AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kuka suheer ta fashe da, tana cewa “wllh ammi da gaske ne, zo ki ganshi, dazu fa mun rabu dashi jikin da sauki, kuka take yi sosai, sai kuma ta fara bubbuga filon da yake kai tana kiran sunanshi, habeebi!habeebi, bude idonka kaganni.”

Zuwa lokacin zuciyar shi ta fara kasa jurewa kukan masoyiyar tashi, a hankali ya bude idanunshi ya sauke su akanta, tsaida kukan tayi tace cikin shagwaba ” habeebi me ya sa me ka bayan tafiya ta? duk ka daga min hankali, murya kasa kasa yace ” nima fa bansan komai ba, kawai wannan shirin mama ne, kuma har yanzu bata ce min komai ba akai.

Numfashi suheer ta sauke cikin nutsuwa tace ” ga ammina tazo duba ka.

Cikin jin kunya ya sunkuyar da kai dan shi baiyi noticing ammi a wurin ba, kana ya gaisheta cikin ladabi, amsa wa tayi, sannan ta mishi sannu da jiki, bayan kamar minti biyu, tace da suheer zata je gidan hajiya saratu dan haka ita ta wuce gida kawai.

Bayan fitar ammi da kamar minti biyar, saiga mama asabe ta shigo tana ta washe hakora kamar gonar auduga, hannunta rike da wani dogon file, still tayi a wurin ganin suheer zaune, a ranta tace ” kai wannan ya akwai jarabar tsiya,” amma a zahiri murmushi ta kirkiro tace ” a’a kedai bakya gajiya da hanyannan, inba haka ba, ba dazu kika fita ba amma harkin kuma dawowa, to angode da ziyara, yi maza ki koma gida kar iyayenki su ne me ki, Allah ya muku albarka.

“Ameen” Suheer ta amsa kana ta mike tana gyara zaman mayafinta, hada ido sukayi da habeeb wanda sam baiji dadin abunda maman shi tayi ba, tace cikin sanyin murya “Allah ya kara sauki” bai iya ya amsa mata ba, ta nufi hanyar fita, taku daya biyu tayi kafun ta iso kofar aka bude kofa a kashigo, buba ne da lauyan rasheed suka shigo, chak taja tunga ta tsaya, buba da bai kula da ita ba yace yana kallon asabe, “hajiya kin shanya mu a waje baki mana iso ba shiyasa muka shigo domin sauri muke matukar bamu koma da wuri ba komai na iya faruwa da oga na.

Mama asabe tana murmushin karfin hali tace ku karaso mana, ta nufi habeeb tana mika mishi dogon file dake hannunta tace mishi “kasa hannu akan wannan yanzunnan.”

Karba yayi yana kallonta yace “na me ye wannan din,? tace kaidai kayi abunda aka saka, bude cikin file din yayi yana karanta abunda ke ciki, da sauri ya dago yace mama wannan fa yarjejeniya ne akan cewa Rasheed baisan komai akan buge ni da yayi ba, idan nasa ka hannu hakan na nufin na yarda Rasheed baisan da maganar buge ni da ya yi ba, jiki na rawa asabe ta fitar da wani signed cheque daga cikin rigar mamanta tace “ba wancan rubutun zaka kalla ba, wannan zaka kalla, ta fada tana nuna mishi tace ” kalla da kyau habeeb mamman, naira miliyan 20 ONLY.

Kallonta kawai yake without blinking, yayinda zuciyar suheer dake tsaye har lokacin kamar statue ya tsananta bugu.

Buba ne ya kariso bakin gadon da sassarfa yana kallon habeeb, yace “wannan kudin duka naka ne, abun bukata kawai sa hannunka akan wadanan papers din, habeeb yace ” amma cewa akayi rasheed baisan komai ba akai, murmushin lauyan yayi yace ” young man, wannan shi ake kira da out-of-court settlement. Kana sa hannu za’asaki rasheed kai kuma makudan kudin su zama naka, ya kare yana dariya.

Murmushi habeeb yayi sannan yace “kozan samu biro? da sauri buba da farin cikin shi ya kasa boyuwa, ya zaro biro daga gaban rigar shi ya mika mashi.

Wani irin shock ne ya kama suheer a take bakin ta yana rawa tace ” habeebi are you going to sign those papers?, yana murmushi yace ” come here plsss” Matsowa tayi cikin sanyin jiki, cheque din ya nuna mata yace ” duba kiga? dubi yawan kudin da suke rubuce a kai duk tsawon rayuwa ta ban taba ganin makamancin wannan kudi ba koda a rubuce ne kuwa, yana murmushi yake magana yayinda zuciyar suheer ke ta bugawa.

Miko mata takardar ya kuma yi yace dan rike min gefe daya kinsan hannu na daya baya aiki, rikewa tayi har hawaye ya kawo idonta. Daga biron yayi yace, dama million yana da ziro da yawa haka ya fara irgawa daya yasa biron a ciki saida ya bule, yakuma sawa a na gaba shima ya bule haka ya dinga bin rubutun yana bulawa saida suka kare, na karshen da ya bula saida biron ya fito har karshe kana ya tsatsaga sauran ya watsawa buba a fuska ya koma ya kwanta, wani irin dariyar farin ciki suheer tayi. Mikewa buba yayi suka fice daga dakin shida lauyansu ranshi yana kuna, yazaiyi ya fitar da rasheed kafun ya kwana a cell.

Kallon suheer asabe tayi ranta yana kuna, (jitake da akwai bindiga a hannunta ba abunda zai hanata harbe wannan yarinya mai dan banzan naci haka, tun yanzu ma ta mallake mata da, inaga in anyi auren kuma,). Tace waye ubanki, me sunanshi,?a take dariyar fuskar suheer ta dauke cak juyowa tayi tace “me ya faru mama”.

Asabe tace cikin daga murya “nasan mamanki, nasan wannan birkitacciyar yayar mamanki da kuma addanki, ubanki ne kawai bansani ba, inda zan ganshi zan tambaye shine, shin wannan shine irin tarbiyar da ya miki? ke wacce irin yarinya ce hakane eyye, kin taba ganin ya mace da taurin kai? to wannan ba halin matan kwarai bane? sannan wannan ba halin zaman gidan miji bane, tun yanzu kin mallake min da sai abunda kika ce zaiyi, inaga nan gaba kuma in yasan dadin mace, me zai faru,? tukunna ma ina kika sanshi? ta ina kuka hada dangi dashi da zaki ke yanke masa bukuncin da ni uwarshi banba? kanin baabarkine shi? zuwa lokacin kukan suheer ya tsananta ,ji take duniyar yana juya mata,.

Asabe taci gaba da magana “tambayarki nake, ta ina kuka hada dangi dashi,? inace accident kawai ya samu kika taimaka kika kawoshi asibiti,? to daga rana irinta yau na datse alakar dake tsakaninku, kar inkuma ganin kafarki anan, habeeb da ya tashi zaune yana kallon mamanshi da mugun mamaki, yace “mama mekā€¦.. Dakatar dashi tayi ta hanyar daga masa hannu tace “rufe min baki shanyayye kawai”,.

Rufe baki suheer tayi da hannu hawaye na tseren gudu akan fuskarta, da baya baya take fita har ta iso kofa da gudu ta fice daga dakin tana kuka mai matsanancin ciwo, tunda take ba’a taba cimata zarafi irin na yau ba. Kuma cin zarafinma daga wanda take mutuntawa, kuma take tsammanin mutuntawa daga garesu.

A haka tazo gida, mai taxi dinma bai karbi kudi daga wurinta ba ganin halin da take ciki, tsayawa tayi ta goge hawaye da suka ki tsayamata, cikin jan kafafu ta iso kofar palonnasu ta bude, shiru taji gidan kamar ba kowa, a hankali ta taka ta shiga tana kiran ammi, ammi , a ranta tace kodai ammai bata dawo ba, ta kuma fadin sweetheart, anty hafsa, nanma shiru, murya taji daga bayanta ance “nikam tunda ba’a damu dani ba ko sunana ba’akiraba,.

Da gudu ta juya inda taji muryarshi taje ta rungume shi, wani sabon kuka ne ya kubce mata, kukan ta dinga gi tamkar ranta zai fita, yayinda lamido yake ta rarrashinta, da kyar ta iya dagowa tace ” kawu me ya sa sai yanzu ka dawo? nayi kewarka, da kananan da duk hakan bai faru ba, don Allah nayi laifi akan abunda na aikata?.

Dago kanta yayi yace “no wonder nidai nasan ba haka na bar gida na ba, it seems like bango hudu da suka hadu suka rike ginin gidannan they’re separate each other. Me ya faru? fada min yata daina kuka kinji.

Kafun suheer tayi magana suka ji muryar fareeda daga bakin kofa tana cewa “duk hakan ya fadu ne saboda mugun halinta, ita tajamana duk abunda yake faruwa a gidannan, da gudu kuma ta kariso itama ta rungumeshi tana kuka, lamido yace ” me kike fada haka ne fareeda dagowa tayi tace duk abunda yake faruwa ita ta jawo, hafsa ma ta karisa shigowa, (dama tun bayan fitar ammi da suheer tace da fareeda ta tashi suje su sha iska watakil zata warware,.)tace, yayaaa duk wannan ce ta jaxa mana bakin ciki a gidannan, ta nuna mana bare na waje ya fimu muhimmanci a rayuwar ta,yafi iyalenta daraja a idanunta, duk ya rude yace me kuke fada haka ne wai me ya faru ne da kuka kasa kirana a waya ku sanar min?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button