AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lokacinda hafsa ta haife abunda ke cikinta bayan sun rabu da samaila aurensu da wata biyu, sai tace ita fa dole ta mayarda yar dan bazata shayar da ita ba, ba irin lallashinda innar su bata mata ba amma da shike tana da taurin kai haka taki ji ta dau danyar jaririyar randa akayi suna ta mayar da ita kauyen goruba, wannan abunda tayi shiya hasala mahaifinta har ya koreta daga gidanshi.

Kasancewar innarsu tasan halin mahaifinsu kaifi daya ne idan yace ehh, to ba wanda ya isa yasashi cewa a’a, hakan yasa tabi dare ta roki lamido danta na fari akan ya tafi da hafsa inda yake sana’a ya tabbatar ya bata kulawa yadda ya kamata kamar yadda ita zata kula da shi, wnn shine mafarin rayuwar hafsa a kano, bayan wani lokaci sun taba dawowa kauyen su dake makwabtaka da goruba, nan suka iske labarin rasuwar iyayensu da shike kuma fulani ne su irin masu kaurar nan basuda wasu dangi haka suka koma suka cigaba da rayuwa su biyu har kaddarar rayuwa ya jefo adama cikinsu, suka hadu suka zama yan uwan juna.

Daga fareeda ammi tayi ta kama hannunta suka nufi hanyar fita, yayinda hafsa ma tayi karfin halin motsawa tabisu a baya, muryar lamido ne ya dakatar dasu, tambayar alaji samaila yake ina batun aurenshi dake kan adama, duk da yasan ba aure a tsakaninsu amma tabbatarwa yana da amfani, da kyar alaji samaila yace ba aurena akanta domin tun lokacin da aka nemeta aka rasa na cireta daga cikin jerin matana, gyada kai lamido yayi a ranshi yana mai ajiyar zuciyar samun relieve, ammi kuma wasu hawayenne suka kara gangaro mata, da sauri ta karasa ficewa daga dakin…..Da daddare suna zaune dakin uwani duk su hudun, a bangaren lamido kuwa wani karamin guest inn dake garin yaje yayi lodging daki daya,…Tattaunawa suke na abunda ya faru a baya tsakanin ammi da uwani amma banda hafsa da ta zama wata kalan rashin lafiya, yayinda yan matan kuma zaune suke jugum jugum ba um ba uhm uhm…. Wani ihu alaji samaila yayi wanda yasa su zabura gaba dayansu suka mike,..

Ihu yake yana kiran sunan balki,,, hauwa,,, tabawa,,,zasu kasheni, zasu kasheni ku taimakeni zasu kashe ni wuta, wuta suke watsomin a taimakeni, wayyo jikina wuta, zafii, ire iren wannan sambatu yake yana ihun da har makwabta suka fara shigowa gidan, dakin suka pantsama gaba dayansu, suna kallon ikon Allah, banda ihu ba abunda samaila yake yana ambatan jikinshi zafi gasunan suna watsa mishi wuta, wani dattijon malami makwabcinsu mai suna malam iro mai almajirai shi ya fara tofe shi da addu’oi a zatonshi ko jinnu ne, fareeda da suheer kuwa suna dakin uwani sun makale juna sai kuka suke yi ba kakkautawa jin halin da mahaifinsu ke ciki.

Malam iro ne umurci wani makwabcinnasu da ya samo ruwa ganin kamar samaila fa yana kan gargara, fita yayi ya nufi randa ya debo ruwa da sauri ya kawo, kafa mishi yayi a baki saidai ruwan yaki wucewa makwogoranshi, sauke kofin yayi ya fara karanto kalmar shahada ko Allah zaisa samaila ya kama, jin haka gaba daya mutanen dake dakin suka fara karantowa suma a tare a tare, kamar daga sama sukaji samaila yace “ASHHADU ANLA’ILAHA ILLALLAH, WA ASHHADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH, kawai wuyanshi ya juya, ALLAHU AKBAR malam iro ya furta kana yaja wani mataccen zanin gado dake kusa dashi ya rufe shi.

Shikenan samaila sarkin noma kuma ya zama sai tarihi, duk abunda kake aikatawa mai kyau ko akasin haka, kasani akwai ranar mutuwa, saidai yaushe zan mutu? a ina zan mutu,? ina aikata me zan mutu? menene ajalina? duka wannan bamu sani ba, Ya Rabbi kabamu kyakyawar karshe alfarman sayyadi rasulullah S A W.

Washe gari akayi jana’izar samaila aka mika shi gidanshi na gaskiya, sosai abubuwa suka yiwa ahalin samaila yawa gaba daya sun fita a hayyacinsu, musamman fareeda da suheer dan abun yazo ya hadu masu ne lokaci daya, har zazzabi ya kamasu a take. a kofar gida wurin karbar gaisuwa kuma wani sabon rudani aka shiga domin ana tsaka da karbar gaisuwa saiga yan sanda mota uku sun tsaya a kofar gidan dirkowa suka fara yi da ga motar suna jan tunga su tsaya kamar suna fagen daga……

Kwana biyu kunji shiru, sharrin na’urar bature ne ya same ni, na muku typing dayawa irin kusha karatunnan nazo turawa ashe gogewa nayi????. Shiyasa na koma gefe na sha shayi mai zafi na kwanta abuna, kuyi manage da wnn zaku samu long chappy gobe Insha Allah. One luv masoya.

????????????Auren Fansa????????????

Book Two

By

Ummu Fadeela.

Typing????

Page 41 / 42.

… Babban cikin yan sandanne ya sauko daga karshe kana suka nufi inda mutane ke tare,sallama sukayi bayan angaisa, yace “sunana inspecta sani, ya fada yana ciro id card dinsa, yace munzo nanne muna neman alaji samaila,.

Da kallo jama’ar dake wurin suka bisu, zuwa can malam iro yayi karfin halin cewa ” nanda kuka ganmu zaman makokin samaila muke yi Allah ya karbi abunsa jiya cikin dare,. Mamaki ne karara kwance fuskar inspectan, bayan shiru na minti biyu, yace kozamu iya ganawa da iyalanshi, domin abu ne mai muhimmanci ya kawo mu nan, akan maganar danshi dan baba,…. jagora aka musu zuwa cikin gidan babban tabarma aka shimfidawa yan sanda ukun da suka shigo, uwani ta taso jikinta na rawa ko me dan baba ya aikata kuma oho, gashi mahaifinsa ya rasu amma ko kwana baiyi a gidan ba balle ya sani, da wannan tunani ta iso wajensu ta durkusa, adama da su fareeda ma suka fito suka samu zama.

Ta’aziyya inspecta ya musu kana ya daura da cewa “danku yakubu samaila dan baba,yana cikin yan fashin da sukayi artabun da jami’an mu, daren jiya,munsamu kiran gaggawa daga kauyen goji cewar yan fashi sun tare hanyar da ta tashi daga goruba zuwa garin na goji ba tare da bata lokaci ba jami’anmu dake bakin aiki suka fito, bayan artabun da sukayi dasu mun samu nasaran kashe biyar daga cikin yan fashin da kuma raunata biyu saura kuma sun tsere, cikin wadanda suka mutu harda dan baba”. mun sanshi ne saboda irin cases da muke dashi akansa mai yawa a hukumar mu.

Wani irin kara uwani tasa, ihu take yi tana fadin ” Allah na tuba, Allah na tuba, mutuwar miji da d’a a lokaci daya astagfirullah,”. rirriketa ammi take yi, amma sai kokarin fizgewa take tana so ta gudu kamar kwakwalwarta ya fara kwancewa. Abunne ya mata yawa goma da ishirin dama a zabure take tun fara rashin lafiyar alaji ga kuma jarabawar dan baba da Allah ya bata, ga abubuwan da suka dinga faruwa, ita kuma wannan ce kaddararta, Allah ka hadamu da kyawawan kaddarorinmu kai mana sassauci akan munanan.

Tabbas uwa uwace, ko wani irin d’a ta haifa tana kaunar abunta, Allah ka sakawa mahaifanmu da aljannah madaukakiya……..Bayan sati daya abubuwa sundan fara lafawa su ammi sukayi haraman komawa inda suka fi wayo, kuka kawai uwani take yi domin sune take gani taji farin ciki a halin yanzu domin bata da kowa a duniya. Badan sun so ba haka suka tafi suka barta, koda tayi maganan a raba gidan a bawa su fareeda rabonsu, sai cewa sukayi a’a tayi zamanta a ciki ta kama sana’a.

A ranar su ammi suka tarka ta suka koma kano,….Kwana biyu da dawowar su, da daddare habeeb ya kira suheer a waya, koda ta daga wayar wani wawan ajiyar zuciya habeeb ya sauke, yace”Damn it, masoyiya ina kika yarda wayarki?, I’ve already gone mad akan kashe min waya da kika yi, ba abunda ban tuna ba, me ya faru kika kashe wayarki?.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button