AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani wawan ajiyar zuciya habeeb ya sauke, dan daga tsakiyar kansa har kan babban yatsar kafarsa yaji saukar muryarta, hakan yasa gaba daya jikinsa ya amsa, lokaci daya kasala ya saukar masa, “are you there habeebi?” cewar suheer jin yayi shiru, da sauri fareeda ta dago kanta tana kallon yar uwar tata jin sunan da ta ambata, habeebi, tamkar yau ta fara jin ta kira sunan.

Karfin halin saisaita nutsuwarsa habeeb yayi murya can kasa yace ” you want to take me to the early grave suheer,” cikin zaro ido tace me?” sai kuma ta shagwabe murya tace “habeebi nidin kuma, to lallai da tare zamu shiga kabarin kenan, dan idan ba kai tabbas babu ni, ka zamo wani bangare na rayuwata habeeb, ka shiga cikin jerin mutane hudun dake da muhimmanci a rayuwa ta.

Zuwa lokacin jikin habeeb ya gama muguwa gaba daya dan har wani yarrr gashin jikinshi keyi, cikin kasalalliyar murya yace then me zai hana ki barni in zamo babban jigon rayuwarki suheer, kalmomi sunyi kadan in nuna maki irin yadda nake kaunar ki, kibani dama in nuna miki a aikace suheer plssss. Bazaki taba nadamar kasancewa dani ba, bazaki taba nadamar bani ragamar rayuwarki dazakiyi ba.”

“Taya kenan”, cewar suheer murya kasa kasa yace ” ki ba ni dama in turo magabata na ayi maganar manya”.

Da sauri ta rufe ido tace ” kai habeebi da wuri haka” mimicking muryar ta yayi shima yace ” kai habeebiya na girma fa, gashi yanzu ma muryarki yasa ni dole sainayi wanka ina zaman zamana”, kiit ta kashe wayar tana kokarin cusa kanta tsakanin cinyoyinta kamar yana wurin. murmushi habeeb yayi daga bangarensa, dama yakira ta ne yabata hakuri akan abunda mama asabe ta mata saigashi yaji kamar tama manta, but muryar ta akwai damuwa aciki kamar kuma marar lafiya, zaidai finding out zuwa anjuma, dan yasan yanzu kam ya tayar mata da kunyar ta na fulani, murmushi ya kuma yi yana shafa beard nashi.

Rap rap rap,. Suheer taji tapi akanta hakan yasa ta dago da hanzari, fareeda ne tsaye akanta tana tafa mata, kana tace Woww Rabin jiki, wonderfull, that’s really amazing, wato bayan duk abunda kika min har kina da gut na zama a gabana ki kama soyayya? kallonta kawai suheer keyi da mamakin anya lafiyar sweetheart kalau kuwa? da ace lokacin baya ne tana gama wayar nan rungume juna zasuyi su kama dariya, fareeda ta ringa tsokanarta, ita kuma tana jifanta da filon kujera amma dubi yanzu, sanin da tayi cewa su biyune a palon yasa ta amsa wayar a gabanta bata tsammaci abun zai bata mata rai haka ba.

Tace ” sweetheart me kike fada haka ne?” dariyar takaici fareeda tayi tace “ba dole ki kasa gane abunda nake fada ba tunda giyar soyayya tana kwasarki, bayan kin raba ni da komai nawa har kina da damar yin farin ciki ashe,?” tambayar ki nake” ta fada da tsawa wanda ya janyo hankalin ammi kansu, ta fito da sauri, fareeda tana nuna suheer da hannu yayinda abokinnata wato hawaye tuni ya fara ambaliya a akan fuskar ta, tace “KE BAKAR KADDARA CE A CIKIN RAYUWA TA,.

Fareeda!ammi ta fada da tsawan gaske tana karisowa wajensu, wani irin magana kike yi haka kina da hankali kuwa? fareeda tana kuka tace” ammi banyi laifi ba dan nace ita bakar kaddara ce a rayuwata, idan itace a matsayina nasan da burinta tun tana yarinya bazan taba mata abunda tayi mani ba, nikam banyi sa’ar yar uwa ba ta fada kana ta juya da gudu ta shige daki, ba abunda suheer take yi sai aikin juya kalmar bakar kaddara da yar uwarta mafi soyuwa a wurinta ta kirata dashi, tuni itama hawayen ya fara saukar mata, ammi kam tsayuwa kawai tayi a wurin kamar gunki, kafun tayi yunkurin cewa wani abu aka kwankwasa kofar palon, juya wa tayi taga suheer durkushe tana hawaye, fareeda kuwa tuni ta shige daki, hakan yasa ammi jan kafa ta nufi kofar don ganin waye,.

Handle din ta kama, kana ta bude kofar, ido hudu sukayi da Rasheed dake tsaye kikam a bakin kofar kamar wani soja, tsawan minti daya tana kallonshi, kafun tayi karfin halin matsawa da cewa “shigo ciki”.

Shigowa yayi yana karewa palon kallo kamar mai neman ajiyan da yayi, ido suka hada da suheer wacce tun shigowar shi ta tsaida kukan da take ta goge idonta, maido da dubanshi yayi kan ammi da ta hade rai tana ta cika, tace “waye kai me kazo yi anan?” .

Rasheed da yayi fuskar tausayi yace “Are you suheer mother?”

Suheer tayi caraf tace ina ruwanka mai ya kawo ka nan bayan duk abunda ya faru….?

Dakatar da ita ammi tayi tace “barni inyi magana dashi” tana kallon rasheed tace “ehhhhh…. nice mahaifiyar Aisha Suheeer da kuma fareeda, mai ya faru,”?

Rasheed a ranshi yace ” Aysha suheer”!
Da sauri ya dawo nutsuwar shi jin ammi ta sake magana, cikin sanyin murya yace “ta ina zan iya fadan abunda yake tafe dani alhalin kina cikin fushi,” ammi ta kuma cewa maike tafe da kai, Rasheed yace “neman TUBA” kafun ammi tayi wani yunkuri rasheed ya tsugunna bisa guiwowinsa ya cire hular kansa yace ” kisa min albarka UMMIE, sai kuma ya mike yace “irin tarbiyar da kika bawa yarki bawai ita kadai ya amfana ba, tabbas nima ya amfane ni.” ammi dai sai kallonshi take yi baki a bude.

Yaci gaba da magana cikin raunin murya, “tun ina yaro, ba wanda ya taba ce min yi kaza, ko bar kaza, haka na taso ba sawa ba hanawa,. Lokacin da na girma kuma na girma da nasara, ga tarin dukiya ga daukaka, don haka duk mutanen dake zagaye dani ba mai nuna min mistake nawa duk abunda nayi mai kyau ko akasin haka yabawa suke yi, saigashi rana daya yarki tazo gaban dubban mutane ta kalubalanceni, ta nuna min madubin gaskiya, tundaga lokacin nake yawan kallon kaina a cikin wannan madubin amma ba abunda nake gani sai Rasheed, I was wrong judging this rasheed, domin wanda nake kallo shine real rasheed, spoilt, brat, proud, and self-centered.

Ya juya yana kallon Suheer yace “Suheeer yadda kika tsani wannan Rasheed din, nima haka na tsaneshi daidai da tsanar da kika mishi”, hada hannu yayi wuri daya yace “na gode da kika nuna min madubin gaskiya har na gane waye rasheed na gode, ya fada murya kasa kasa,.

Dube dube ya kuma yi a palon bakin kofa ya hango fareeda tana makale don tun fara maganar shi ta leko amma ta kasa fitowa, hada ido sukayi ta juya da sauri zata koma yace “fareeda karki koma kema ina bukatan neman afuwarki, a hankali ta tako cikin palon ta tsaya a gefe, yace ” kiyi hakuri da duk abunda ya faru yar uwarki gaskiya ta nuna, bayan ta aikata abunda ya dace a kaina, naga ya kamata inzo in nemi yafiyar gaba daya ahalin wannan gida, wani dogon file da ya shigo dashi ya mika mata yace “wannan shine contract din film namu, gashinan nayi signing ki shirya nan da kwanaki kadan zamu fara daukan fim din hannu na rawa fareeda ta karba bakinta a sake, yayinda ammi da suheer ke tsaye cikin matukar mamaki.

Rasheed yakuma cewa ” fitowa a cikin film nawa da fareeda zatayi ne kawai zai bani tabbacin cewa kun yafe min duk abunda ya faru, yana kallon suheer har cikin ido yace” nagodeeee” kana ya kalli ammi yace “na barku lafiya ummie”.

Har rasheed ya juya ya fita gaba dayansu uku sun kasa motsi a wurin, tamkar dai wanda ya musu allurar kashe baki. da kyar ammi tayi gathering courage tace “dama Rasheed ba mutumin banza bane kamar yadda mukayi tunani ashe?, da dan sassarfa fareeda tabi bayan rasheed saidai fitowarta ta tadda matasa maza da mata cike kofar gidannasu ana ta daukan selfie da rasheed, da kyar yayi excusing kanshi ya shige mota yabar anguwan cikin mugun speed.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button