AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ammi ne ta fara hango shi yana saukowa ya kara kyau fiye da tunanin mai tunani, yayi wani haske ga wani jiki da yayi kamar ba jinya yaje ba, yana gama saukowa suka hada ido,kasancewar wurin kwanyar yake da haske kai kace rana ce, ai ammi bata yi wata wata ba ta kwasa a guje kamar wata yarinya taje ta rungume lamido shima baida wani zabi da ya wuce na karbar ta (Su ammi yau an manta da karatun islamiyya????),

Suheer da fareeda dake tsaye suma suna hira kasa kasa sai a lokacin suka ankara dasu a guje suka je suka hada ammi da lamido suka rungume gaba daya, hafsa ta koma gefe ta rike kugu tace “tunda ni ba’a farin cikin dawowata bari in koma kawai”. Sake lamido sukayi dukkansu suka koma suka rungume hafsa suna dariya mai hade da kuka…Nan suka rankaya gida suna masu farin ciki, gaba daya abunda suka dafa da soye soyen da suka yi ammi da yaranta suka ringa jidowa suna dire musu a gabansu, hafa ta rike baki tace “wai adama duk wannan namu ne,?”

Ammi ta gyada kai tana jin hawaye yana taruwa a idonta tace “duk naku ne hafsa, nida yara muna farin cikin dawowar ku,” daga kai lamido yayi jin yadda muryarta ke cracking, daga yanayin fuskar ta yasan akwai abubuwa da dama da suka faru,…Bayan kwana biyu da dawowar su anty hafsa suna zaune palo, suna hira,ammi tana ba lamido labarin abubuwan da suka faru bayan accident dinshi, ajiyar zuciya ya sauke yace “Duk hafsa ta fada min adama, nayi matukar murna da abunda kuka min, ina alfahari da irin sadaukarwar da yaran nan da ma ke kanki kukayi a kaina,”. amma meyasa take gida? kadai dan dawowa ta tazo?, dan jimm ammi tayi kafun tace,”zamuyi maganar anjima, nan ta daura musu da labarin ashe maman rasheed itace kanwar babanta da suka fito nema, yace ikon Allah yanzu suheer da rasheed yan uwane ashe basu sani ba duk irin takun sakan da suka ringa yi.”

Suheer ko na rike da plate mai dauke da biredi yanka biyar a kai sai kwalban jam mai strawberry flavour, sai dandana take tana ci, fareeda na gefe tana dan tayata lasa wani lokacin, hafsa dai kure suheer tayi da ido tana mamakin yadda ta sauya da alama ba wadda ya fahimci hakan, duk hiran da ammi ke masu na abunda ya faru bata fahimta.

Ammi ne tace “hafsa bakice komai ba”, dan juyowa tayi tace “akan me fa”?.

Cike da mamaki tace “duk surutun da muke bakya jinmu kenan, akan wanda nace miki yana neman auren fareeda, “mikewa hafsa tayi ta fara tafiya tana fadin na shiga uku ni hafsatu, yanzu Adama ni me nawa a nan da zaki sako ni a ciki, a’a gaskiya ki dena haka babu kyau abunda kike yi, ni me nawa da fareeda da zaki ringa hada ni da ita bayan kina raye ga kuma yayaa a hannun damanki,” gaskiya ki gyara halinki” ta shige daki ta barsu a wurin, dariya lamido yayi ammi tana tayashi, ammi tace “wai ita nan kunyar yar fari take, lamido yace “a’a gaskiyanta ne ai ke kika cancanci komai na rayuwar fareeda, zahiri da badini kece uwarta, kuma itama nasan tana alfahari dake a matsayin uwa, don ke din uwace ta gari abun koyi, irin wacce tayi karanci a wannan zamani da muke ciki”.

Sunkuyar da kai ammi tayi kasa tana murmushi, sannan tace “plus uba na gari, da taimakon ka ne na zama haka da ace za’a ringa samun mutane masu taimako a duniyar nan kamar kai da hafsa da tabbas an rage mutane masu fadawa gararin rayuwa da dama,.Kallonta kawai lamido yake yi, yayinda suheer da fareeda kuma ke kallon su kamar sun samu talabijin.

A hankali fareeda tace “rabin jiki muje daki”…Fareeda na kallon suheer tace rabin jiki mai zai hana……Ta matso ta rada mata magana a kunne,. Da sauri suheer ta dago ta kalleta tace “kinsan Allah sweetheart na dade da tunanin nan a raina kawai dai bansan yadda zasu dau maganar bane,” fareeda tace “to ai ba a bori da sanyin jiki yanzu muje mu samu anty hafsa”….Shiru anty hafsa tayi tana saurarensu har suka kai aya, tace “amma ya akayi yaran nan kuka fini hangen nesa haka, wannan shawara yayi daidai gaskiya….Bayan kwana biyu fareeda da suherr suna ta neman yadda zasu tunkari ammi da kawu lamido da maganar amma sun rasa, yau dai suna zaune suna cin abinci fareeda tayi karfin halin cewa,ammi kawu ina da magana,” duk juyowa suka yi suna kallonta, hakan yasa ta fara inda inda, suheer ta karbi maganan tace “ni da sweetheart da kuma anty hafsa mun yanke shawaran muna son kuyi aure, lamido yayi murmushi yace “inbanda abunki mamana wa zai aureni at this age, ni kam ku kadai kun isheni rayuwar duniya, caraf ammi tayi tace “balle kuma ni mai zankada zankadan y’ay’a kamar ku.hafsa tace “duk mun san da wannan shiya sa muka yanke shawaran muna son ku auri junanku dan mun hango dacewar hakan” ko dar lamido bai yi ba, inda hakan zai kasance sai yafi kowa farin ciki, ammi kuwa ji tayi lomar shinkafar da ta kai baki ya kauce hanya yabi ta hancinta, nan ta fara atishawa kamar kanta zai fado kasa,tun bai lafa ba ta fara masifa kamar zata ari baki har juyawa idanunta keyi, daga karshe ta shige dakinta ta rufo kofa. Galala suka bita da ido, lamido ma ya mike jiki a sanyaye ya nufi hanyar fita….

NOT EDITED..
????????AUREN~FANSA????????

PAGE 79 / 80.

    By 

Ummu Fadeela.

Kallon juna suka yi gaba dayansu, hafsa tace “karku kulasu da kansu zasu sauko musamman adama, nasan me ta ke ji a ranta, just mu basu space. Haka kuwa akayi bayan kwana biyu ammi tazo ta sami hafsa har dakinta tace mata zasu yi magana, gyara zama hafsa tayi tace “I am all ears”. Ammi tace “hafsa a ganina aure yayi kadan ya saka muku abun alkhairin da kuka min a rayuwata ke da yayaa,bansan me zance ba plsss ki bani shawara as your sister.”

Nan hafsa ta ringa bawa ammi shawara da kuma concrate dalilai daya sa suke bukatan wannan hadin da ita da yaran duka,sosai hankalin ammi ya dau zancenta sai kuma tace “amma fa ke zaki fada masa dan naga kamar ma fushi yake yi,…Duk halin da ake ciki saida ammi ta sanar da ummie wacce ta ke gani a matsayin kwafin babanta da kuma mamarta,ummie ma ta karfafa mata guiwa hadi da bata shawarwari masu amfani,…Da shike abune ba na yara ba,cikin kwana uku ammi ta amarce da kawu lamido wannan iyalai ba karamin farin ciki suka shiga ba a wannan rana.Koda dare yayi ammi sai nonnokewa take ganin idon yara ga kuma kunyarta na gado,basarwa su fareeda suka yi suka ma shige daki da wuri hakama hafsa da farin cikinta ya gaza boyuwa,…A oda room ma kawu lamido bai cuci kanshi ba kasancewar sa sabon shiga bai boye maitar shi ba, the first round was woww duk yadda ya tsammaci abun ya wuce haka, bayan anje hutun half time kawu lamido ya kuma komawa second round sosai abun ya bada armashi, nidai jawo musu kofa nayi nace asuba ta gari adama lamido.

Suheer na kwance sai juyi take akan gado ta rasa me ke damunta gaba daya jikinta ciwo yake mata jin gadon take kamar akan k’aya take kwance, juyawa tayi taga fareeda tayi bacci bayan sun gama shan soyayyarsu da sugar daddynta, a hankali ta mike ta fita kitchen ta shiga ta dau biredin da ta ajiye dazu ta zauna dabas a tsakar kitchen din ta bude ta fara ci, gayan biredin haka take ci yau ko arzikin jam din bai samu ba, da alama kuma da farin ciki take cin abunta don har wani lumshe idanu take yi, taci kusan yanka bakwai kafun ta mike ta dau goran ruwa ta kwankwada ta koma daki nan da nan ko bacci ya kwasheta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button