai idanu, suma sunyi wani circle alamar ya kwanta rashin lafiya,

Habeeb, ba shakka tunda asabe ta dauko shi daga gidanshi aka samu ya dawo hayyacinshi suheer ne ta fado mishi arai ko wanne hali take ciki? hakanne yasa ya faki idon mamanshi ya fito zuwa nan, ya dade zaune bai samu dan aike ba, sai gashi kamar daga sama yaga mota ta tsaya suheer ta fito daga ciki, ganin habeebi ya kara dagula mata lissafi, take yanayin saukar numfashinta ya sauya, saidai ko ba komai taji dadin ganinshi domin ta sanar dashi wannan bidiyon karya ne.

Bata san ya iso inda take ba sai saukar muryarshi mai cike da rauni taji a kusa da ita, “yace masoyiya nasan karya ne, nasan bazaki aikata hakan ba, shiyasa nayi iya kokari na in fahimtar dasu amma sun kasa ganewa, sunyi nasarar raba ni dake suheer, sun raba ni da ruhi na, yanzu gangar jikina ce kawai ke tafiya amma kece ruhina, mama tace sai inzaba ko ita ko ke, bansan ya zanyi ba Suheeeerrrr ya fada idanunshi sun kada sunyi jajawur, wasu zafafan hawaye ne suke tsere a fuskarta “ya ilahi ka sasauta min wannan jarabawar ka bani ikon cinyewa, ” ta fada tana kallon habeeb da ya canza gaba daya ya fita a kamanninshi, tace “go habeebi go, kaje kayiwa mahaifiyarka biyayya insha Allahu bazaka tabe ba, akwai albarka mai tarin yawa cikin yiwa iyaye biyayya, bazaka taba ganin daidai ba matukar ka saba musu, musamman uwa, jeka habeebi jeka ta fashe da wani kuka mai cike da rauni ta juya a guje zuwa cikin gida.hannu yasa da niyyan kamota tsabar yadda yakejin zafin zubar hawayenta kuma wai shine sila, saidai tuni ta shige gida.

Durkushewa habeeb yayi a wurin domin ji yayi kafafunshi sun kasa daukarshi…

Ina kaunarku irin sosai dinnan my fansss…
????????????AUREN~FANSA????????????

BY.

Asma’u Mai Anguwa

Ummu Fadeela.

Typing????

Book Two

Page 53 / 54.

Da gudu ta shige gida…Gidan tsiit yake ba alamun motsin mutane, kan doguwar kujera ta fada ta fara rera kuka maiban tausayi, ganin habeebi ya dawor mata da komai sabo, ya fama mata ciwon dake cikin zuciyar ta wanda rashin lafiyar kawu lamido shine ya danne wannan ciwon, dama tana kokarin dannewa ne ganin halin da family dinta ke ciki, amma yanzu ganin da ta masa, da kuma halin da ta ganshi komai ya dawo mata sabo filll, ga kuma sabon al’amarin da Rasheed ya shigo mata dashi, wanda wnn zabin daidai yake da zabar rayuwar kawu lamido ko kuma mutuwar sa, ji tayi kanta na juyawa, kamar ana dagula kwakwalwarta, ga wani kara da take ji a kunnuwanta kamar an kunna injin markade.

Habeeb ya dade durkushe wajen tun bayan wucewar Suheer, kuka yakeson yi kamar yadda yaga tanayi ko zai samu saukin radadin da yake ji a zuciyar shi amma yakasa, sai wani irin harbawa da kirjinshi keyi idanunshi har wani rufewa sukeyi, a hankali ya fara karanta,”la haula wala kuwwata illah billah, Allahumma lah sahla illah ma ja’altuhu sahla, wa’anta taj’alul hazna iza shi’ita sahlan,….. la’ila ha illallahu wallahu akbar……Astagfirullah…..Ya hayyu ya qayyum birahmatika astaqisu…”

Sannu a hankali ya fara jin nutsuwa tana saukar masa, gathering courage yayi ya mike yana jin kamar an zare masa lakar jikinsa ya juya ya nufi gida.

Kuka sosai mai sauti suheer keyi ba tare da tasan ma tanayi ba, duk ta jigata har farar fuskarta ta koma jawur ta fara kumbura.fareeda dake kwance tana fama da ciwon mara mai tsanani don duk wata saita fama da wnn matsalar , mikewa tayi a cikin nutsuwa tana dafa bango domin kafarta ta rike gam haka yake mata kafarta ta zama kamar wadda aka sa a firiza tsabar sanyin da yake mata, wani lokacin har bata iya tafiya, cikin kulawa take tafiya tana rumtse ido, da haka ta iso palon , hango suheer tayi kwance cikin doguwar kujera tana ta rera kuka abunta, dan matsar da kafafunta tayi ta zauna a wajen , suheer da bataji fitowar ta ba sai zamanta, ta tashi da sauri ta rungume fareeda cikin disashiyar muryarta na wadda tasha kuka ta gode Allah tace “sweetheart ya zanyi, ya zanyi dan Allah komai ya tsaya min kawu a asibiti ammi da anty suna cikin tashin hankali, mamar habeebi tasa ya gujeni, ga kuma wnn…….Sai kuma tayi shiru tana cigaba da sheshshekar kuka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button