AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

AUREN FANSA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gyada kai ammi tayi tace” insha Allah”.

Yan rubuce rubuce yayi kan farar takadar dake gabanshi kana ya mika musu gami da cewa “kuje pharmacy ku karbi wannan, sannan akwai injections da zata ke karba tsawan wasu kwanaki kafun muga yadda al’amarin zai kasance.”

Mikewa suka yi ammi tana kallonshi tace “mun gode dacta”, shidai kallonta kawai yake yi with much suprise, har ta iso kofa ganin da gaske tafiya zatayi yayi karfin halin cewa “wani dare,.. Kauyen goruba….cikin fufore jihar adamawa mata da ciki, da yarinya karama.” cakkk ammi ta tsaya yayinda numfashinta ya dauke na wucin gadi.

Sai kuma ta juyo da sauri ta dawo gaban teburinshi tana kare masa kallo, tabbas bata gane shi ba kasancewar a rikice take a lokacin amma kuma baza ta taba mancewa da wannan ranar ba ba kuma zata mance da mutanen da suka taimaketa ba,sune suka fara taimakonta bayan tabawa kuma sune jigon nasarar ta a rayuwa da ba dan su ba, da yanzu wani labarin ake ba wannan ba…. Kure ta yayi da ido kafun ya furta where is the little girl and yana nuna cikinta da yatsan hannunshi…..Nuna masa fareeda tayi da hannu tace “here is the girl, ” ciki kuma…..

Zaune suke a palo yana sanye da kananan kayan da suka yi mugun zaftare masa shekaru bazaka taba tsammanin ya kai shekara hamsin ba.,ammi tana bashi labarin yadda rayuwa yayi da ita bayan ta bar gidansu da asuba fahimtar da tayi alaji manga abokin mijinta ne.Ta kare da cewa wannan shine abunda ya faru tana share kwallarta.

Gyara zama AMMAR yayi yana kokarin boye damuwar sa yace “take heart dear, dama haka rayuwa take kunshe da kaddarori da kuma jarabawowi idan kayi hakuri ka jure sai kayi nasara…Bayan munyi cigiyarki har mun gaji bamu samu labarinki ba haka muka hakura, amma kina makale a ranmu especially twin broda dina Amaan bai cika damuwa da damuwan wani ba amma ke kin dade yana damuwa a kanki ganin cewa ga tsohon ciki kuma ga yar yarinya and baki ma san ina kika nufa ba, bayan wani lokaci duk muka manta dake muka ci gaba da rayuwar mu,Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa, yanzu haka muna tare da mom da kuma amaan a london shi yana aiki da gidan rediyon BBC ni kuma kwararren therapist ne a halin yanzu, nakan shigo nigeria once in a while domin taimakawa kasa ta da al’ummarmu, Amaan yana da mata daya da kuma yaya uku, twins mata sai kuma kaninsu da muke kira Ayaan.”

Jin yayi shiru yasa ammi daga kai tace “And what about you? ya batun iyalai, yaranka nawa yanzu.”?

Shafa lallausan gashin kanshi da ya soma dan furfura kadan ammar yayi zuwa kan beard nashi yana murmushi yace “so far dai babu,iam still a bachelor duk matan ne basa burgeni ya fada da salon zolaya like always.amma yanzu na samu, na samu wacce ta burgeni ina fatan baza ta bani matsala ba,” ya fada yana kallon ammi har cikin ido,dago kai ammi tayi da sauri suka kalli juna…

Yau sati daya kenan da tafiyan rasheed, cikin satin nan ummie da suheer sun samu kusanci sosai, suna yawan zama suyi ta hira yawancin hirar kuma suheer keyi ammin ta kaza ko sweetheart kaza daya bayan daya yanzu ba wanda ummie bata sani ba cikin yan gidan su, ko da ta tambayi ummie me yasa ta dena ganin rasheed har tsawon sati ummie tace mata “dama ya kanyi hakan sau tari kinsan baya min magana amma yana sanar da buba so buba ya kira ni wai sunje shooting a abuja”.

Rasheed yana zaune a wurin da suke daukan wani shiri a abuja, ya karanta script na hannunshi ya kusan sau hamsin amma ya kasa fahimtar komai a kai, banda tunanin gida da labarin da ummie ta bayar ba abunda ya tsaya mishi a rai cikin ko wanne fitar numfashin sa.daga karshe yaga script din yayi ya watsar a wurin yana huci kamar wanda yayi dambe kana ya mike, mikewar sa yayi daidai da shigowar sako wayar sa, bude wayar yayi yabi content din da kallo, cikin zaro ido yace “what?” Damn it!.

Sai kuma yayi hanzarin nemo layin buba ya danna masa kira bugu biyu ya daga magana rasheed ya fara masa da dan sauri sauri kusan minti daya sannan ya kashe kiran ya bar wurin zuwa hotel da suka sauka ba tare da yabi takan directors da sauran producers ba.Harhada kayanshi ya fara yi da dan sauri sauri cikin jakar shi dama tsab yake cikin wankanshi.Zama yayi a bakin gadon hadi da dafe kanshi dake sarawa yana barazanar ballewa. Kiran buba ne ya shigo wayar shi cikin hamzari ya dauka.

Buba yace “boss an dace fa, akwai flight mai tafiya kano saidai in less than 30 minutes zasu tashi, so you have to be hurry up.” rasheed bai tanka masa ba ya kashe wayar kana ya goya jakarshi a baya ya fito a motar hotel din yaje airport ba bata lokaci suka daga zuwa kano…

Misalin biyar na yamma ya shigo cikin palon kamar an jeho shi, ummie na zaune saman kujera yayinda suheer ke duke a kasa kusa da ita tana mata tausa a kafarta, zuciyar ta fal farin ciki dan dazu sunyi magana da ammi ta wayat ummie har ma ta hada su sun gaisa, kuma sunyi waya da anty hafsa daga india can ma taji dadin labarin da antyn ta bata na ci gaban da ake samu akan jikin lamido, ta hada da fadin “suheer ki godewa mijinki ba karamin dawainiya yake yi damu anan ba, musamman ya turo wani yake kula damu tunda docto sageer ya koma nigeria,kuma akwai wasu kudade da aka kara bukata duk shi ya biya, ki saka masa kema da alkairi duk da nasan yadda auren naku ya kasance”.

Sosai maganganun suka ba suheer mamaki amma sai ta dake kawai domin farin cikinta yafi mamakinta yawa.

Duk dago kai sukayi suna kallonshi ganin ya fado musu kamar wadda aka koro, kallo daya ummie ta masa ta fahimci akwai damuwa tattare dashi,tsam ta mike ta wuce kitchen ta barsu a palon don tasan inba hakan tai ba haka zai ta tsayuwa a wurin, tana wucewa kuwa ya zo ya cafki hannun suheer dake kallon ikon Allah, ba ta mishi musu ba balle ya jima ta ciwo binshi ta shiga yi yana tafiya har zuwa second floor,tura ta yayi cikin palon kana ya shiga ya rufo kofa.

Yana kallonta strictly yace “tomorrow night akwai wani gagarumin party da abokan sana’a ta suka shirya min,manufar partyn kuwa,shine in gabatar dake a matsayin MRS RASHEED AHMAD MATAWALLE, so ina gargadinki kada ki yadda ki bani kunya dan wannan party ne da classic mutane zasu halarta,am i clear?.cikin zare idanu ya karasa maganar kana ya juya da nufin wucewa daki.

Suheer da ta zuba mishi ido kamar ta samu majigi tace “I won’t attend the party”.

Dakatawa yayi daga tafiyar da fara ya juyo yace “excuse me”.

Cikin tamke fuska tace “you’ve heard me right!, ba zanje wani so called party ba”. Cikin tabe baki yace “ohk let see “

Washe gari misalin sha daya na safe ummie ta sauko ta shiga kitchen domin sanar da chief nasu abunda za’a dafa for lunch, ta hango buba ta window din kitchen din sai making calls yake yi gaba daya ya zama busy,ga wani doguwar bus na wani decoration company dake pake gefe ana ta sauke wasu kwalaye ana shigar dasu cikin garden. Da tarin mamakin me ake a gidan haka ta fito gami da yafito buba da hannunta.Da dan hanzari ya iso yana kokarin kashe wayar dake kunnenshi.

“What’s going on here?” cewar ummie tana bin hanyar garden da kallo, buba yace “abokan harkar boss ne suka shiryawa amarya welcoming party kasancewar yadda auren ya kasance da dama basu halarci daurin auren ba, gashi anyi shi salam ba event ko daya, sai kuma yadan sunkuyo da kai cikin sigar gulma yace “saidai bansan meyasa boss ya zabi a yi a cikin gidannan ba maimakon event center.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button