AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Karfin halin matsowa kusa dashi suka yi, suka zube kan guiwowinsu, bala yabuɗe baki da niyyar yin magana kenan wannan boka ya ɗaga musu hannu, take suka yi tsit, tsawon mintuna biyu idanunshi a rufe,sannan ya buɗe suya dubi samaila wanda kallon idanun nashi kawai yasa jin gudawa na shirin barke masa.

Da wata murya mai ƙarfin amo yace” kana so a baka sarautar sarkin noma, kanaso duk wani manomi dake yankin ku ya zama a karkashin ikonka, kanaso dukiyar ka ya bunƙasa fiye da tunanin mai tunani, kana so kana so basuda iyaka, lallai zan baka kazo kankat zan biya maka duk wani buƙata taka. ( WA’IYAZU BILLAH) amma da sharaɗi ɗaya tal ….sharaɗin shine kada ka bari wata daga cikin matanka ta haifa maka ɗiya mace,

Idan kuma ka bari hakan ya faru, to wannan aiki zai lalace zaka talauce, zaka zamo abun kyama da gudu cikin al’umma samun mai baka sadaka ma zai gagareka. shin ka amince?.

Ba tare da dogon tunani da nazari ba samaila ya gyaɗa kai alamun ya amince,y yana ganin ai wannan abu ne mai sauƙi cikin wanda zai iya aikatawa matukar zai samu mulki da arziki, ( INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN). ya manta Allah shike bada mulki da arziki ga wanda yaso a kuma lokacin da yaso, ya manta Allah shine AR-RAZZAQU idan ka roƙeshi da imani, taqawa, da kuma ikhlasi zai baka, Allah shine wanda yaba Annabi Sulaiman (AS) mulki irin wanda ba’a taɓa yiba a wannan duniya( ALLAHU AKBAR.)

Take wani ƙullin magani ya faɗo a gabansu, yaci gaba da magana cikin sautin shi marar daɗin sauraro. “ka ɗauki wannan idan dare ya raba ka je ka barbaɗa a duk wata mahaɗa ta jama’a ,sauran aiki kuma sai wannan ya ƙare,.

Haka kuwa a kayi cikin dare sama’ila yabi duk wata matattarar jama’a ya barbaɗe wannan magani. dama ance tsafi gaskiyan mai shi.

Cikin kwana uku a ka tabbatar da sama’ila a matsayin sarkin noman goruba likkafa taci gaba arziki yana ta bunkasa, shi kanshi baisan daga ina suke ɗiɗɗikowa ba, ga jama’a kowa sarkin noma, cikin lokaci kaɗan ya tashi daga sama’ila yakoma Alhaji sama’ila duk kuwa da cewa baije makka ba, Nera kenan Allah ka ba kowa rabinshi ta hanyar halal.

Kwatsam bayan wasu wattani sai ga ciki babba ya bayyana a jikin amaryar Alaji sama’ila balki, nanfa ake yinta domin kuwa baisan yadda zai gane mace ce a cikinta ba ko namiji ba, don haka ya tsare balki a ɗaki da tambayar ta menene a cikinta yacigaba da cewa “dole kin sani tunda ai a jikinki yake” balki tace ” ikon Allah, alaji ta ya zan sani? niba masaniyar gaibu ba wannan ai Allah kadai ya barwa kansa sanin me zan haifa kuma ni koma wanne iri ne ina farin ciki fatana Allah yabamu mai albarka kuma ya sauƙeni lafiya”. ta karisa da murmushi saman fuskar ta. da sauri alaji yace “a’a balki badai ko wanne ba ni ɗa namiji na keso ki haifar min kinji ko? namiji nakeso, duk ya rikice lokaci ɗaya har fuskar shi ya fara sauya kamanni.

Da sauri balki tace” haba alaji, kayi hakuri da abunda zan faɗa amma sam wannan kalma bata dace da musulmin kwarai ba, wanda ya yadda cewa Allah ne mai bayarwa ba wayo ko dabarar mu ba, ko ka manta faɗin Allah S W T cikin suratul ASH-SHURA aya na 49 zuwa aya na 50?

LILLAHI MULKUS SAMAWAATI WAL ARD’, YAKHLUQU MAA YASHAAA’, YAHABU LIMAN YASHAAA’U INAASANW WA YAHABU LIMAN YASHAAA’U ZUKOOR .
ga Allah mulkin sammai da ƙassai suke’, yana halittan abunda yaso. ya na bawa wanda yaso ƴaƴa mata. kuma yana bawa wanda yaso ƴaƴa maza.

AU YUZAWWIJUHUM ZUKRAANANW WA INAASANW WA YAJ’ALU MAN YASHAAA’U AQEEMAA’. INNAHOO ‘ALEEMUN QADEER.
Ko ya haɗa musu duka wato ƴaƴa maza da mata , kuma yabar wanda yaso a mara haihuwa kwata-kwata Allah shine Aleemun Qadeer.

Kuma……..fuuu ya fice daga ɗakin ba tare da ya jira jin me zata kuma faɗa ba, ya nufi fadar sa inda jama’a ke tare ana ta fadanci irin na ƙauye, ya hakimce akan kujerar sa , bala ne ya matso kusa dashi yace ” akwai matsala ne sama’ila”?

Ya juyo ya dube shi yace “kwarai kuwa bala akwai matsala sai yanzu nake nadamar ban tambayi mutuminnan yanda zan gane me matata ke ɗauke dashi ba inta na da ciki, yanzu dai ga can balki da juna kuma bansan yanda zanyi ba, nafara tambayar ta ta kama min wa’azi haɗi da jawo min ayoyi,”

Dariya bala yayi sannan yace a hankali “wannan ba matsala bane ae kawai ɗaukarta zakayi ka kaita babban asibitin kuɗi a birni kawai hoto zasu mata take zasu gano abunda ke cikinta, gaɗai zamani Allah ya kawo mu komai yayi sauƙi ai kawai cema ta zaka yi ta shirya kuje a duba lafiyar ta da na abunda ke cikinta.

Wani wawan ajiyar zuciya alaji sama’ila ya sauƙe yace” shiyasa nake son shawara da kai bala ” bala ya washe hakora jin an yabe shi. (Allah ka haɗa mu da abokai na gari ameen).

Koda alaji yasa mu balki da batun ta shirya suje asibiti, firr taƙi a cewarta lafiyar ta ƙalau to me kuma zai kaita asibiti. sanda ya nuna mata jan ido kafun ta yarda ta bishi, wani haɗaɗɗen asibitin kuɗi ya kaita, scanning na farko likita ya gano ya macece kwance mahaifar balƙi. alaji yace da balki ta fita ta jirashi a waje yana zuwa.

Alaji yana goge zufar dake tsatsafo mishi a goshinsa yace” likita kataimake ni ka cire cikinnan ko nawa ne zan biyaka” kallon baka da hankali likitan ya masa, sannan yace ” kayi hakuri bama cire ciki a nan saidai kaje gaba.” likita kad……… get out of my office my friend, fita kafun insa security su fitar mun kai akwai wasu patients dake kan layi” ya katse shi yana nuna masa kofar fita da yatsarshi. simi simi ya fita ya samu balki zaune a reception tana jiranshi,

Haka suka koma gida ba wani walwala.

Wannan karon ma bala ya kuma samu da batun. cikin murya kasa kasa yace” bala cikin mace balki ke ɗauke da, kuma nayi ƙoƙarin ganin likitan ya cire cikinnan amma mutumin yaƙi, karshe ma hukuma yayi barazanar kira min.” dan matsowa bala yayi kana yace ” wannan ba abun damuwa bane kabani yini ɗaya zan samo maka mafita” ajiyar zuciyan samun mafita alaji yayi a ranshi yana mai godiya wa Allaj daya bashi aboki mai ƙaunarshi. hmmm.
a zahiri kuma cewa yayi” bala badon kaiba da bansan yadda zanyiba ” ” karka damu ” cewar bala wnn shine zaman taren ai kuma ma ai nida kai duk mun zama abu ɗaya.

Washe gari sai ga bala da sanyin safiya, yazo da wani kullin magani daure a leda, miƙawa alaji yayi sannan yace” wannan a zuba mata a kunu tasha an tabbatar min matuƙar tasha shi to tabbas cikin zai fita a yau ɗinnan.”

Cikin farin ciki ya amshi ledan ya jefa a babbar rigar shi, kana ya juya cikin gidan .

Tabawa ya ƙira koda tazo cikin sakin fuska yace mata ” muna da kunu a gidan ” da hanzari tace a’a amma muna da kamu, in gaggawa kake sai in dama maka kunun” da sauri yace ” yauwa tabawa ta uwar gidan alaji sama’ila a duniya da aljanna, maza damo min.

Da fara’a ta wuce madafa cikin minti sha biyar sai gata da kofin kunu yana ta tururi, ta miƙa masa yayi godiya haɗi da cewa “Allah ya miki albarka” . da sassarfa yayi hanyar ɗakin balki, balki na kwance haka kawai yau take jinta very restless, tama rasa tunanin me zata yi ga wani zazzaɓin da yake taso mata sama sama, kawai taji an faɗo mata ɗaki ba tare da sallama ba, a firgice ta tashi wanda hakan yayi sanadiyar motsawar abunda ke cikinta da masifar karfi ba shiri ta koma ta kwanta, gami da faɗin washhh alaji ka tsoratamu wallahi, dubi fa har ɗanmu saida ya tsorata”, matsowa yayi kusa da ita ya zuba mata ido without blinking, tayi fiyau da ita ga cikin yayi ɗas a jikinta gwanin sha’awa badon wannan sharaɗi da boka ya basu ba da yafi kowa farin cikin wannan abu, da a yanxu rungumar ta zai yi ya shafa cikin yace “( sannu yata baba ya tsorata ki ko ? lallai zamu hukunta baba.”)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button