AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tattaro dan karfin da ya rage mishi yayi ya ringa tattaka steps din bibbiyu har ya iso bangarenshi, ba tare da tunanin wanka, da sauya suturar dake jikinshi wanda su da bola basu da banbanci ba, ya wuce inda yake ajiye kayan zanenshi kasancewar sa kwararre a bangaren zane zane, wani kujera mai dan tsawo ya dauka ya mikar da ita, kana ya dau hard carbon paper fari sol ya shimfida akai, sannan ya debo pensira nshi nayin aiki, zanen ya fara cikin fushi, da sauri sauri yake yi yana hada zufa fuskar shi na kumbura tsawon minti sha biyar yana zanen, kat bakin pensir din ya karye wani ya dauka ya jefar da wanda ya karyen yacigaba, kat, shima ya karye, reza ya dauka ya fara fere pensir din baiyi aune ba rezar ya yanka shi, saiga jini yana zuba, cigaba yayi da zanen bai tsaya ba, tsawon wani lokaci kafun ya gama, saiga hoton suheer tsaye a jikin papern kamar ka kirata ta amsa, saidai fuskar ta ba annuri ko kadan hannunshi dake tsiyayar jini ya daga yana kallon fuskarta kana yabi fuskar ya ringa shafa jinin dake hannunshi a fuskar tata, take fuskar ya zama kamar ansa reza ko wuka an yanyanka shi,…. wani murmushin gefen baki yayi sannan yace “this is my vow, SUHEEEEEER…..

Gashinan nabaku harda bonus,… Dafatan na wanke laifina….. kuma anan na kawo karshen littafin auren fansa book one.

Shin ina labarin alaji samaila sarkin noma ne? koya ta kaya dashi bayan annemi adama ba’a ganta ba.
Wane mataki Rasheed zai dauka akan suheer?
Tsakanin rasheed, fareeda , da kuma suheer waye zaiyi auren fansa?, kuma wane irin fansa zasu dauka.?
Akwai yiwuwar soyayya mai karfi tsakanin rasheed da fareeda,? ko dai da suheer ne?,
Ina labarin yar uwar baban adama wato ammi, wacce suka zo nema a nigeria?,
Shin menene silar mutuwar mahaifin rasheed?
Menene silar zamowar rasheed mugu?
Shin me zai faru da wadannan yan uwa masu kaunar junan da suke kiran kansu rabin jiki da kuma sweetheart?.
Wacece hafsa da kuma lamido?
Shin fareeda xata cika burinta na zama jaruma?,
Ya zata kasance da habeeb da kuma asabe?
Duka amsan wadannan tambayoyin zasu zo muku a book two har ma da karin wasu, amma book two din zamu sa mishi kudi tunda bakwa KWAMEN, nawa yakamata musa yanda kowa zai iya biya?,
Kodai muci gaba da free…… Kai amma fa free dinnan ido ya fara ciwo, dan yanzu saina daddage kafun in hango fadeela daga nesa????????
Sai naji daga gareku, one luv guys????….

????????????Auren Fansa????????????

BOOK TWO

         NA 

Ummu Fadeela.

Typing????

Page 31 / 32

    A GIDANSU    SUHEEER.

……….Zaman yan bori suheer tayi a wurin hade da furta Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, wato ta nan rasheed ya bullo kenan,.

Da sauri ammi tabi bayan fareeda zuwa dakin, dan tasan karamin aikinta ne tajiwa kanta ciwo, kwance ta tadda ita lamo a kan gado tana ta sheshshekar kuka, hakan yasa ta fito a hankali taja mata kofar, dawowa palon ammi tayi ta zauna hadi da dafe goshi, da hannu tayi wa suheer alamar ta matso domin gaba daya kalmomin bakinta sun kafe, ba wanda take tunani sai lamido, ko sai yaushe zai dawo oho, gaba daya gidan yafi karfinta, ga hafsa kuma she’s not kinda support.

Da rarrafe suheer ta kariso inda ammi take zaune, domin ji take gaba daya jikinta ya rasa garkuwarsa.

Kirrrr wayar ammi tayi kara alamar shigowar kira, dubawa tayi taga kawarta hajiya saratu ke kira, da kyar ta amsa kiran gami da karawa a kunnenta, sallama tayi, hajiya saratu ta amsa mata daga daya bangaren hadi da cewa hajiya adama lafiya kuwa naji muryarki wani iri haka,? ammi tace “lafiya lau hajiya, kawai dai yanayinne sai a hankali,.”

Hajiya saratu tace “toh Allah dai yamana mai kyau, dama nakira kan maganar kayan da mukayi dake cewa in an sauke insanar dake ne, ammi tace au to to, sun iso kenan? saratu tace kwarai kuwa, dan dazu alhaji fatihu ya kira yake sanarda ni, don haka ki fito da wuri mu samu muje akan lokaci, kar a mutane su kwashe kayan ko,?

Ammi tace “insh Allah ganinan fitowa ki jiraye ni, bayan sun kashe wayar jinginar da kai ammi tayi da kujera hadi da lumshe idanu, yan kwanakinnan abubuwa sun mata yawa, just of a sudden wani yanaso ya rushe mata ginin da ta dau tsawon shekara ashirin tana yi, a bangare guda kuma tana yawan mafarki da alaji sama’ila cikin wani yanayi, sannan ga hafsa gaba daya ta dauke mata wuta, shima lamido yaki dawowa, tasan da yananan da abubuwa baza su kwabe a tsakanin yaran har haka ba,.

Dafe goshi tayi da furta “Astagfirullah” dan tashi tayi hade da maida kallonta kan suheer da ta hade kai da guiwa itama tana dan sheshsheka kadan kadan, hannu ta kai kanta tana shafawa a hankali, kana ta dau remote da niyyan kashe tvn dake ta babatu shikadai a palon tun dazu amma ba wanda ya maida hankali akai, kowa tashi ta isheshi, har zata danna kenan taga an hasko fuskar rasheed, hakan ne yaja hankalinta ta pasa kashewar.

Da sauri suheer ma ta dago fuska jin ana anbaton sunanan habeeb mamman, aiko tayi mugun gani, habeeb na kwance sambal ba alamun numfashi a tare da shi, ga kuma asabe tana ta zayyano bayani, cewa habeeb yana cikin mawuyancin hali, baisan ko wanda yake kanshi ba. tana bayani tana kuka a gaban taron yan jarida.

Ammi ne tace ” dama jikinnashi yakai har haka tsanani ne? girgixa kai tayi cikin matukar rudani tace “a’a ammi ko dazu ma fa da sauki na barshi har munyi magana dashi sosai faa, to kuma me ya sameshi haka yanzu? tana maganar ne tashin hankali rubuce akan fuskarta,.

Da sauri ta tashi tace “ammi bari inje induba ko wani abun ya sameshi ne tunda baya bata kadan. ganin irin rikicewar da tayi yasa ammi cewa ta jirata sutafi tare, tunda itama fita zatayi daman.

Dakinsu fareeda ammi ta leka ta ganta kwance bacci ya kwasheta cikin kuka, gyara mata kwanciya tayi sannan ta fita zuwa nata dakin ta dauko hijabinta, harta wuce dakin hafsa kuma ta dawo ta bude ta shiga, zaune ta ganta tayi tagumi alamar akwai abunda ke damunta, dagowa tayi jin anbude kofar, ammi ta mata kallo daya, da sauri ta kauda idanunta, domin bata son kallon damuwa ko kadan a idanun hafsa da dan uwanta, sune gatanta, sune danginta, kap duniya bata da wanda zata kalla a yanzu tace shi dan uwanta ne saisu, sune suka bata mafaka a lokacin da duniya tayi kokarin juya mata baya. Gathering courage tayi, ta dubi hafsa da tunda ta mata kallo daya bata kuma juyowa ba, tace “plsss hafsa ki kula min da fareeda zan dan fita amma ba jumawa zan dawo,” ” to” kawai hafsa tace ta juya kanta.

Fita ammi tayi ta iske suheer data kasa zama waje daya sai safa da marwa take a palon ji take kamar taje ta ciccibo ammi su tafi, tana ganinta kuwa ta dau hanyar kofar palon, a nutse suke tafiya har suka iso bakin hanya suka samu taxi, sanar masa sunan asibitin da habeeb ke kwance suheer tayi kana suka shiga, lokacinda suka iso yan jaridar sun watse, direct dakin da habeeb ke kwance suka shige, still yananan kamar sumamme, har lokacin bai bude ido ba, kuma baiyi motsi ba, a ranshi dai yana ta mamakin wanne irin al’amarine yake faruwa haka.

Kamshin turarenta da ya ziyarci kofofin hancinsa ne ya sanar da shi wanzuwarta a wurin, a hankali tayi sallama cikin siririyar muryarta, zuciyar shine ya shiga tseren gudu, yanason ya amsa yana tunanin kar mama tana wurin,da hanzari suka karisa shigowa dakin, kana suka nufi gadon daya ke,.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button